28/07/2022
Me yasa ka ajiye mukaminka na shugaban kungiyar Arewa Media Writers?
Shin korarka akayi daga shugabancin?
Me ya faru da kungiyar?
Shin zamu iya sanin dalili?
Wa 'yan nan sune tambayoyin da ake ta turo min tun jiya da dare har zuwa yanzu da safiyar nan, wallahi dole tasa na sauka daga online na kashe data din wayana na toshe duk wasu hanyoyin da za'a cigaba da kirana sai dai turo sakonni.
Ga amsoshin tambayoyin ku a kasa
👇👇👇
A shekarar 2020, na jagoranci wasu daga cikin abokanan da muke yin rubuce rubuce da kuma yada labarai a kafofin sada zumunta, muka kafa ƙungiyar "Arewa Media Writers" daga ƙarshe s**a naɗa ni a matsayin wanda zai jagoranci ƙungiyar a matakin ƙasa baki ɗaya, s**a zaɓi abokina, aminina Comr Haidar Hasheem Kano, a matsayin sakataren ƙungiyar na ƙasa baki ɗaya, s**a kuma bamu damar naɗa sauran muƙamman ƙungiyar tun daga matakin ƙasa har zuwa jihohi domin yardar su a gare mu.
Mun gudanar da wannan babban aikin, mun naɗa kowane muƙami a bisa chanchanta na iya kwarewarmu, a cikin shekaru biyu da ƙungiyar tayi a Najeriya, an samu ɗumbin nasarori masu yawa, mun saka wasu a shafukanmu da gidajen jaridu a makwanni biyun da s**a gabata.
Mun kafa "Arewa Media Writers" ne ba don siyasa ko don wani ɗan siyasa ba, sai don mu bada gudummuwar mu ga yankin mu na Arewa, tare da tabbatar da haɗin kan marubutan yankin.
Mun fuskanci ƙalubale tun daga ranar da aka ayyanamu a matsayin shugabannin ƙungiyar na ƙasa, sharri, ƙazafi, ɓatanci, barazana, ƙiyayya, muzgunawa, cin fuska, habaici, zagi da cin zarafi, wallahi babu wanda ba'a yi mana ba.
Wallahi ansha saka mutane suci mutuncin mu musamman ni ko rubutun ɓatanci na ƙarya akaina, wanda bamu san adadi ba, ansha yi mana sharrin cewa an bamu maƙudan miliyoyin kuɗaɗe don mu baiwa al-umma amma mun cinye nida makusantana.
Tun a watan junairu na farkon wannan shekarar kungiyar ta gudanar da meeting a taron ta na Katsina, ta cimma matsaya akan lallai idan kungiyar ta cika shekaru biyu za'a sauke kowa a sake nada sabbin jagorori bisa chanchanta k**ar yadda aka yi a farkon kafa kungiyar, duba da yadda wasu sun nuna zalama na siyasantar da kungiyar a baya kuma kungiyar ta dakatar dasu, wasu kuma suna ta cin dun-duniyar kungiyar kan duk wani yunkurin ta na cigaban kungiyar.
A cikin tsarin doka "Constitution" na kungiyar ba'a tsara adadin tsawon lokacin da kowane shugaba zai sauka ba.
A yanzu haka kungiyar tana hannun mutanen da ko bamu raye ba zasu bari kungiyar ta rushe ba, kuma muna da yakinin zasu gudanar da ayyukan kungiyar a bisa gaskiya da amana sama da yadda muka gudanar.
Mutane Goma da aka damkawa alhakin sake zaban sabbin shugabanni babu wani National Excos da ya fisu shan wahala a kungiyar, ko ya fisu yiwa kungiyar hidima, muna kyautata musu zato akan zasu zabo nagartattun jagorori Insha'Allah.
Duk abunda kwamitin zasu aiwatar muna da tabbacin za su aiwatar dashi ne a bisa chanchanta ba ra'ayin wani ko son zuciya ba.
Babu wata kungiya a Najeriya musamman ma yankin mu na Arewa da babu rikici a cikin ta, saidai na wata yafi na wata, har kungiyoyin Addini suna fama da rikice-rikicen cikin gida, amma na "Arewa Media Writers" da sauki.
Ina fatan duk wani mai tambaya, ya samu amsar tambayan shi?