Albarka Radio

Albarka Radio Albarka Radio 97.5 is a Nigerian English and Hausa Radio Station based in Bauchi, Bauchi State, NG. and also promote businesses through advertisement.
(5)

Albarka Radio 97.5 FM Bauchi is a Nigerian English and Hausa radio station based in Bauchi, Bauchi State. It was founded and owned by Arrowhead Global Communication services Limited. Renowned for its humorous approach to broadcasting, the station broadcast a mixture of news, features, sport, entertainments, talk shows, topical issues and interviews. Mission
As an independent broadcast station, Alb

arka radio shall reflect and promote all sides of issues and opinions and build a tradition of trust and credibility with our audience. Vision
To be a reference point in quality radio broadcasting in Nigeria using the professional ethics of balance and fairness to motivate the listeners.

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na uku ya shawarci ƴan Najeriya da su fahimci ƙalubalen da ke gabansu dom...
11/05/2024

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na uku ya shawarci ƴan Najeriya da su fahimci ƙalubalen da ke gabansu domin tunkarar su.

Sultan ɗin dai ya faɗi hakan ne yayin wata ziyara da ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru ya kai masa a fadarsa ranar Juma'a.

"Bai k**ata mu bari wani ya samu galaba a kanmu ba. Ministan tsaro ya san irin girman alhakin da ke rataye a wuyansa. Na kuma yi amannar cewa yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki domin su taimaka masa. Muna aiki tare kuma ba za mu daina ba.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ba komai ba ce illa rabin jikin ...
11/05/2024

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ba komai ba ce illa rabin jikin PDP da ya rube, saboda kashi 80 na ƴaƴan APC duk tsofaffin ƴan PDP ne.

Sule Lamido ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Arise game da fagen siyasar Najeriya.

Da yake mayar da martini kan kalaman shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje na cewa babu gurbi a kujerar shugabancin Najeriya a 2027, Lamido ya ce magana ce kawai ta ƴan siyasa, domin tsarin mulki ya bayar da damar gudanar da zabe duk bayan shekaru 4.

A cewarsa, jam’iyyar APC ta zo kan karagar mulki ne ba tare da manufofi ba, amma lokacin da PDP ke kan karagar mulki akwai dimbin manufofin da s**a tsara gudanarwa domin ci gaban Najeriya. Don haka ba za a taba hada gwamnatin PDP da ta APC ba, domin akwai bambanci sosai.

Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Zamfara sun bayyana cewar ƴan bindiga sun kai hare-hare mabanbanta, inda s**a kashe ma...
11/05/2024

Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Zamfara sun bayyana cewar ƴan bindiga sun kai hare-hare mabanbanta, inda s**a kashe manoma 30, tare da wani malamin addinin Muslunci a jihar.

Maharan sun kai mabanbantan hare-haren ne a kauyen Gidanngoga da ke karamar hukumar Maradun da kuma kauyen Bilbis da ke karamar hukumar Tsafe a jihar.

Jaridar Leadership ta rawaito cewar maharan sun fara kai farmaki karamar hukumar Maradun, inda s**a kai hari kauyen Gidangoga, yayin da manoma ke kokarin gyara gonakinsu saboda karatowar damina.

Kazalika, maharan sun hallaka Malam Makwashi Maradun Mai Jan Baki, a lokacin da yake aiki a gonarsa.

Da yammacin wannan rana, ƴan bindigar sun sake kai wani hari kauyen Bilbis da ke gundumar Tsafe, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 20.

10/05/2024

Shiri na musamman tareda Shaik Mai warka warka Alh DANLADI INUWA OC KWANO kan aiyukan Mai girma GWAMNAN JIHAR BAUCHI
Wanda Bala Dahiru zai jagoranta

10/05/2024

Shiri na musamman tareda babban bakonmu Abubakar Yusuf Ladan wanda yayi taken Albarka Radio kala daban daban irin su KANDAMO TSAKI, ALBARKA SAI DAN ALBARKA, JIKIN KULBA LUMUI LUMAI, DA GIZO DA KOKI DUK KWASKWANSU SU GUDANE FADIN ALBARKA SE DAN ALBARKA da dai sauranmu,

10/05/2024

Shiri na musamman tareda babban bakonmu Abubakar Yusuf Ladan wanda yayi taken Albarka Radio irin su KANDAMO TSAKI, ALBARKA SAI DAN ALBARKA, JIKIN KULBA LUMUI LUMAI, DA GIZO DA KOKI, dai dai sauransu

Ku kasance damu a Yau tare da OC Kwano
10/05/2024

Ku kasance damu a Yau tare da OC Kwano

Wasu daga cikin masu shaguna na wucin gadi a gefen titunan cikin garin Bauchi sun fara bin umarnin gwamnati bayan basu t...
10/05/2024

Wasu daga cikin masu shaguna na wucin gadi a gefen titunan cikin garin Bauchi sun fara bin umarnin gwamnati bayan basu takardar wa'adi.

Sojoji sun ceto wata matar aure tare da ƴaƴa mata uku da ta haifa wa wani dan Boko Haram da kungiyar ta yi mata auren do...
10/05/2024

Sojoji sun ceto wata matar aure tare da ƴaƴa mata uku da ta haifa wa wani dan Boko Haram da kungiyar ta yi mata auren dole da shi.

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakilatar Ƙananan hukumomin Babura da Garki ta jihar Jigawa ya  rasu.
10/05/2024

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakilatar Ƙananan hukumomin Babura da Garki ta jihar Jigawa ya rasu.

Ana sanar al'uma cewa duk wadanda suke da shaguna na wucin gadi a gefen hanyoyi a cikin garin Bauchi su gaggauta cirewa ...
10/05/2024

Ana sanar al'uma cewa duk wadanda suke da shaguna na wucin gadi a gefen hanyoyi a cikin garin Bauchi su gaggauta cirewa nan da mako guda daga ranar wannan sanarwa.

Sanarwa daga janar manajan hukumar kula da birane ta jihar Bauchi Town Planner Gimba Aliyu Ahmed

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! 🎉 Abubakar Umar Al'turaawii, Lawal Ismail,...
10/05/2024

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! 🎉 Abubakar Umar Al'turaawii, Lawal Ismail, Abdulrahaman Adam Pim, Abdurrahaman Said Yunusa Asy, Abbas Ibrahim, Nuruddeen Sulaiman, Mai Tijjaniya Abba Sosimita, Abdulrazaq Isah, Ayshert Sunusy, Abubakar H Zadawa

10/05/2024

Yadda Sadiq Zubairu ya kashe abokinsa

🎥: SP Abdullahi Haruna Kiyawa

Majalisar wakilai, ta umarci babban bankin Najeriya (CBN), da ya janye aiwatar da harajin tsaro na yanar gizo wanda za a...
09/05/2024

Majalisar wakilai, ta umarci babban bankin Najeriya (CBN), da ya janye aiwatar da harajin tsaro na yanar gizo wanda za a ke cire kashi 0.5 daga asusun kwastomomin bankuna.

Ƴan majalisar sun bayyana matakin a matsayin abu mai wuyar gaske.

Sama da shugabannin ɗalibai 60 daga manyan makarantu uku a jihar Bauchi ne s**a taru domin halartar taron ƙarawa juna sa...
09/05/2024

Sama da shugabannin ɗalibai 60 daga manyan makarantu uku a jihar Bauchi ne s**a taru domin halartar taron ƙarawa juna sani wacce take da manufar inganta musu ƙwarewa a fannin shugabanci.

Taron wadda ƙungiyar Young Leaders Network ta shirya tare da tallafin Leap Africa da Asusun matasan goben ta Najeriya wato Nigeria Youth Futures Fund yana gudana ne a ɗakin taro na American Space dake nan Bauchi wadda aka fara daga 7 zuwa 8 ga watan Mayun shekarar 2024.

Taron ƙarawa juna sanin dai ya haɗa hancin shugabannin ɗalibai daga jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, Jami'ar jihar Bauchi dake Gadau da kuma Kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya dake Bauchi.

An tsara shirin ne don baiwa mahalarta ilimin siyasa, ƙara inganta damamaki wa mata, ƙarfafa fafutukar siyasa gamida faɗaɗa tsare-tsaren siyasa a wuraren ɗalibai.

Manajan kula da shirye-shirye na Young Leaders Network Moses Danjuma ya buƙaci mahalarta taron da suyi amfani da damar da s**a samu wajen inganta kansu ta yadda zasu kawo sauyi mai ma'ana a makarantun su dama ƙasa baki ɗaya.

Har ila yau, taron nada zummar sauya rayuwar mahalartan ta yadda zasu samu cikakken ilimin shugabanci da kuma haɗuwa da wasu mutane daban ta yadda zasu samu ƙarin basira.

Taron ya kuma nuna aniyar ƙungiyar Young Leaders Network, LEAP Africa da Asusun matasan gobe ta Najeriya wajen bunƙasa ilimin matasa gamida ciyar da cigaban shiyyar arewa maso gabas zuwa mataki na gaba.

An k**a wani dan shekara 71 bisa zargin yin lalata da ƴar wani magidanci da ke haya a gidansa ƴar shekaru 14, har ta sam...
09/05/2024

An k**a wani dan shekara 71 bisa zargin yin lalata da ƴar wani magidanci da ke haya a gidansa ƴar shekaru 14, har ta samu juna biyu.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa an k**a tsohon wanda ma’aikacin asibitin ne yana lalata da yarinyar ’yar shekara 14 a cikin bandaki a Karamar Hukumar Ifo ta Jihar Ogun.

Yarinyar ta shiga bandakin gidan ne domin yin wanka, amma bayan ’yan mintoci sai mai gidan ya bi ta cikin bandakin inda ake zargin ya yi lalata da ita.

Kakakin ’yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar.

“An kai yarinyar Asibitin Tamara da ke Akute kuma sak**akon gwajin da likitocin s**a gudanar ya nuna cewa ba wannan ne karon farko ba, domin kuwa yarinyar na dauke da cikin makonni shida.

Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika da ƴarsa kan kudi Naira miliyan 100 kan kowannensu.
09/05/2024

Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika da ƴarsa kan kudi Naira miliyan 100 kan kowannensu.

Tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika da diyarsa sun isa kotu domin kare kansu a badakalar kudaden da s**a ka...
09/05/2024

Tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika da diyarsa sun isa kotu domin kare kansu a badakalar kudaden da s**a kai Naira bilyan 2.7

Ba kowanne dan cikin garin Bauchi ba ne zai gane nan wajen b***e kuma 'yan kauyukan Bauchi k**ar su Ningi, Azare, Gombe,...
09/05/2024

Ba kowanne dan cikin garin Bauchi ba ne zai gane nan wajen b***e kuma 'yan kauyukan Bauchi k**ar su Ningi, Azare, Gombe, da sauransu wadanda sai Allah ya kirasu suke samun damar shigowa birnin nan na Bauchi.

Da fatan masu bibiyar shafin Albarka Radio sun tashi lafiya.

Yadda akan tarbi tawagar farko na maniyyata aikin hajjin bana daga kasar India a garin Madina.📷: Inside the Haramain
09/05/2024

Yadda akan tarbi tawagar farko na maniyyata aikin hajjin bana daga kasar India a garin Madina.

📷: Inside the Haramain

Hukumar EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Sanata Hadi Sirika ranar Alhamis bisa za...
08/05/2024

Hukumar EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Sanata Hadi Sirika ranar Alhamis bisa zargin badakalar kudin da sauka kai Naira bilyan 2.7

08/05/2024

"A baya jihar Bauchi tana samun litan ruwa dubu talatin ne, amma a yanzu dubu sittin take samu" Abubakar Musa Madaki PA

Kungiyar TUC ta yi barazanar gudanar da zanga-zanga idan har gwamnatin tarayya bata soke harajin CBN na 0.5% ba
08/05/2024

Kungiyar TUC ta yi barazanar gudanar da zanga-zanga idan har gwamnatin tarayya bata soke harajin CBN na 0.5% ba

08/05/2024

BIKIN RANAR YAWON BOLA

Masu bikin sun ce sun kirkiro bikin ranar ne don taya abokin sana'ar su na tsince tsince a bola (Bola jari) murnar aure.

Wani Magidancin mai shekaru 40 ya caka wa matarsa almakashi da yayi sanadiyar mutuwar ta saboda za ta je ganin danta a g...
08/05/2024

Wani Magidancin mai shekaru 40 ya caka wa matarsa almakashi da yayi sanadiyar mutuwar ta saboda za ta je ganin danta a gidan tsohon mijinta

Lamarin ya faru ne yayin gardamar da ta barke a tsakaninsu bayan daukar dogon lokaci suna zaman doya da manja.

Makwabtantan ma’aratan da ke zaune a garin Akure a Jihar Ondo sun shaida wa Aminiya cewa, sun sha yi musu sulhu amma abin ya ci tura.

Kakakin ƴan sanda a jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce, “Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin da matarsa suna yawan yin rigima kan batun zuwa duba yaronta a gidan tsohon mijinta.

Kawo yanzu dai wanda ake zargin yana hannun hukuma ana gudanar da bincike da nufin daukar mataki na gaba.

08/05/2024

Jihar Bauchi zata iya noma abincin da zai ciyar da ƴan Najeriya idan ta maida hankali akan harkar noma...."Alh. Usman Isa, jigo a jam’iyyar APC"

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah yayi rasuwa wa Alhaji Garba Aliyu Jalam (Danburan din Jalam) a daren jiya Talat...
08/05/2024

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un

Allah yayi rasuwa wa Alhaji Garba Aliyu Jalam (Danburan din Jalam) a daren jiya Talata 07/05/2024.

Za a masa sallah a yau Laraba 08 ga watan Mayu na shekarar 2024 a Masallacin Jumu'a na JIBWIS Gwallaga da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

Allah ya gafarta masa, Amen summa Amen.

Babbar kotun jihar Edo ta tasa keyar wani mutum zuwa gidan yari zaman sauraron hukunci bisa zargin yi wa wata ’yar sheka...
08/05/2024

Babbar kotun jihar Edo ta tasa keyar wani mutum zuwa gidan yari zaman sauraron hukunci bisa zargin yi wa wata ’yar shekara 50 fyade.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wanda ake tuhuma ya musanta zargin da ake masa na yunkurin yi wa dattijuwar mai shekara 50 da haihuwa fyade.

Lauya mai shigar da kara, Misis Ama Iyamu, ta shaida wa kotun cewa a ranar 27 ga Maris, 2023, a birnin Benin ne wanda ake zargin ya yi yunkurin yi wa matar fyade.

Barista Iyamu ta ce, wannan laifi ya saba wa sashe na 4 na dokar cin zarafin jama’a ta jihar Edo, ta 2021, kuma laifin na da hukunci a sashe na 5 (2) na wannan doka.

Bayan sauraron karar ne Mai Shari’a Efe Ikponmwonba, ta bayar da umarnin a tsare wanda ake zargi a gidan yari, da dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Yuli 2024

Address

NO. 22 MAMBILA Avenue, OFF SUNDAY AWONIYI STREET, NEW GRA
Bauchi
740271

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Albarka Radio posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Albarka Radio:

Videos

Share

Category



You may also like