03/04/2022
Kana tsammanin Najeriya zata gyaru?
Najeriya bazata taɓa gyaruwa ba muddin Malamai zasu cigaba da zama kwaɗayayyu sannan kuma yaran ƴan siyasa domin kuwa babu yadda za'ayi mutum ya baka abun duniya sannan kuma kace zaka fito ka faɗi gaskiya.
Muna da tarin Malamai a ƙasar nan amma da dama daga cikin su ba zasu iya fitowa suyi magana akan abubuwan da suke faruwa a ƙasar nan ba saboda abun duniya ya rufe musu ido.
Ba daidai bane don wanda yake Shugabantar ƙasar nan Musulmi ɗan arewa ne ace idan yayi kuskure ba za'a faɗa ba domin kuwa hakan ba adalci bane.
A lokacin da Goodluck Jonathan yake Shugabantar ƙasar nan abubuwa basu taɓarɓare k**ar yanzu ba amma kuma yasha s**a da Allah wadai daga wajen ƴan arewa yanzu kuma da ɗan arewa ne akan kujerar sun kasa ce komai.
Imam Nuru Khalid ya fito ya faɗi gaskiya ya kuma bada shawarin cewa zaɓe bata da amfani matuƙar waɗanda ake zaɓa bazasu kare rayuka da dukiyoyin al'umma ba.
Yanzu don Allah kai hakan yana maka daɗi yadda ake rayuwa a Najeriya? Kodai saboda lamarin bai shafeka kai tsaye bane? Ko kuma don lamarin bai shafi wani naka ba?
Wallahi idan har muna neman mafita tou dole ne muyi amfani da shawarin Imam Khalid.
Allah yasa mudace.
[email protected]