08/11/2023
Makiyayi ya gartsa wa kada cizo don kubutar da kansa
Wani makiyayi dan kasar Australia ya tsallake rijiya da baya, bayan ya yi artabu da wani kada da ya far masa, inda shi ma ya gatsa wa kadan cizo.
Mai kiwon shanun Colin Deveraux ya shafe tsawon wata daya yana jinya a asibiti, bayan zabgegen kadan mai tsawon kafa goma ya raunata shi a yankin Northern Territory.
Ya fada wa tashar labarai ta ABC News cewa ya gartsa wa kadan cizo ne a kan fatar idonsa lokacin da yake fafutukar tsira da rai.
Mista Colin Deveraux ya ce ya shiga garari ne bayan ya tsaya a wani tafki lokacin da yake tafiya a kusa da Kogin Finniss cikin watan jiya.
Ya ce ya dan tsaya a gefe, bayan ya lura da kifayen da ke ninkaya a ruwa. Amma lokacin da ya dan ja da baya, sai ya ji kawai kada ya cafkar masa kafar dama, inda ya jijjiga shi k**ar tsumma sannan ya fizge shi cikin ruwa.
Makiyayin ya fada wa tashar ABC cewa da farko ya sa daya kafarsa ya shuri kadan - kafin ya sa baki ya gartsa masa cizo.
"Ina cikin wani yanayi na rudewa… sai kwatsam na ji hakorana sun k**a fatar idonsa. Tana da matukar kauri, k**ar wata jakar fata, amma kawai sai na ja da karfi, ai kuwa sai ya sake ni.
"Na yi tsalle na fito, na nufi wurin da motata take. Amma ya sake biyo ni k**ar tafiyar mita hudu, kafin kuma sai ya tsaya."
Mista Colin Deveraux ya ce ya yi amfani da tawul da igiya wajen daure kafarsa da ke zubar da jini, sannan dan'uwansa ya tuko shi a mota, tafiyar kilomita 130 zuwa Asibitin Royal Darwin.
© BBC Hausa