29/12/2022
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata manyan motoci 25 na barasa a 2022
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta lalata manyan motoci 25 na barasa tare da k**a wasu mutane 2,260 da ake zargi da aikata laifuka a ayyukanta da ta gudanar daga watan Janairu zuwa Disamba na 2022.
Dakta Harun Sani Ibn-Sina, babban kwamandan hukumar ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar hukumar a yau Alhamis a Kano.
Ya ce manyan motocin na dauke da dubban kwalabe na barasa iri-iri, inda ya ce za a farfasa wasu karin kwalaben na giya kafin watan Janairu.
“Yawancin wadanda aka k**a da laifin aikata laifuka, an mika su ga hukumomin tsaro domin daukar matakin da ya dace, wadanda ke kasa da kasa sun hadu da iyalansu.
“A shekarar da ake bankwana da ita, domin a rage barace-barace a cikin birni, mun kwashe mabarata kusan 1,269 a cikin wata daya, 386 aka mayar da su jihohinsu.
“Hukumar Hisbah ta jihar Kano kuma ta yi nasarar tarwatsa tarurrukan lalata 86 da sauran laifuka mak**antansu domin dakile munanan dabi’u a fadin jihar,” inji shi.
~ Daily Nigeria