Hantsi24

Hantsi24 Jaridar Hantsi24, Jarida ce mai zaman kanta data shahara wajen kawo muhimman labarai da dumi duminsu tare da tsage gaskiya dangane da kowanne al`amari.

YANZUN NAN !Babbar kotun jihar Kano ta ba da umarnin gudanar da zaben kananan hukumomi. Hukuncin ya ci karo da na kotun ...
25/10/2024

YANZUN NAN !

Babbar kotun jihar Kano ta ba da umarnin gudanar da zaben kananan hukumomi.

Hukuncin ya ci karo da na kotun tarayya fa ke jihar da ya umarci kada a gudanar da zaben.

Gobe Assabar ne ake sa ran gudanar da zaben a kananan hukumomin jihar 44.

KANO: SOJOJI SUN HARBI MASU ZANGA ZANGA UKU* Jama'a na tarwatsa shaguna a Zoo Road.* Sojoji da yan sanda sun fara janyew...
01/08/2024

KANO: SOJOJI SUN HARBI MASU ZANGA ZANGA UKU

* Jama'a na tarwatsa shaguna a Zoo Road.

* Sojoji da yan sanda sun fara janyewa suna zubawa mutane ido.

* Dubban matasa na ta ci gaba da tudadowa wasu suna komawa gida suna sake shiri

* Matasa na ci gaba fa bankawa tayoyi wuta.

SARKI AMINU NA SON KOTU TA HANA ABBA RUSHE GIDAN NASSARAWAWasu bayanai da Hantsi24 ta samu sun nuna cewa yau Jumma'a Sar...
21/06/2024

SARKI AMINU NA SON KOTU TA HANA ABBA RUSHE GIDAN NASSARAWA

Wasu bayanai da Hantsi24 ta samu sun nuna cewa yau Jumma'a Sarkin Kano na 16 Aminu Ado Bayero, zai shigar da kara gaban kotu a jihar, don neman a dakatar da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf daga rushe Gidan Nassarawa, inda yake zaune.

Jiya Alhamis ne dai gwamnan ya bayar da umarnin rushe fadar don yin gyare gyare, bayan hukuncin wata kotun tarayya da ya tabbatar da dokar da gwamnan jihar ya sanyawa hannu, ko da yake ya ce ba a bi ka'ida wajen dawo da sarki Sanusi ba

DA DUMI DUMI : ABBA YA BADA UMARNIN K**A AMINU ADO BAYEROGwamnan Kano Abba Kabir Yusuf  ya bada umarnin k**a tubabben sa...
25/05/2024

DA DUMI DUMI : ABBA YA BADA UMARNIN K**A AMINU ADO BAYERO

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin k**a tubabben sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero nan take.

Cikin wata sanarwa da Hantsi24 ta samu mai dauke da sa hannun kakakin gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce an shigo da tsohon sarkin jihar Kano cikin dare domin tayar da tarzoma.

Gabanin hakan mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdussalam, ya zargi mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, da kitsa dawo da sarkin jihar Kano.

Yanzu haka wasu bayanai da Hantsi24 ke samu na nuna cewa tubabben sarkin Aminu Ado na gidan sarki na Nassarawa, yayin da shi kuma sarki Sanusi da aka sake nadawa ya shige gidan sarki da tsakar dare bayan samun labarin an taho da Aminu Ado.

DA DUMI DUMI: GWAMNAN EDO YA MUTURahotannin da Hantsi24 ke samu na tabbatar da mutuwar gwamnan jihar Edo Rotimi Akeredol...
27/12/2023

DA DUMI DUMI: GWAMNAN EDO YA MUTU

Rahotannin da Hantsi24 ke samu na tabbatar da mutuwar gwamnan jihar Edo Rotimi Akeredolu.

Ya mutu ne a wani asibiti da ke Lagos, bayan shafe tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya.

RUNDUNAR SOJIN NIJAR TA MIKA WUYA  GA MASU JUYIN MULKIRundunar sojin Nijar ta sanar da goyon bayanta ga sojojin da s**a ...
27/07/2023

RUNDUNAR SOJIN NIJAR TA MIKA WUYA GA MASU JUYIN MULKI

Rundunar sojin Nijar ta sanar da goyon bayanta ga sojojin da s**a sanar a wani jawabi a gidan talabijin cewa sun hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Hantsi24 ta ga wata sanarwar babban hafsan hafsoshin sojin kasar, inda a ciki ya ce ya yi hakan ne domin kaucewa fada tsakanin sojojin.

Mista Bazoum, wanda na hannun daman kasashen yammacin duniya ne da ke yaki da masu kaifin kishin Islama, na tsare a hannun dakarun tsaron fadar shugaban kasa har yanzu.

Tuni sojojin da s**a karbe iko s**a rufe iyakokin kasar da kuma soke duk wani mukamin siyasa da rushe majalisub dokoki da bangaren shari'a.

AN YI JUYIN MULKI A NIJARWasu sojoji sun bayyana a babban gidan talabijin mallakin gwamnati a Nijar, inda s**a sanar da ...
26/07/2023

AN YI JUYIN MULKI A NIJAR

Wasu sojoji sun bayyana a babban gidan talabijin mallakin gwamnati a Nijar, inda s**a sanar da hambarar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum.

Wani soja da ya bayyana kansa a matsayin Major Amadou Aboramane ne sabon shugaban kasa a yanzu.

AN GA WATAN KARAMAR SALLAHMahukunta a Saudiyya sun ba da sanarwar ganin jinjirin watan Shawwal, wato watan karamar Salla...
20/04/2023

AN GA WATAN KARAMAR SALLAH

Mahukunta a Saudiyya sun ba da sanarwar ganin jinjirin watan Shawwal, wato watan karamar Sallah.

Hakan na nufin gobe Juma'a ne daya ga watan Sallah a galibin kasashen musulmai, ciki har da Najeriya.

Allah ta'ala ya karbi ibadun da muka yi a wannan wata da muke shirin bankwana da shi na Ramadan.

Address

Mai Tama
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hantsi24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hantsi24:

Share

Hantsi24

Hantsi24 Ingantacciyar jarida ce a wannan shafi na sada zumunta dake kawo muku labarai da dumi-dumin su, kuna da damar aiko mana da hotuna da bidiyon wani abu dake faruwa a inda kuke domin mu wallafa idan mun tabbatar da ingancin sa.