18/12/2024
: ALLAH YA TSINEWA MUKU , YA MAKANTAR DA KU DON ANNABI MUHAMMADU SAW
Wato barayi (Yan daba) da s**a SARI Malam Bashir Kafinta jiya da dare a Unguwar Sheka kusa da layin Masallacin Mai Dalla Dalla da duk wani mai hannu ,Ya Allah har wadanda s**a yi farin ciki saboda munafinci irin munafikai.
Mai Girma PRO Abdullahi Haruna Kiyawa barayin nan an san su a Sheka domin an sha gayawa Yan Sandanku na Sheka Wallahi sun san su, ga guraransu kamar haka
1 Bayan Makaranta Sheka
2 Dan Fodio Sheka
3 Layin Marigayiya Hajiya Rabi Sheka Gidan Kaji
4 Sheka Babban Layi musamman layin Service wato layin da ake yiwa lakabi da Layin Uwa Babu Kwaba
5 Sheka Gidan Gunti / Achilafiya
Ya Hayyu Ya Kayyum don sirrin dake cikin YASIN ka wulakanta yaran nan domin basu da nufin komai sai kokarin hallaka mutane kamar yadda s**a so kashe Malam Bashir Kafinta.
Ina rokon Allah ya bashi lafiya da kulawarsa
Zamu cigaba da baiwa Yan Sanda da gwamnatin Kano labarin sirri da muke samu kan shedanun da suke damun Kano Albarkar Annabi Muhammadu SAW.
Arewa Reporters