03/12/2024
BABINLATA IS BACK!
Ina ma'abota karatun littafan Hausa musamman tsofaffin littattafan shahararre kuma fasihin marubuci Bala Anas Babinlata?
Ko kun tuna da littattafansa irin su ÆŠA KO JIKA (wanda son zuciya ya kai ga uwa ta auri É—anta a rashin sani)?
Ko kun tuna littafin SIHIRTACCE wanda aka sihirce wani matashi ya koma shuri a zamanin da babu mota da keke sai bayan shekaru É—ari ya dawo mutum?
Ko kun tuna SARA DA SASSAKA na soyayyar bakin fata É—an talakawa da Æ´ar É—aya daga cikin manyan turawan mulkin mallaka?
Toh wadannan da ma sauran littatafansa duk sun dawo cikin cikakken tsari mai ƙayatarwa ga duk mai bukata wato BOOK-ON-DEMAND cikin farashi mai sauki.
Duk mai so ya yi magana da Bala Anas Babinlata kai tsaye ta lambar WhatsApp +2348036253479 don saka order dinsa. Za a kawo maka duk inda kake bukata.