19/05/2025
Taron Manema Labarai;
SUNA COMR YUSUF ALIYU FADA SHUGABAN KUNGIYAR SEN. SHEHU BUBA FREE MEDICAL OUTREACH TEAM.
Barka da Safiya/Rana taron 'yan jaridu, abokan aiki da al'ummar jihar Bauchi baki daya.
Yau rana ce mai muhimmanci ga kungiyar mu ta Sen. Shehu Buba Free Medical Outreach Team, kungiyar data fashe shekara guda wadda take dauke da jajirtaccun ma'aikatan kiwon lafia wadda ya hada da; medical doctors, nurses,. midwives, community health practitioners, medical record professionals, medical lab scientist and technicians, environmental health practitioners, public health practitioners, dental health technicians and therapists da sauran su. Kungiyar da take dauke da membobi sama da mutum dubu goma (10,000) a kananan hukumomi ashirin na jihar Bauchi.
Kungiyar tana da bayyanan nen manufa tare da yin aiki tukuru wajen cimma manufofin ta wadda shine; isar da jinya kyauta ga al'ummomi mabukata, wadda munayin hakan ne dan tabbatar da goyon bayan mu ga Sen. Shehu Buba a matsayin dan takarar gwamnan jihar Bauchi.
Muna yin wannan aikin ne cikin salon dabara da yakinin cewa hakan na da matukar muhimmanci da tasiri acikin al'umma, bisa ga wannan dalilin yasa muka sadaukar da kudaden mu wajen gudanar da wannan aikin jinya kyauta. Ga wasu daga cikin aikace-aikacen da mukayi kamar haka;
1. Ranar 7 ga watan 7, 2024, mun gudanar da aikin jinya kyauta ga al'ummar Sabon Garin Nabordo dake karamar hukumar Toro, wadda ma'aikatan mu sun samu nasarar jinyar mutum 153 wadda mafi yawa iyaye mata ne, da yara da tsoffi.
2. Bayan nan ranar 13 ga watan 7, 2024, mun sake samun nasarar fadada aikin jinyar a garin Bidir dake karamar hukumar Katagum wadda mukayi jinyar mutum 171 iyaye mata, yara da tsoffi.
3. Bugu da kari, alokacin da aka samu ibtila'in bullar cutar Amai da Gudawa a jihar Bauchi a watan 8, 2024, kungiyar mu ta Sen. Shehu Buba Free Medical Outreach Team ta shiga cikin lamarin kamar haka,
Munyi amfani da kudaden mu wajen gudanar da aikin sanya maganin kashe kwayar cutar Amai da Gudawa a Rijiyoyin al'umma, raba maganin kashe cutar Amai da Gudawa acikin ruwan sha ga magidanta 100, gudanar da aikin feshin kashe kwayar cutar Amai da Gudawa a garin da aka samu bullar cutar, gangamin wayar da kai kan yadda za'a kaucewa cutar wadda ya gudana a Gwallagan Mayaki, kofar Fada primary school, Yakubiyatul Islam da Madarasatul Aunin Islam Bauchi.
Duk wadan nan aikace-aikace masu muhimmanci, munyi sune da kudaden aljuhun mu da manufar tallata Sen. Shehu Buba a matsayin dan takarar gwamnan jihar Bauchi.
Saide duk da irin jajircewa dayin aiki tukuru mai muhimmanci da mukayi, mun fiskanci kalubale a zahiran, na sama da shekara guda wadda munyi kokarin ganawa da Sanata lokaci da dama ta hanyar rubuta bukatar hakan tare da bin sawun ma'aikatan sa da makusantar sa irin su Malam Yahya, Hassan Gaji, Baba Sade,Barr Mukhtar da Barr Clinton da sauran su, dan su nema mana lokacin ganawa da Sanata. Abin mamaki, kokarin hakan yaci tura.
Sai dai ayar tambaya anan itace wasu kungiyoyi da mukayi imanin cewa aikace-aikacen su bai kai manu muhimmanci da tasiri ba suna samun damar ganawa da Sen. Shehu Buba. Amma mu kungiyar mu ta gagara samun wannan dama wadda hakan a bayyane yake cewa ba'a bukatar irin aikace-aikacen mu agidan Sen. Shehu Buba musamman kan manufar tallata shi a matsayin dan takarar gwamna.
A saboda haka, bayan dogon nazari da tuntuba, Shugabancin wannan kungiya ta cimma matsaya kamar haka nan take;
Na farko; muna sanar da janye goyon bayan mu ga Sen. Shehu Buba a matsayin dan takarar gwamna, kuma mun ayyana wannan kungiya tamu ta Sen. Shehu Buba Free Medical Outreach Team a matsayin rusasshiya. Bisa lura da mukayi baida tanadi na musamman akan harkar kiwon lafia musamman yazamo gwamnar jihar Bauchi.
Na biyu; A matsayin sa na mai ilimin addini muna kira da tattausar murya gare shi daya dawo mana da 7.6 millions da muka kashe a aljuhun mu wajen gudanar da aikace-aikacen jinya kyauta a madadin sa (wadda hakan ya harta a musulunci)
Na uku; dan zakulo shugaba mai kishi da son cigaban al'ummar jihar Bauchi, muna jaddada goyon bayan mu ga Dr. Ibrahim Ali Usman a matsayin dan takarar Sanata a shiyar Bauchi ta kudu 2027.
Na hudu; munayin kira zuwa ga 'ya'yan kungiyar mu masu biyayya kuma jajirtaccu dake kananan hukumomi ashirin na jihar Bauchi su kwantar da hankali su da cigaba da kasancewa masu biyayya. Nan bada jimawa ba zamu sake zakulo dan takarar gwamna da yasan muhimmancin mu da bamu dukkan nin goyon bayan da muke bukata dan cimma manufofin mu na tabbatar da ingantaccen tsarin kiwon lafia a jihar Bauchi.
A karshe; ba haufi a bayyane take; a wannan karon ba za'a barmu abaya ba. Za'a dama damu sosai a harkokin siyasa dan tabbatar da wadda s**a chachanta, suke da tsarin inganta harkar kiwon lafiyar al'ummar mu, sune zamu basu dama da goyon baya dan shugabancin al'umma dan inganta harkar kiwon lafia a jihar mu ta Bauchi dama tarayyar Nigeria baki daya.
Ina godiya bisa lokacin ku na sauraro/karatu, Allah yayi albarka wa jihar mu ta Bauchi da tarayyar Nigeria.
Sa Hanu;
Comr Yusuf Aliyu Fada.
Chairman, Sen. Shehu Buba Free Medical Outreach Team.
17th May, 2025.