18/12/2023
*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na tara_
.....Da ɗai-ɗai s**a dinga isowa gidan. Hakan ya sake ɗaga hankalin mata dake cike da gidan ana jajantawa. Dan duk yanda akaso suyi bayani kasancewar an san sunje can gidan haka ya gagara. Baba ne kawai ke iya maimaita kalmar, “Akwai matsala. Gidan Jazool babu lafiya ƙwarai da gaske”.
Zugum-zugum akai kowa na sauraren baba cikin ƙara tsorata da jimantawa. Sai da s**a samu nitsuwa kusan ta awa ɗaya sannan s**a bada labarin abinda ya faru. Yanda Yaya Mujee ke siffanta sunga Alimah tamkar irin horror ɗin nan ya hargitsa zukatan mutane. Yanda wasu s**a firgice ma sai ka ɗauka da su aka gano. Yaya Inusa da baice komai ba tun ɗazun cikin damuwa ya ce, “Baba dole ne fa a nema iyayen yarinyar nan akan lokaci. Dan abinda na fahimta gidan nan na Jazool akwai aljanu, kuma da alama sun shiga jikin matarsa”.
“Gaskiyarka Inusa dole aɗauki mataki da wuri kam, dan barin yarinyar can a wannan halin ita kaɗai akwai tashin hankali. Bari muga a lalubo mahaifin nata”.
Kowa dake wajen ya gamsu da zancen Baban. Yayinda tausayin Alimah da JJ ya sake mamaye zukatan kowa. Sam Baba ya kasa samun number ɗin mahaifin Alimah, dole ya yanke hukuncin idan sun idar da sallar la'asar zaije shi da Yaya Mujee gidan su Alimah ɗin.
Bayan idar da sallar la'asar suna shirin wucewa gidan su Alimah kira ya samesu daga asibiti cewar JJ fa ya farka a wani yanayi. Dan a yanzu haka ma rirriƙe ake da shi. Dole su Baba s**a saki zancen zuwa gidan su Alimah s**a tafi asibiti. A yanayin da s**a sami JJ kam abun akwai tausayi, ga likitoci sun tabbatar da su basuga komai a tattare da shi ba. Brain ɗinsa lafiya lau take. Hakama fatarsa babu wata damuwa amma ga wasu irin ƙananun ƙuraje sun maidashi butsaaa babu ƙyawun gani tamkar jikin kada. Su baba da s**a fahimci komai a yanzu roƙonsu s**ai kan su masa allurar barci kawai zasu wuce da shi gida. Dan sun gano