Sabuwar Nigeria

Sabuwar Nigeria Tare ya kamata mu gina SABUWAR NAJERIYA

28/12/2024

Shirin Sabuwar Najeriya kashi na 52.

28/12/2024

Prof Mansur Sokoto ya yi kira da yan Najeriya suyi watsi da zarge zargen da Tchani yayi wa Najeriya.

28/12/2024

Wasu Ƴan Najeriya mazauna yankin da Shugaban Mulkin Sojin Nijar Abdurrahman Tchani ya ce an kai Sojojin Faransa sun bayyana abin da s**a sani kamar yadda za ku gani.

27/12/2024

*JADAWALIN SOJOJIN KASASHEN WAJE DA S**A ZAUNA A NIJAR*

*Kasar Faransa*
Ta girke dakaru 1,500, da jirage marasa matuka da na yaki masu iya tattara bayanan asirin Kasar ta Nijar da na makwabtanta. A cewarsu sun mayar da hankali ne wajen tallafa wa sojojin Nijar wajen yaki da ta'addanci.

*Kasar Amurka*
Ta girke Kimanin sojoji 1,100, wadanda s**a yi aiki daga sansanonin guda biyu masu boda da Najeriya ko kasar Libya, ita ma da tarin jirage marasa matuki masu iya tattara bayanai

*Kasar Italiya* ita ma ta girke Kimanin sojoji 300, a cewar ma'aikatar tsaron Italiya
*Tarayyar Turai*: Dakaru 50-100 turawa s**a aike don aikin horar da sojojin kasar Nijar da kuma tattara bayanai na tsawon shekaru uku.
*Kasar Jamus*
Duk da tana cikin tarayyar turai ita ma ta kara ware wasu sojoji guda 60 don nata aikin a Kasar Nijar.

A yanzu da Nijar ke kokarin kakkabe wadannan sojojin daga ƙasarta, ba fa ta tsaya da kafarta ba ne, tana maye gurbinsu ne da sojin wata kasar turawan wato sojojin Ƙasar Rasha

Duk a wannan Bajekolin da sojojin kasashen waje ke yi a kasar Nijar kuma akan bodojin Najeriya, Ba a taɓa jin Najeriya ta nuna damuwarta ko ta tsangwami ƙasar Nijar din ba, duk da kuwa Najeriya ta ki yarda a sami irin wannan sansanonin a kasarta, hasali ma akasarin masu sansanin a Nijar Najeriya s**a fara yi wa tayi, amma tace akai kasuwa. Shin a yanzu ne Nijar ke zaton za ta tilasta wa Najeriya yin adawa da duk wanda gwamnatin su ke yin adawa da shi?

26/12/2024

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata kalaman shugaban kasar Nijar da yayi kan zargin Najeriya na taimakawa ayyukan ta'addanci daga bakin Malam Abdulaziz Abdulaziz mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan yaɗa labarai.

26/12/2024

A makon da ya gabata Shugabancin Soji na Jamhuriyar Nijar yayi ta baƙaƙen addu’a da kalmomin tsana da ƙiyayya ga Najeriya da Ƴan Najeriya, har yana rokon Allah ya kawo ma Najeriya tashin hankali, yau kuma Shugaban Soji na Nijar ɗin Janar Abdourahmane Tchiani ya zo yana faɗar wasu tuhume tuhuma marasa tushe duk dan ya cigaba da ɓata wa Najeriya suna da kuma ƙirƙirar ƙiyayyar da babu ita tsakanin Najeriya da Nijar.

Wannan ya ishi mai hankali ya gane ina mutumin man ya dosa da kuma mummunan hadafin sa ga Najeriya.

Iƙirarin da Shugaban Gwamnatin Soji ta Nijar yayi akan Najeriya shaci faɗi ne; cewar Gwamnatin Najeriya. Gwamnatin Najer...
26/12/2024

Iƙirarin da Shugaban Gwamnatin Soji ta Nijar yayi akan Najeriya shaci faɗi ne; cewar Gwamnatin Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata iƙirarin da Shugaban Gwamnatin Soji Na Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani yayi a wani bidiyo da yake yawo cewa akwai alaƙa tsakanin Najeriya da Faransa don tarwatsa ƙasar Nijar.

Wannan iƙirari ne na shaci faɗi domin Najeriya bata taɓa yin alaka a bayyane ko a ɓoye ba da Faransa ko wata ƙasa don ɗaukar nauyin hare haren ta’addanci ko lalata Jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulkin da soji s**a yi a kasar.

Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin sa na Jagoran ECOWAS yayi amfani da hikima da dabara ta mulki dan tabbatar da cewa ƙasashen yammacin Afrika sun zama tsintsiya ɗaya ba tare da kallon banbancin siyasa da ke tsakanin su ba. Najeriya ta cigaba da tsayuwa tsayin daka dan tabbatar da zaman lafiya da kuma alaƙar diflomasiyya da Nijar.

Dakarun sojin Najeriya tare da hadin gwiwar Dakarun Haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa na samun nasara wajen kawo ƙarshen ta’addanci a yankin, zai zama abin tir ga wani mutum ya ƙaddara cewa Najeriya zata haɗa kai da wata ƙasar waje don kawo tarnaƙi ga zaman lafiya da tsaron ƙasashen da ke makwabta da mu.

Gwamnatin Najeriya ko wasu jami’anta basu taɓa goyon bayan wata ƙungiyar ta’addanci ba don kawo hari ga Jamhuriyar Nijar. Haka kuma babu wani waje a Najeriya da aka keɓe wa wata ƙasar waje ta gudanar da wani abu ga jamhuriyar Nijar. Muna kara maimaitawa cewa jami’an gwamnatin Najeriya na yin dukkan mai yiwuwa don tabbatar da zaman lafiya da tsaro tsakanin gwamnati da al’ummar Najeriya da Nijar, kuma muna goyon bayan su akan haka da ƙoƙarin da suke yi dan samar da haɗin gwiwa mai ƙarfi a yankin Yammacin Afrika.

Iƙirarin cewa Najeriya tana ƙoƙarin lalata noma da bututun kasar Nijar shima zance ne mara tushe, ba gaskiya bane. Najeriya ta kasance cikin taimakawa Jamhuriyar Nijar ta fuskar cigaban tattalin arziƙin su ta kan samar da makamashi da kuma ayyukan raya ƙasa, daga cikin su akwai Bututun iskar gas na Trans-Saharan da aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi. Babu hankali da tunani a ce Najeriya za ta gurgunta ayyukan da ta yi na cigaba.

Ikirarin da ake yi na kafa hedkwatar ‘yan ta’adda da ake kira Lakurawa a Jihar Sakkwato, da ake zargin Najeriya da hadin gwiwar Faransa ne s**a shirya, tabbas ba shi da tushe b***e makama. Najeriya ta kasance gaba-gaba a yankin wajen yaki da ta'addanci, tare da sadaukar da dimbin albarkatu da rayuka domin tabbatar da zaman lafiya a yankin tafkin Chadi da ma wajenta.

A kwanakin bayan na sojojin Najeriya s**a kaddamar da Operation Forest Sanity III, musamman don magance barazanar Lakurawa wanda aka sa wa suna Operation Chase Lakurawa Out. Ta yaya gwamnatin da ke yaki da ta’addancin Lakurawa za a tuhume ta da basu mafaka a cikin iyakokinta? Wadannan tuhume-tuhumen ba su da wata hujja da aka dogara, alama ce ta wani babban yunkuri na kawar da hankalin mutane daga kalubalen cikin gida da Nijar ke fuskanta.

Ana kira ga jama'a da su yi watsi da wadannan zarge-zargen na karya. Dole kuma masu irin wadannan ikirari, musamman Shugaban Soja na Jamhuriyar Nijar, su bayar da hujjoji don tabbatar da su. Duk wani yunƙuri na ɓata wa Najeriya suna a kan matsayar ECOWAS bisa ƙa'idar karɓar mulki da ya kira abinda akai a jamhuriyar Nijar ba bisa ƙa'ida ba, ba zai yi nasara ba.

A ƙarshe, zargin da shugaba Tchiani ya yi ba wai kawai ƙarya ba ne, har ma da wani yunƙuri mai na kautar da hankalin jama’a daga gazawar gwamnatinsa. Najeriya zata ci gaba da jajircewa wajen samar da zaman lafiya a yankin kuma za ta ci gaba da jagorantar kokarin magance ta'addanci da sauran kalubalen kasashen. Muna kira ga Nijar da ta mai da hankali kan tattaunawa mai ma'ana da hadin gwiwa maimakon yin zarge-zarge marasa tushe.

Mohammed Idris
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a na kasa,
Tarayyar Najeriya.

Alhamis, Disamba 26, 2024

Bayanai Akan Muhimman Tsare-Tsaren Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
25/12/2024

Bayanai Akan Muhimman Tsare-Tsaren Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu

17/12/2024

Shin da gaske ne za a cire Haraji daga dukiyar gado?

Masani kan Kimiyyar Tattalin Arziki a Najeriya Malam Ado Muhammad Abubakar yayi cikakken bayani kan zancen da ake yaɗawa cewar 'wai' sabuwar dokar haraji da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya aikewa zauren Majalisar Dokokin ƙasa don amincewa akwai batun cire wani kaso na Haraji daga dukiyar mamata.

Ayi sauraro lafiya.

*Ziyarar Kashim Shettima Ga Raudar Manzon Allah SALLALLAHU ALAIHI Wasallam*A wata ziyarar Ibada da yake yi a Kasa mai Ts...
17/12/2024

*Ziyarar Kashim Shettima Ga Raudar Manzon Allah SALLALLAHU ALAIHI Wasallam*

A wata ziyarar Ibada da yake yi a Kasa mai Tsarki, mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima ya fara yada zango a Raudhah, wato makwancin Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad SALLALLAHU ALAIHI WA ALIHI WASALLAM, da ke tsakanin gidansa da Masallacinsa a garin Madinatul Munawwara dake kasar Saudiya.

Kashim Shettima ya isa wajen
tare da rakiyar gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, da Engr Ibrahim Umar na Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya; da jami’an Ofishin Jakadancin Najeriya a Saudiyya,

Mataimakin Shugaban kasar ya yi addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da bunkasar arziki ga Nijeriya, da ma duniya baki daya.

Mataimakin shugaban kasar ya ja hankalin duniya da wannan ziyara ta wuri mai dauke da tsarki da tarihi a Musulunci, inda ya saje da dubban musulmi wajen neman yardar Allah da Salati ga Manzon Allah SALLALLAHU ALAIHI wasallam.

Da yake jawabi bayan kammala ziyarar mai cike da tarihi da ibada, mataimakin shugaban kasar ya bayyana jin dadinsa dangane da samun damar ziyartar wannan wuri mai tarin albarka, dake kunshe da lada da kuma koyarwar Annabi Muhammad (SAWA) wannan wuri, daya ne daga wurare biyu da miliyoyin Musulmi masu neman kusanci da Ubangiji, da aminci, ke dafifin zuwa ziyara.

Kungiyar ECOWAS ta bai wa Burkina Faso, Mali, da Nijar wa’adin watanni shida don su sake duba matsayarsu kan ficewa daga...
15/12/2024

Kungiyar ECOWAS ta bai wa Burkina Faso, Mali, da Nijar wa’adin watanni shida don su sake duba matsayarsu kan ficewa daga kungiyar.

An yanke wannan shawarar ne a wajen taron shugabannin kungiyar ta ECOWAS karo na 66. Sabon wa'adin zai fara aiki daga ranar 29 ga watan Janairu zuwa 29 ga Yulin shekarar 2025.
Hakan na nufin kofofin ECOWAS za su kasance a buɗe ga kasashen uku har zuwa lokacin za su fayyace matsayarsu kan ko za su dawo ko kuma sun tafi kenan.
Idan kasashen s**a tabbatar da ficewarsu, hakan na iya tasiri ga yankin ta fannin tattalin arziki, da diflomasiyya, da tsaro kazalika yana iya kawo cikas ga zirga-zirgar mutane da kayayyaki musamman na kasuwanci wanda zai ta'azzara rashin daidaito kan harkokin tattalin arziki

Kasashen uku sun kulla sabuwar kawance tsakaninsu mai taken kawancen kasashen Sahel ko (AES), da nufin samar da hadin gwiwa a fannin tsaron iyakoki.

Kazalika shugabannin kungiyar ECOWAS sun yaba da kokarin da shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal da takwaran aikinsa na kasar Togo Faure Gnassingbé s**a yi wajen ganin sun dawo da kasashen uku cikin kungiyar ECOWAS. Hukumar ta kuma kara wa'adin shugaban kasar Togo da shugaban kasar Senegal na ci gaba da aikin shiga tsakani har zuwa karshen wa'adin da ta bai wa kasashen.

14/12/2024

Shin san cewa farashin man fetur ya fara sauka a Najeriya?

Ku saurari shirin Sabuwar Najeriya kashi na 50.

12/12/2024

Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta bukaci gwamnatocin jihohi da su sanya hannu kan shirye-shirye sashin kula da tsarin samar da abinci na shugaban kasa (PFSCU) a kokarin da ake na magance matsalolin da ke hana samun wadatar abinci tare da tushen matsalolin.


Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ya bayyana cewa, irin tattalin arzikin da gwamnatin tarayya ta shuka ta hanyar kawo sababbin tsare-tsaree da bayar da tallafi a shekarar 2024 ya fara yin 'ya'ya.

Majalisar ta dauki matakin ne a ranar Alhamis yayin taronta na 147 da mataimakin shugaban ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Yayin gabatar da jawabinta, mai taimakawa shugaban kasa kan dabarun noma a ofishin mataimakin shugaban kasa, kuma shugabar sashin kula da tsarin samar da abinci na shugaban kasar, Marion Moon, ta yi karin haske kan dabarun da sashin ya gabatar don yin aiki tare da gwamnatocin jihohi wajen magance matsalar karancin abinci da kuma bunkasa harkokin noma a fadin Najeriya.

Marion ta ce shirin sashin Kula da Tsarin Abinci na Shugaban Kasar (PFSCU) zai mayar da hankali bangaren bunkasa kasuwancin amfanin gona, da hakan zai taimaka wajen inganta hanyoyin isar da kayayyaki hadi da hanzarta aiwatar da manufofin da aka sanya a cikin shirin sabunta fata (Renewed Hope) na gwamnatin Tinubu da kuma cin ma manufofin gwamnatocin jihohin

A nata bangaren, majalisar tattalin arzikin ta kasa ta yaba da jawabin na shugabar shirin, yayin da ta yi kira ga gwamnatocin jihohi su shiga cikin wannan shiri, har ila yau, majalisar ta bukaci sashin kula da tsarin samar da abinci na shugaban kasar (PFSCU) da su gabatar da nasarorin da s**a samu a taron majalisar na gaba

Gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar da sabon tsari da ya fara farfaɗo da darajar Naira. A karshen watan Nuwamba da ya ga...
11/12/2024

Gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar da sabon tsari da ya fara farfaɗo da darajar Naira.

A karshen watan Nuwamba da ya gabata, Dalar Amurka ta kai N1,672.69 zuwa N1,730, tsakanin farashin CBN da na kasuwar bayan fage, amma a yanzu, dalar ta karya zuwa N1,525 wanda ya kai kusan kimanin kashi 10 cikin ɗari. Wannan ya samu ne sakamakon sabon tsarin EFEMS da gwamnatin Tinubu ta ƙirƙiro dan samar da daidaito da kuma sanya idanu akan hada-hadar kuɗaɗen waje a Najeriya.

Yaya wannan tsarin yake?

Tsarin EFEMS wato (Electronic Foreign Exchange Matching System) tsari ne da CBN ta samar da shi da ya kawar da tsohon tsarin da ake kai na AFEM wato (Autonomous Foreign Exchange Market.

Kamar yadda ma’abota siyan Dollar suke yi a tsarin P2P dake kan Binance, kowa zai iya sanya farashin da yake siyan Dollar ko kuma ya Siyar, zaɓi ya rage ga wanda zai siya ya zaɓi inda ta fi sauƙi ya saya a ƙarƙashin kulawar Binance. Kwatankwacin haka wannan tsarin na EFEMS yake, bankuna za su sanya farashin su akai, masu siya sai su zaɓi su siya daga farashi mafi sauƙi ƙarƙashin kulawar CBN. Hakan ya sa farashin Dalar samun daidaito saɓanin tsarin baya na AFEM da kowanne banki zai sanya farashin da ya ga dama ba tare da kulawar CBN ba, kuma saidai mai son siya ya siya a haka muddin a nan bankin yake son siya, babu zaɓin neman sauƙi daga wani wajen ta bankin ka ko da farashin su ya fi sauƙi akan bankin ka.

A yanzu dukkan bankuna suna kan wannan tsarin na EFEMS, kuma nan da lokaci kaɗan zai haɗe dukkan kamfanonin canji da suke da lasisi a faɗin ƙasar, hakan zai tsayar da farashin dollar ya zama bai ɗaya tare da samun sauƙin tashin ta da ake samu a baya da kuma kulawar yadda ake hada-hadar kuɗin daga CBN.

Wani abu da gwamnatin tarayyar ta ƙara yi shi ne, tayi ƙoƙarin samar da hannun jari daga ƙasashen ƙetare wanda hakan ya sanya yawaitar Dalar a Najeriya wanda zai cigaba da rage farashin ta da ɗaga darajar Naira, sai kuma ƙaruwar kuɗaɗen haraji da ƙasar ke samu daga mai, da kuma sababbin tsare-tsaren inganta tattalin arziƙin ƙasar ta ɗabbaƙa.

*Dubban Yan Najeriya, Ciki Har Da Nakasassu ne Ke Neman Samin Aiki A Hukumar NNPC*A wani yanayi da ba kasafai aka saba g...
07/12/2024

*Dubban Yan Najeriya, Ciki Har Da Nakasassu ne Ke Neman Samin Aiki A Hukumar NNPC*

A wani yanayi da ba kasafai aka saba gani ba, ƴan Najeriya kimanin 45,689 ne ke jarabawar share fagen samin aiki a babban kamfanin mai na ƙasar, wato NNPC,

Jarabawar wadda ake yinta a bayyane don bai wa kowane ɗan ƙasa damar samin aikin yi, na daga cikin manufofin gwamnatin shugaba Tinubu na ganin an daina mayar da talakawan ƙasar saniyar-ware a bangaren samin aiki a manya da kananan maikatun kasar.

Tuni dai masu rubuta Jarabawar daukar ma’aikatar, ciki har da masu bukata ta musamman da aka tanadar wa nasu wurin, s**a duƙufa akan na’urorin da aka tanada a cibiyoyin kamfanin NNPCL dake sassa daban-daban na fadin kasar nan.

Masu sa-ido akan sahihancin jarabawar sun haɗa da shugaban gudanarwar kamfanin Malam Mele Kyari wanda a safiyar yau ya ziyarci cibiyar samar da albarkatu ta Ansar-Ud-Deen Society Centenary Resource Center da ke Maitama a Abuja, don tabbatar da ana bin duka tsarikan da aka shimfida don tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Malam Kyari ya sake jaddada cewa ma'aikatar na shirye da ɗaukan wadanda s**a cancanta aiki, kuma zasu fito ne daga cikin mutane 45,689 dake neman gurbin aikin a faďin ƙasar

07/12/2024

Gwamnatin Tarayya ta ce sabuwar dokar haraji da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya aikewa zauren Majalisar Dokokin Kasar nan ba zata fifita wani yanki na Najeriya ba.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma Malam Muhammad Idris ne ya bayyana hakan, lokacin da Ƙungiyar Ƙwararrun Jami'an Yaɗa Labarai ta (NIPR) ta shirya taron jin ra'ayoyin jama'a kan sabuwar dokar haraji.

Muhammad Idris yace ganin yadda wannan sabuwar doka ta tada hazo a tsakanin yan Najeriya, akwai buƙatar wayar da kan al'umma da bayyana musu abubuwan da dokar ta kunsa.

Ministan ya ce, Gwamnati na son aiwatar da tsarin ne da kyakyawar manufa domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Abubuwan da Yarjejeniyar Najeriya da Faransa ta ƙunsaA makon nan, an ƙulla yarjejeniya tsakanin Najeriya da Faransa don ...
05/12/2024

Abubuwan da Yarjejeniyar Najeriya da Faransa ta ƙunsa

A makon nan, an ƙulla yarjejeniya tsakanin Najeriya da Faransa don samar da ayyukan hadin gwiwa da zasu inganta harkokin ma’adanai a kasashen biyu.

Ma'adanan sun haɗa da jan karfe (Copper), Lithium, Nickel, da Cobalt.

A cikin yarjejeniyar da kasashen biyu s**a rattaba hannu yayin ziyarar shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙasar ta Faransa, sun amince da yin hadin gwiwa kan bincike da horas da daliban ƙasashen biyu domin musayar ilimi da samar da kwarewa.

Babban abin da ke cikin yarjejeniyar shine haɓaka ayyukan hakar ma'adinai masu ɗorewa ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen da zasu rage gurɓatar muhalli da ruwa yayin haƙar ma’adinai.

Ministan ci gaban ma’adanai na Najeriya, Dr Dele Alake ne ya rattaba hannu akan yarjejeniyar a madadin Najeriya, yayin da wakilin ma’aikatar kula da ma’adanai da karafa na Faransa, Benjamin Gallezot, ya sanya hannu a madadin Faransa.

Ana sa ran wannan yarjejeniya za ta bude sabbin damammaki na gyaran ramuka sama da 2,000 da aka yi watsi da su a cikin kasar ta hanyar shirinta na ayyukan gyara muhalli da haƙar ma'adinai.

Wannan yarjejeniyar na daga kokarin gwamnatin Tinubu na inganta bangaren haƙar ma’adinan domin muyi kafaɗa-kafaɗa da takwarorin mu na duniya.

*Gwamnati Za ta Saurari Koken Mutane kan Sabon Daftarin Haraji-*Ministan yaɗa labarai ,Muhammad Idris Malagi ne ya sanar...
04/12/2024

*Gwamnati Za ta Saurari Koken Mutane kan Sabon Daftarin Haraji-*

Ministan yaɗa labarai ,Muhammad Idris Malagi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa
Shugaba Tinubu ya umurci ma’aikatar shari’a da ta yi aiki tare da Majalisar tarayya kan kudirin gyara harajin

Bugu da kari Ministan ya ba da tabbacin cewa za a warware matsalolin da ake da su a Daftarin, kuma babu kamshin gaskiya kan zargin cewa za a kara wa talakan Najeriya sabon nauyin haraji ko kuma a durkusar da wasu cibiyoyi ko hukumomi da ke aiyukan raya 'yan kasa irinsu NASENI, Ko NITDA da sauransu.

Ministan ya gargadi 'yan kasa da su guji yaɗa labaran karya, domin suna da illa da raba kan al'ummar kasa

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sabuwar Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sabuwar Nigeria:

Videos

Share

Category