Sashen Hausa Muryar Najeriya, Abuja

Sashen Hausa Muryar Najeriya, Abuja VON-HAUSA (MURYAR NAJERIYA) YA FADADA MU'AMULLA DA MASU SAURARO KAI TSAYE DOMIN BAYYANA RA'AYOYINKU

15/01/2025

BULLAR MURAR TSINTSAYE A JIHAR KANO

Tun bayan da aka samu labarin bullar murar tsintsaye a jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya mahukunta s**a tashi tsaye wajen fadakar da alโ€™umma kan matakan da ya k**ata su dauka don kaucewa wannan cuta da kan k**a dabbobi har da sanadi na shafar dan Adam.

To ko wane hali a ke ciki a jihar ta Kano kawo yanzu? Tambayar kenan da abokin aikinmu a Kano Yusuf Bala yayi wa Dr. Abdullahi Abubakar Gaya likitan da ya fara gano alamun bayyanar cutar .

15/01/2025

๐—ž๐—”๐—•๐—œ๐—ฅ๐—จ ๐—”๐—Ÿ๐—›๐—”๐—ฆ๐—ฆ๐—”๐—ก ๐—ฅ๐—จ๐—ฅ๐—จ๐—  ๐—ฌ๐—” ๐—š๐—ช๐—”๐—ก๐—š๐—ช๐—”๐—๐—˜ ๐—”๐—Ÿโ€™๐—จ๐— ๐— ๐—”๐—ฅ ๐— ๐—”๐—ญ๐—”๐—•๐—”๐—ฅ๐—ฆ๐—” ๐—” ๐—™๐—”๐—ก๐—ก๐—œ๐—ก ๐—œ๐—Ÿ๐—œ๐— ๐—œ ๐—•๐—”๐—ฌ๐—” ๐—š๐—” ๐—”๐—•๐—”๐—•๐—˜๐—ก ๐— ๐—ข๐—ฅ๐—˜ ๐—ฅ๐—”๐—ฌ๐—จ๐—ช๐—” ๐—” ๐—ž๐—”๐—ก๐—ข

Sashen Hausa Muryar Najeriya (VON) ya leka wasu sassa na yankin mazabar dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano da Bunkure da Kibiya don gani a kasa irin ayyukan da alโ€™ummar wannan mazaba suke amfana daga ayyukan wannan danmajalisa. da ke wakiltar wadannan al'umma daga jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ga dai karin bayani a rahoton da wakilinmu a Kano Yusuf Bala ya hada mana.

'YANSANDA SUN FAFATA DA MASU FASHIN TEKU A ORON-CALABARWani harin "yanfashin teku yayi sanadi na samun raunuka da bacewa...
14/01/2025

'YANSANDA SUN FAFATA DA MASU FASHIN TEKU A ORON-CALABAR

Wani harin "yanfashin teku yayi sanadi na samun raunuka da bacewar 'dansandan ruwa.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 11 ga watan Janairu, 2025 a yankin mashigar ruwa ta Oron-Calabar a lokacin da suke aiki.

A cewar rundunar 'yansandan na Akwa Ibom masu dauke da mak**ai 24 :cikin kakin soja a jiragen ruwa su uku sun bude wuta ga jami'an 'yansandan lokacin da s**a fita aiki.

Duk da kokari da dakarun s**a yi na gwabzawa da 'yanfashin wasu daga cikinsu sun samu raunuka k**ar Insfekta Sunday Usuyak da Edet Enenyi bayan harbin bindiga da s**a samu raunikan bindiga yayin da sifeto Udi Emenyi ba a gan shi ba.

Kwamishinan 'yansanda a jihar CP Baba Mohammed Azare, ya ziyarci inda lamarin ya faru inda
aka kara tsaro a yankin.

Rundunar 'yansandan ta bayyana cewa za ta yi aiki tukuru don tabbatar da ganin an k**a masu laifi a yankin .

Sai rundunar ta bukacibal'umma su ba da hadin kai da ya dace wajen samar wa jami'an bayanai.

Rundunar 'yansandan da ke Akwa Ibom sun bayyana cewa za su ci gaba da ba wa al'umma bayani kan halin da ake ciki.

๐—ž๐—”๐—ก๐—ข: ๐—š๐—ช๐—”๐— ๐—ก๐—” ๐—ฌ๐—จ๐—ฆ๐—จ๐—™ ๐—ฌ๐—” ๐—ฅ๐—”๐—•๐—” ๐—ž๐—”๐—ฌ๐—”๐—ก ๐— ๐—”๐—ž๐—”๐—ฅ๐—”๐—ก๐—ง๐—” ๐—ž๐—ฌ๐—”๐—จ๐—ง๐—” ๐—š๐—” ๐——๐—”๐—Ÿ๐—œ๐—•๐—”๐—œ ๐—ฆ๐—”๐— ๐—” ๐——๐—” ๐Ÿณ๐Ÿด๐Ÿฌ.๐Ÿฌ๐Ÿฌ๐ŸฌA wani gagrumin yunkuri na tallafa wa fannin...
13/01/2025

๐—ž๐—”๐—ก๐—ข: ๐—š๐—ช๐—”๐— ๐—ก๐—” ๐—ฌ๐—จ๐—ฆ๐—จ๐—™ ๐—ฌ๐—” ๐—ฅ๐—”๐—•๐—” ๐—ž๐—”๐—ฌ๐—”๐—ก ๐— ๐—”๐—ž๐—”๐—ฅ๐—”๐—ก๐—ง๐—” ๐—ž๐—ฌ๐—”๐—จ๐—ง๐—” ๐—š๐—” ๐——๐—”๐—Ÿ๐—œ๐—•๐—”๐—œ ๐—ฆ๐—”๐— ๐—” ๐——๐—” ๐Ÿณ๐Ÿด๐Ÿฌ.๐Ÿฌ๐Ÿฌ๐Ÿฌ

A wani gagrumin yunkuri na tallafa wa fannin ilimi a jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya, gwamnatin jihar ta kaddamar da raba kayan makaranta kyauta ga dalibai 789,363 a daukacin makarantun firamare 7,092 da ke kananan hukumomi 44 na fadin jihar ta Kano.

Gwamnan da yake kaddamar da aikin rabon kayan makarantar ga dalibai a jihar ya bayyana cewa daga martabar ilimi shine abin da gwamnatinsa ta ba wa fifiko.

Gwamna Yusuf ya bukaci iyaye da masu lura da daliban su tabbatar da ganin cewa daliban suna zuwa makaranta yayin da gwammnati take nata bangaren.

"Yadda muka farfado da makarantu da gina sabbi da kyautata wa malamai, haka sauran kayayyaki k**ar alluna da kujeru da bencina da allin rubutu da sauransu. "

A cewar gwamnan wannan zai karfafa gwiwar daliban su fita zuwa makaranta, ganin an samar masu kayan koyo da koyarwa ga kuma kayan makaranta.

โ€œZa mu raba wa yara kaya na sawa rigunan maza da mata 789,363 mun ba da kwangilar kayan an kuma dinka su . Muna taya iyaye da yara murna, kuma kayan nan kyauta ne. Nan gaba kadan za mu raba kwamfuta ta yadda yara da ke gaba da firamare za su iya karatu da wannan naโ€™ura.โ€

A cewar shugaban hukumar ilimin baidaya a jihar ta Kano (SUBEB), Yusuf Kabir wannan ba da kaya ga daliban ya zo a lokacin da ya dace wanda zai tallafi gwiwar iyaye da yaran.

Kwamishinan ilimi a jihar ta Kano Ali Haruna Makoda yace maโ€™aikatar ta yi kokari wajen samar da horo ga malamai da sama masu kayan koyo da koyarwa wanda zai karfafa wa malaman gwiwa wajen aikinsu abin da ke zama kalubale garesu su samar da ilimin ga manyan na gobe.

Yace ilimi shine abu da gwamnatin Kano tafi bawa fifiko, don samar da alโ€™umma tagari anan gaba.

Gwamnan Kano ya yaba wa kwamitin da yayi aikin samar da tufafin daliban ganin yadda ya dawo da rarar kudi miliyan dari da yace za a ci gaba da amfani da su don samar wa daliban kayan makaranta.

13/01/2025

๐——๐—”๐—ก๐—š๐—ข๐—ง๐—˜ ๐—œ๐—ฆ๐—Ÿ๐—”๐— ๐—œ๐—ฌ๐—” ๐—ง๐—” ๐—ฌ๐—”๐—ฌ๐—˜ ๐——๐—”๐—Ÿ๐—œ๐—•๐—”๐—œ ๐—ฆ๐—”๐— ๐—” ๐——๐—” ๐Ÿญ๐Ÿฑ๐Ÿฌ ๐—” ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฑ

A yayin zantawa da wakilinmu Yusuf Bala a Kano a wannan Lahadi 12-01-2025 shugaban makarantar Gwani Sagir Usman Madabo (Mai Sittin) ya kalubalanci daliban su zama masu tarbiya da koyi da abubuwan da s**a koya cikin darusan Alqur'ani mai gurma.

Gwani Maii Sittin ya kuma ja hankali iyaye da shugabanni da su kula sosai wajen tallafar irin wadannan makarantu na tarbiya tun daga tushe

12/01/2025

๐——๐—”๐— ๐—•๐—”๐—ฅ๐—จ๐—ช๐—”๐—ฅ ๐— ๐—”๐—ฆ๐—”๐—ฅ๐—”๐—จ๐—ง๐—”๐—ฅ ๐—ž๐—”๐—ก๐—ข:

Aminu Babba Dan'Agundi wanda ke zama danmajalisar Sarki kuma Sarkin Dawaki Babba yayi Karin haske kan matsayar bangaren Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero a dangane da hukuncin Kotun daukaka kara ta Tarayya da ke Abuja.

A cewar Dan'Agundi Jama'a da dama basu fahimci abin da Kotun ke nufi ba wanda akwai bukatar a yi masu fashin baki.

A yayin zantawarsa da manema labarai karamar fadar Sarki da ke gidan Nasarawa a birnin Kano Dan'Agundi yace bai k**ata wani bangare a wannan shari'a yayi ikirarin nasara ba har sai an kammala shari'a don ya gabatar da kokensa ga kotun koli.

Ga dai karin bayani daga bakin Sarkin Dawaki Babba Aminu Babba Dan'Agundi

11/01/2025

๐—ฆ๐—จ๐—ช๐—” ๐—ž๐—˜ ๐—ญ๐—”๐— ๐—” ๐— ๐—”๐— ๐—•๐—ข๐—•๐—œ๐—ก ๐—ž๐—จ๐—ก๐—š๐—œ๐—ฌ๐—”๐—ฅ ๐—ง๐—ฆ๐—ข๐—™๐—”๐—™๐—™๐—œ๐—ก ๐—ฆ๐—ข๐—๐—ข๐—๐—œ?

Ko wane jami'in sojan Najeriya da ya gama aiki lafiya nada hurumin zama mamba a kungiyar tsoffin Sojojin kasar, wato Nigerian Legion inji Manjo Janaral Abdulmalik Jibrin Mai ritaya,

Shugaban kungiyar na kasa ya bayyana haka yayin ziyarar da ya kawo nan gidan Rediyon Muryar Najeriya VON a Abuja Fadar Gwamnatin Najeriya.

11/01/2025

๐—ฅ๐—œ๐—ž๐—œ๐—–๐—œ๐—ก ๐—ฆ๐—”๐—ฅ๐—”๐—จ๐—ง๐—”๐—ฅ ๐—ž๐—”๐—ก๐—ข: ๐—š๐—ช๐—”๐— ๐—ก๐—”๐—ง๐—œ๐—ก ๐—ž๐—”๐—ก๐—ข ๐—ง๐—” ๐—•๐—”๐—ฌ๐—ฌ๐—”๐—ก๐—” ๐— ๐—”๐—ง๐—ฆ๐—”๐—ฌ๐—”๐—ฅ๐—ง๐—” ๐—” ๐——๐—”๐—ก๐—š๐—”๐—ก๐—˜ ๐——๐—” ๐—›๐—จ๐—ž๐—จ๐—ก๐—–๐—œ๐—ก ๐—ž๐—ข๐—ง๐—จ๐—ก ๐——๐—”๐—จ๐—ž๐—”๐—ž๐—” ๐—ž๐—”๐—ฅ๐—”

Kwamishinan shari'a kuma Atoni Janar Barista Haruna Isah Dederi yayi Karin haske ga manema labarai, inda gwamnatin jihar ta nuna gamsuwarta da hukuncin kotun tarayyar k**ar yadda za a jinkarin bayani.

GWAMNATIN KANO TA BIYA 'YANFANSHO NAIRA MILIYAN DUBU 16Gwamnatin jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ta kashe Naira ...
09/01/2025

GWAMNATIN KANO TA BIYA 'YANFANSHO NAIRA MILIYAN DUBU 16

Gwamnatin jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ta kashe Naira miliyan dubu 16 don biyan hakkin โ€˜yanfansho a jihar.
Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a wannan Alhamis lokacin da ya kaddamar da biyan naira biliyan dubu 5 ga wasu rukunin โ€˜yan fansho a jihar.

Gwamna Yusuf a Karo na uku ya amince da biyan Naira biliyan 5 ga 'yanfansho kudinsu na giratuti da wadanda s**a rasu suke neman hakkinsu a hannun gwamnatin ta Kano.

Abu Muhammad Fagge shugaban hukumar fansho ta jihar Kano yace wannan tsari da gwamnan yake kai na taba rayuwar mutanen da s**a sadaukar da lokutansu wajen raya jihar ta Kano a lokacin da suke lokacin aikinsu kafin su yi ritaya.

Gwamnan y ace za su biya kudin kai tsaye a asusun wadanda s**a amfana da wannan tsari na biyan giratuti, wanda wannan shine na karo na uku a baya an biya miliyan dubu 11 ga kuma miliyan dubu 5.

Yace mun ware kudi biliyan 5 don biyan haklkokinsu kuma ina fadi anan cewa za mu biya kudin ne ta asusun bankuna, ba biyan kudi hannu da hannu ba, ba za mu bari abin da ya faru a baya a lokutan gwamnatin baya ya sake faruwa ba.

Mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdusalam yace โ€˜yanfansho tsawon shekaru sun sha wahala a baya. โ€œโ€™Yanfansho sun sha matabubu basu san ma abin da ake biyansu a wata ba sai abin da s**a gani a gwamnatin baya. Ballantana kudin giratutiโ€

Da dama dai cikin โ€˜yanfansho da aka ware za su amfana da kudaden a wannan rukuni sun bayyana farin cikinsu yadda a wajen bikin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya latsa kwamfutar maโ€™aikatan banki s**a fara samun kudadensu k**ar yadda s**a bayyana.

Idiris Garba dakataโ€tsohon hedimasta shekara tara da gama aiki sai yau Allah yay aye min kudina ya shigo miliyan biyu da dubu dari tara da doriya. โ€

Tijjani Inuwa Adamu โ€œNayi aiki a maaikatar ilimi 2016 na kammala aiki yau kudina sun shiga naira miliyan uku da dubu dari shida da doriya Alhamdulillah.โ€

Shugaban kungiyar โ€˜yanfansho ta kasa a Najeriya Godwin Abomesi ya y aba wa gwamnan na Kano wanda yace tun daga lokacin da yah au mulki ya gaji kudadade hakkin โ€˜yan fansho sama da naira miliyan dubu 40 wanda sannu a hankali yake ragrewa.

A cikin malaman da s**a halarci taron sun hadar da shugaban hukumar Hisbah Malam Aminu Daurawa da ya bayyana abin da gwamnan yayi a matsayin abin da ke zama ko yi da umarnin fiyayyen halitta S.A.W "Abin da Gwamna Yusuf ke yi abu ne da ya dace kasancewar Annabi S.A.W ya nunar da bukatar ganin an biya mutum hakkinsa bayan yayi aiki tun kafin ma gumun jikinsa ya bushe."

Wadanda s**a halarci taron Wakilin Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu da Sarkin Karaye, da wakilin Sarkin Gaya da wakilin sarkin Rano.

TSOHON SHUGABAN KASCO YA ZARGI HUKUMAR KARBAR KORAFE-KORAFE DA KWACE MASA KADARORI DUK DA UMARNIN KOTU A KANO Tsohon shu...
08/01/2025

TSOHON SHUGABAN KASCO YA ZARGI HUKUMAR KARBAR KORAFE-KORAFE DA KWACE MASA KADARORI DUK DA UMARNIN KOTU A KANO

Tsohon shugaban kamfanin samar da albarkatun gona a jihar Kano KASCO Dr. Bala Inuwa ya zargi hukumar karbar korafe-korafe da rashin mutunta umarnin kotu ta hanyar karbe masa kadarori da ma kwace iko da su.

Bala ya fada wa manema labarai a ranar Laraba cewa hukumar PCACC ta karbe iko na wasu kadarorinsa na biliyoyin naira wanda hakan ya sabawa umarnin kotu na tsayar da yin haka ga duk wata hukuma har sai ta kammala shariโ€™ar da ke gabanta.

Yace kadarorin nasa da aka ajiye sun hadar da tarin buhunhunan takin zamani da injinan markade da wasu kayan ayyukan gona hukumar ta karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta karbe su duk da umarnin kotu.

Bala ya bayyana cewa shariโ€™ar mai lamba K/M 1563/2024 da ke gaban mai shariโ€™a Aisha Ya'u tsakanin Bala Inuwa Muhammad da Safiyanu Hamisu da aka gabatar a gabanta kan batun kamfanin da hukumar โ€˜yansanda, matsayar da kotun ta dauka a ranar 19 ga Agusta, 2024 ta ba wa Bala Inuwa rinjaye. Har ila yau a umarnin da kotun ta bayar ta haramta yin amfani da karfi wajen shiga kamfanin da ke lamba 157 Kumbotso Rasha a karamar hukumar Kumbotso wajen daukar duk wani abu da za a iya fita da shi daga kamfanin da sunan an je binciken Bala Inuwa Muhammad da karbe masa kadarori ko hana shi gudanar da kasuwancin kamfanin duk sun sabawa doka.

Hukuncin da kotun ta fitar k**ar yadda aka nunawa manema labarai ya nunar da cewa duk wani kokari na hukumar ta PCACC na karbar kadarorin โ€œna iya zama abin da ya saba wa doka da yin karantsaye ga kundin tsarin mulkin kasa da take hakki na me kara kan abubuwan da ya mallaka wadanda za a iya motsasu da wadanda ba za a iya motsa su ba, k**ar yadda sashi na 44 na kundin tsarin mulikin Najeriya na 1999 ya tanada.โ€

Bala Inuwa ya kuma bayyana cewa kotu ta kuma ba da umarni na janyewar โ€˜yansanda daga kamfanin nasa a lamba 157 Kumbotso Rasha a karamar hukumar Kumbotso ta yadda zai samu cikakken โ€˜yanci na amfani da kayayyakin da ke zama mallakarsa.

Kazalika a cewar Bala Inuwa Muhammad bayan wanda yake kara yaki amincewa da bin umarnin kotu na farko ya kuma garzayawa kotu da neman kotu ta hana wanda yake karar da โ€˜yansanda da kwamishinan โ€˜yansanda da hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar ko su da kansu ko wakilansu ko masu yi masu hidima ko wakilai da kada su kuskura su shiga kamfanin mai lamba 157 da ke Kumbotso Rasha ko su sa baki kan harkokinsa ko mamaya ta kowace fuska.

Sai dai a nasa martani shugaban hukumar da ke karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa a Kano PCACC Barista Muhyi Magaji Rimin Gado yayi watsi da zarge-zargen inda yace duk umarnin kotu da Bala Muhammad ke da su suna da alamar tambaya, โ€œba za a iya kafa hujja da su ba a fagen shariโ€™a.โ€

Rimin Gado ya jaddada cewa umarnin da aka bayar na hana shi gudanar da aikinsa ba za a iya amfani da su ba sun riga sun gama aiki tun a 2024.

Haka kuma wasu umarnin sun shafi โ€˜yansanda ne da suke a kamfanin da ake magana a kansa, kuma tuni aka kwashe su, wannan kuma ba zai hana su gudanar da aikinsu ta wata hanyar ba, โ€Don haka ne muka yi amfani da jamiโ€™an hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa ta KAROTA don aiwatar da aikinmu k**ar yadda sashi na 58 na kundin dokar da ta tanadi hukumar ya tanadar.

Shugaban Najeriya  Bola Ahmed Tinubu, ya ce shugabannin Afrika za su cigaba da jajircewa wajen fitar da alโ€™ummarsu daga ...
08/01/2025

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ce shugabannin Afrika za su cigaba da jajircewa wajen fitar da alโ€™ummarsu daga ฦ™angin talauci.

โ€œZa mu fitar da al'ummarmu daga kangin talauci, mu gina tattalin arziki mai ษ—orewa a kan kan mu "

Shugaban ya bayyana haka ne a birnin Accra na kasar Ghana yayin da ya kasance babban bako a wajen bikin rrantsar da Shugaba John Mahama na kasar Ghana.

YAKI DA TALAUCI- GWAMNATIN KANO TA TALLAFI MATA 41,600Gwamnatin jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya  karkashin jagor...
08/01/2025

YAKI DA TALAUCI- GWAMNATIN KANO TA TALLAFI MATA 41,600

Gwamnatin jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta dora a ci gaba da tallafa wa mata da jari a kafatanin kananan hukumomin jihar 44 na jihar, inda a wannan Talata ta tallafa wa mata 5,200 wanda ke zama cikin alkawarun da gwamnatin ta yi masu a yayin yakin neman zabe a 2023.

A cewar Gwamna Yusuf tun bayan da a watan Mayu,2024 gwamnatin Kano ta kaddamar da aikin ba da tallafin ga mata kawo yanzu an tallafi mata 41,600 a fafutuka ta zakulo su daga bakin talauci ta yadda su ma za su ba da tasu gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin Kano.

โ€œMun dukufa wajen ba da tallafin 50,000 kowane wata ga mata 5,200 saboda irin gudunmawar da suke bayarwa wajen gina kasa bata misaltuwa.โ€ a cewar Gwamna Yusuf.

Gwamnan yace idan ba a manta ba a jadawali da aka fitar na rahoto kan yadda talauci ke addabar alโ€™umma a Najeriya ya nunar da cewa sama da mutane miliyan 10 na fama da talauci ta fuskoki da dama.

โ€œWannan ya sanya muka dukufa wajen fitar da tsare-tsare da za su fitar da miliyoyin alโ€™umma daga talauci da yardar Allah.โ€

A cewar gwamnan sanin wannan ya sa ba za su tsaya ga ba da jari kadai ba har ma da ilimi da dabarun yin sanaโ€™a ta yadda za su inganta rayuwarsu.

Wannan na zuwa baya ga tarin tsare-tsare a fannoni da s**a hadar da ilimi da lafiya da wadata jihar da abinci da tsaro da bunkasar birane da samar da damarmaki ga matasa da matan.

Gwamnan yace naira 50,000 da aka ba wa matan ba bashi bane fatan da suke da shi shine su yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace don fatattakar talauci daga cikin alโ€™umma ba kawai ta hanyar sama wa kansu abin yi ba har ma da daukar wasu aikin.

A karshe gwamnan ya yaba da karfafa gwiwa da ya samu daga kamfanin harkokin sadarwa na Leg-wide da hadin gwiwar hukumar da ke kula da kanana da matsakaitan masanaโ€™antu ta SMEDAN da s**a bayyana shi a matsayin gwarzo me tallafar kanana da matsakaitan masu masanaโ€™antu a 2024.

GWAMNAN KANO YA NADA SABBIN KWAMISHINONI DA WASU MUKAMAIGwamnan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Abba Kabir Yusuf...
06/01/2025

GWAMNAN KANO YA NADA SABBIN KWAMISHINONI DA WASU MUKAMAI

Gwamnan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Abba Kabir Yusuf ya nada sabbin kwamishinoni da wasu mashawarta na musamman ga gwamnan baya ga manyan sakatarori shida a ma'aikatu na gwamntin jihar.

Gwamnan ya dauki wannan mataki a kokari na kara karfafa gwamnatinsa ta yadda al'umma za su sharbi romon dimukuradiyya k**ar yadda ya bayyana bayan karbar rantsuwar k**a aiki da s**a yi karkashin jagorancin Kwamishinan shari'a kuma Atoni Janar Barista Haruna Isah Dederi.

Da yake jawabi a yayin rrantsar da sabbin wadannan masu muk**ai a fadar gwamnatin ta Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa zai bibiyi ayyukan dukkanin kwamishinonin da Mashawartan na musamman 13 da manyan sakatarori 6 a manyan ma'aikatu na gwamnwtin jihar don tabbatar da ganin sun gudanar da aiki bisa kwarewa da bin ka'idoji.

Kwamishinoni bakwai sune:

Dr.Dahiru Muhammad Hashim Kwamishinan muhalli da Dr. Gaddafi da Nura Iro Ma'aji mร 'aikatar Kula da harkokin jama'a da Shehu Wada Sagagi Kwamishinan harkokin kasuwanci da ziba jari da Abdulkadir Abdussalam Kwamishinan raya karkara da Dr.Ismail Aliyu Danmaraya da Com.Ibrahim Abdullahi Wayya Kwamishinan yada labarai.

Manyan sakatarori; Bashir Baffa Muhd ma'aikatar ilimi Fatima Adamu ma'aikatar raya karkara da Pharm. Aminu Bashir ma'aikatar lafiya da Dr.Bashir Sunusi ma'aikatar ayyukan gona ida Injiniya Abdurrazak Haruna mร aikatar albarkatun ruwa.

Har ila yau ckin sabbin nade-naden sun hadar da Ahmad Muhammad Speaker Mashawarcin na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai da Malam Sani Abdullahi Tofa mashawarci na musamman kan ayyuka na musamman.da Farfesa Tijjani Muhammad Naniya mashawarci kan harkokin masarautu da Sani Musa Danja kan harkokin matasa da wasanni da Fatima Abubakar da Sani Adamu Yola da Dakta Ibrahim Musa da Ahmad Muhammad Speaker da sauransu.

Gwamnan ya bukaci sabbin wadanda aka nada da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu ta yadda za su dace da manufofin gwamnatin jihar ta Kano.

JAWABIN SHUGABAN NAJERIYA CIKIN HARSHEN TURANCI
02/01/2025

JAWABIN SHUGABAN NAJERIYA CIKIN HARSHEN TURANCI

NEW YEAR MESSAGE TO NIGERIANS

By President Bola Ahmed Tinubu Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Fellow Nigerians,

As we enter 2025, I wish everyone a happy and prosperous New Year. May you be rich in joy, success, and good health.

As the new year dawns, it brings many hopes, aspirations, and prospects for better days. By the grace of God, 2025 will be a year of great promise in which we will fulfill our collective desires.

Though 2024 posed numerous challenges to our citizens and households, I am confident that the New Year will bring brighter days.

Economic indicators point to a positive and encouraging outlook for our nation. Fuel prices have gradually decreased, and we recorded foreign trade surpluses in three consecutive quarters. Foreign reserves have risen, and the Naira has strengthened against the US dollar, bringing greater stability.

The stock market's record growth has generated trillions of naira in wealth, and the surge in foreign investment reflects renewed confidence in our economy. Nevertheless, the cost of food and essential drugs remained a significant concern for many Nigerian households in 2024.

In 2025, our government is committed to intensifying efforts to lower these costs by boosting food production and promoting local manufacturing of essential drugs and other medical supplies. We are resolute in our ambition to reduce inflation from its current high of 34.6% to 15%. With diligent work and God's help, we will achieve this goal and provide relief to all our people.

In this new year, my administration will further consolidate and increase access to credit for individuals and critical sectors of the economy to boost national economic output.

To achieve this, the federal government will establish the National Credit Guarantee Company to expand risk-sharing instruments for financial institutions and enterprises.

The Companyโ€”expected to start operations before the end of the second quarterโ€”is a partnership of government institutions, such as the Bank of Industry, Nigerian Consumer Credit Corporation, the Nigerian Sovereign Investment Agency, and Ministry of Finance Incorporated, the private sector, and multilateral institutions.

This initiative will strengthen the confidence of the financial system, expand credit access, and support under-served groups such as women and youth. It will drive growth, re-industrialisation, and better living standards for our people.

On a personal note, thank you for placing your confidence in me as your president. Your trust humbles me, and I promise to continue serving you diligently and wholeheartedly.

We will continue to embark on necessary reforms to foster sustainable growth and prosperity for our nation.

I seek your cooperation and collaboration at all times as we pursue our goal of a one trillion-dollar economy. Let us stay focused and united.

We are on the right path to building a great Nigeria that will work for everyone. Let us not get distracted by a tiny segment of our population that still sees things through the prisms of politics, ethnicity, region, and religion.

CITIZENSHIP

To achieve our national goals and objectives, we must become better citizens and uncompromising in our devotion and allegiance to Nigeria.

Citizensโ€™ moral rectitude and faith in our country are fundamental to the success of the Renewed Hope Agenda. In 2025, we will commit to promoting adherence to ethical principles, shared values, and beliefs under the National Identity Project.

I will unveil the National Values Charter, already approved by the Federal Executive Council, in the first quarter of 2025. I will launch an ambitious national orientation campaign that fosters patriotism and love for our country and inspires citizens to rally together.

The Charter will promote mutual commitments between the government and citizens and foster trust and cooperation among our diverse population and between the government and the citizens.

As far-reaching and foundational as our reforms are, they can produce the desired outcomes only through shared common values and identities and unconditional love for our country.

The Youth Confab will begin in the first quarter of 2025, a testament to our commitment to youth inclusiveness and investment as nation-builders. The Ministry of Youth will soon announce the modalities for selecting the conference's representatives from our diverse, youthful population.

Dear Compatriots, I urge you to continue believing in yourselves and keeping faith in our blessed country.

Let me use this New Year's message to urge our governors and local council chairpersons to work closely with the central government to seize emerging opportunities in agriculture, livestock, and tax reforms and move our nation forward.

I commend governors who have embraced our Compressed Natural Gas initiative by launching CNG-propelled public transport. I also congratulate those who have adopted electric vehicles as part of our national energy mix and transition. The Federal Government will always offer necessary assistance to the states.

To all citizens, your sacrifices have not been in vain over the past 19 months. I assure you they will not be in vain even in the months ahead. Together, let us stay the course of nation-building.

The New Year will bring us closer to the bright future we all desire and the Nigeria of our dreams.

God bless you all, and may God bless our beloved country, Nigeria.

Happy New Year and a prosperous 2025 to you all!

Bola Ahmed Tinubu,
President of the Federal Republic of Nigeria
January 1, 2025

01/01/2025

Babban Pasto a Majami'ar ECWA da ke Wuse 2, Abuja Fadar Mulkin Najeriya, Pastor Azaki Nash ya taya 'yan Najeriya murnar shiga sabuwar shekara ta 2025, tare kira a baiwa gwamnatin Najeriya goyon baya domin cigaban kasa.

A gefe guda kuma, Pastor yayi kira ga gwamnatin Najeriya da ta rubanya kokarinta na bunkasa tattalin arziki cikin shekarar nan da aka shigo ta 2025

๐—ฆ๐—”๐— ๐—” ๐——๐—” ๐— ๐—”๐—ฆ๐—จ ๐—Ÿ๐—”๐—œ๐—™๐—จ๐—ž๐—” ๐Ÿฎ๐Ÿฐ๐Ÿฌ๐Ÿฌ ๐—ก๐—˜ ๐—ฆ๐—จ๐—ž๐—” ๐—™๐—”๐——๐—” ๐—ž๐—ข๐— ๐—”๐—ฅ โ€˜๐—ฌ๐—”๐—ก๐—ฆ๐—”๐—ก๐——๐—” ๐—” ๐—ž๐—”๐—ก๐—ข, ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฐ โ€ฆ๐—–๐—ฃ ๐—ฆ๐—”๐—Ÿ๐— ๐—”๐—ก ๐——๐—ข๐—š๐—ข Kwamishinan โ€˜yan sandan jihar Kano, ...
01/01/2025

๐—ฆ๐—”๐— ๐—” ๐——๐—” ๐— ๐—”๐—ฆ๐—จ ๐—Ÿ๐—”๐—œ๐—™๐—จ๐—ž๐—” ๐Ÿฎ๐Ÿฐ๐Ÿฌ๐Ÿฌ ๐—ก๐—˜ ๐—ฆ๐—จ๐—ž๐—” ๐—™๐—”๐——๐—” ๐—ž๐—ข๐— ๐—”๐—ฅ โ€˜๐—ฌ๐—”๐—ก๐—ฆ๐—”๐—ก๐——๐—” ๐—” ๐—ž๐—”๐—ก๐—ข, ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฐ โ€ฆ๐—–๐—ฃ ๐—ฆ๐—”๐—Ÿ๐— ๐—”๐—ก ๐——๐—ข๐—š๐—ข

Kwamishinan โ€˜yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya ce Rundunar ta sami nasarar k**a wadanda take zargi da aikata laifuka daban-daban su 2,425 daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 Disamba,2024.

Kwamishinan Dogo Garba na bayyana hakan ne a shelkwatar โ€˜yansanda da ke Bompai yayin da yake karin haske kan nasarorin da rundunar ta samu, inda ya ce sun kuma kwato muggan mak**ai, kwayoyi da kuma kayan sata k**ar shanu da awaki da sauransu.
Ya kara da cewa a farkon shekarar 2024, an yi fama da yunkurin โ€˜yan bindiga na shigowa jihar wanda suke da kananan hukumomi 17 akan iyakokin jahohin, Kaduna, Katsina, Jigawa da kuma Bauchi, baya ga barazanar fadan daba da kuma masu taโ€™ammali da miyagun kwayoyi a kananan hukumomin 8 na kwaryar birnin Kano.

Sai kananan hukumomi 19 wadanda basa cikin birni ko kan iyaka, da aka samu yawan sace-sace da fada tsakanin makiyaya da manoma.

Cikin nasarorin da rundunar ta samu sun hada da cafke wadanda ake zargi da zama โ€˜yan fashi da makami 189, masu garkuwa da mutane 34, barayin shanu 10, masu safarar bindigu 2, barayin motoci 22, dilolin kwaya 58, masu fasa kaurin 18, barayin Adaidaita sahu 46 da barayin babura 28 dama cafke masu buga takaddun bogi 4, โ€˜yan damfara 27 da kuma yan daba 1987.

Har ila yau ya ce rundunar ta tseratar da mutane 40 da aka yi safarar su da kuma kubutar da mutane 18 wadanda aka yi garkuwa da su , sai mutane 2 da aka sace, baya ga kwato bindiga kirar AK-47 guda 7, Beretta Pistol 1, Pump Action 4, Bindigar harbin tsintsaye 7, kirar gida 4 da kuma bindigar wasan yara 4.

Haka kuma an kwato harsasai 1,213, Adduna 57, Wukake 198, motoci 12, babura 44, adaidaita sahu 15, kudin jabu naira Bilyan 129 da Milyan 542 da dubu 823 na kudaden ketare da kuma na Nigeria, sai shanun sata 308, Katin cirar kudi (ATM Card) 65, wayoyin sata 415, zoben azurfa 67, baturan sola 34 da kuma allura 105.

A karshe rundunar ta godewa gwamnatin jihar Kano da sauran hukumomin tsaro da kungiyoyin alโ€™umma da kafafen yada labarai da wakilansu, a bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen wayar da kan jamaโ€™a musamman akan abin da ya shafi tsaro.

๐—ž๐—”๐—ก๐—ข ๐—ญ๐—” ๐—ง๐—” ๐—ž๐—”๐—ฆ๐—›๐—˜ ๐—•๐—œ๐—Ÿ๐—œ๐—ฌ๐—”๐—ก ๐—ก๐Ÿณ๐Ÿญ๐Ÿต.๐Ÿณ ๐—” ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐ŸฑGwamnan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu ...
01/01/2025

๐—ž๐—”๐—ก๐—ข ๐—ญ๐—” ๐—ง๐—” ๐—ž๐—”๐—ฆ๐—›๐—˜ ๐—•๐—œ๐—Ÿ๐—œ๐—ฌ๐—”๐—ก ๐—ก๐Ÿณ๐Ÿญ๐Ÿต.๐Ÿณ ๐—” ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฑ

Gwamnan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan kasafin kudi N719,755,417,663.00 kudaden da za a kasha a 2025.

Idan aka rarraba kudaden: harkokin yau da kullum za su lakume N262,670,660,562.68, wato kaso 36 cikin dari na adadin jumular kudaden yayin da manyan ayyuka za su lashe N262,670,660,562.68, wato kaso 64 cikin dari na jumullar kudaden.

A sakon da ya aika wa manema labarai mai magana da yawun shugaban majalisar dokokin jihar Kano Ismaโ€™il Falgore wato Kamaludeen Sani Shawai yace Falgore ya bayyana cewa mambobin majalisar dokokin jihar Kano sun zauna da shugabannin hukumomi na gwamnatin jihar dama jin raโ€™ayin jamaโ€™a kafin tattance bukatun da s**a bijiro da su aka shigar cikin kasafin.

โ€œYayin da muke gudanar da aikin da kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar mana, bukatar kara kudade ta bijiro ne bayan tattaunawarmu da bangaren hukumomi na gwamnatin jiha dama wadanda s**a zo yayin jin raโ€™ayin jamaโ€™a da wannan muka kafa hujja da amince da kara kudade N170,595,000,000.00.โ€

Wannan kasafi za a dauki nauyimnsa ne daga kudade da ake bawa jihohi da kudade daga harajin VAT da kudaden da ke shigarwa jihar daga haraji na IGR da sauran tallafi da ake samu daga gwamnatin tarayya.

Da yake jawabi yayin amincewa da kasafin Gwamnan Kano Yusuf yace wannan ci gaba ne a kokari da gwamnatinsa ke yi na ciyar da jihar gaba ta hanyar zuba jari a harkokin samar da ababen more rayuwa da yaki da talauci tsakanin alโ€™umma.

Wannan kasafi dai an bashi take na โ€œKasafin Fata samar da ci gaba bunkasar tattalin arziki.โ€yace yana da buri ne na tallafar alโ€™umma ta yadda za a samu bunkasa a jihar.

A cewar gwamnan kasafin zai fi mayar da hankali kan batun ilimi da lafiya da ayyukan gona ta yadda zaa samar da damarmaki ga dukkanin alโ€™ummar Kano.

โ€œBurin da muke da shi shine mu samar da jiha cike da kwanciyar hankali da ci gaba.โ€œ A cewar gwamnan, inda anan sai yayi godiya ga mambobin majalisa ganin yadda s**a yi aiki tukuru kan kasafin s**a kuma amince da shi a kan lokaci.

BARKA DA SABUWAR SHEKARA DAGA MURYAR NAJERIYA (VON)
01/01/2025

BARKA DA SABUWAR SHEKARA DAGA MURYAR NAJERIYA (VON)

Address

VON Corporate Headquarters Plot 1386 Oda Crescent, Off Aminu Kano Crescent, Wuse II
Abuja
PMB5089,WUSEPOSTOFFICEABUJA.

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sashen Hausa Muryar Najeriya, Abuja posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sashen Hausa Muryar Najeriya, Abuja:

Videos

Share