12/06/2023
Dr. IDRIS AHMED ƘOLOLUWAR ABIN ALFAHARIN BAKAR FATA A DUNIYA BAKI DAYA.
Rubutawa: Haruna Shu'aibu Danzomo .
Cikakken Sunan sa Shine Idris Ahmed, an Haife shi a Unguwar Kolere Dake Garin Mubi a Karamar Hukumar Mubi North Dake Jihar Adamawa a Nigeria.
Mahaifin sa Mallam Ahmadu Dan asalin Fulanin Nyinbbunga ne Dake Jihar Bauchi yayin da Mahaifiyar sa Hajiya Khadija ta Kasance Yar Fulanin Gaya a Jihar Kano.
Mahaifin sa Malamin Zaure ne Domin har yana da tsangaya a wancan lokacin Kafin Allah ya Karbi Rayuwar sa a Shekara ta 1969.
Dr. Idris Ahmed yayi Karatun Primary a Makarantar Mubi One Primary School Dake Mubi, Sannan Kuma yayi Government Science Secondary School Hong Duk a Jihar Adamawa inda Kuma bayan ya Rubuta Jarabawar WASC ya samu Kyakkyawan sak**ako Sai Kai tsaye ya wuce zuwa School of Basic Studies (SBS) ta Babbar Jami'ar Tarayya Dake Zaria wato Amadu Bello University Zaria ( A.B.U ZARIA ) Amma yana tsakiyar Wannan karatun Kuma Bai kammala ba Sai Yayan sa Engineer Ahmed ya tura shi zuwa England Domin yin Karatu a Shekara ta 1988.
Da ya iso England a shekaran 1988, ya yi karatun GCE Advanced Level a wata private makaranta, sunanta St Aldates College, a garin Oxford.
Bayan ya gama da Oxford sai ya sami shigewa Babbar Jami'ar Conventry University Dake England.
Dr. Idris Ahmed ya Karanta Cryptology, wato ilimin sarrafa sirrin na na'ura mai kwakwalwa. Ana amfani da wannan ilimin wajen bawa kafofin sadarwa da kuma manhaja tsaro. Har kazalika ana amfani da ilimin wajen bawa motocin zamani tsaro daga hackers.
Yayi Dogon Karatu har ya Kai Matsayin ya samu Digirin Digirgir Wato Doctorate Degree a turance wato (PhD) Wanda Abin Alfahari Shine Kuma Bakar Fata na Farko Daya fara samun Wannan Damar a Duniya Baki Daya.
A ƴanzu haka Kuma yana Cikin Manyan masana a Wannan fannin a Duniya Baki Daya haka tasa Kuma yana Cikin Manyan Ma'aikatan Babban Kamfanin Dake kera Motocin Alfarma na Zamani masu Aiki da Na'ura Mai Kwakwalwa na Duniya Dake Kasar Burtaniya.
Kafin Dr. Idris Ahmed yabar Nigeria zuwa England yayi sana'ar Sayar da Kayan Gini a Garin Mubi Kuma ya Dan taba Aiki da Wani Kamfanin Yayan sa, Engineer Ahmed, dake Victoria Island a Lagos.
Ba Karamin Aiki bane kasancewa a matsayin da Dr. Idris Ahmed yake a ƴanzu Domin yana Jagorantar kula da tsaron Manyan motoci na alfarma ne wadannan Manyan Shuwagabannin Duniya da Ƴan Kasuwa da Masu Arzuki da Duk Wani Wanda yake da fada aji ne yake Hawa a Duniya Fuskar Kare su shiga hatsarin kwacewa ko Aikata kowanne Irin Laifi daya Shafi Juya akalar su ta Hanyar Amfani da Na'ura Mai Kwakwalwa (Hacking).
Ni Nasan shine a Kafar Sadarwa ta zamana Abin da zai baka Mamaki duk Irin Wannan Matsayin nasa Bai Hana Shi lokacin da zai tsaya ya fuskanci matsalar Nigeria Kuma yayi Rubutu akan Hakan ba ya wallafa a Shafin sa musamman Abin Daya Shafi zalunci da Cin Hanci da rashawa to anan Nasan Dr Idris Ahmed har Kuma na fada bincike Akan Sa.
~Ya k**ata mu Samu Karin Dr Idris Ahmed~
Da dama mutane Basu fahimci Amfanin Wannan Ilmin ba musamman anan Nigeria Kamar dai lokacin da aka karatun Computer ne a Nigeria Saida aka barmu a a Baya Sosai saboda Muna Ganin cewa Ilmi ne Daya Shafi Turawa Saboda sune Suke Aiki da ita yau gashi Komai kake Karanta saika hada da Computer to jama'a mu kula da Kyau zuwa gaba wadancan Motocin Alfarma da suke kasashen Turai zuwa gaba sune zasu zo Nigeria Ballantana ma Yanxu haka Manyan mutane a Nigeria duk da su suke Amfani Don Haka Lalle yana da Kyau Nigeria ta fara koyar da Wannan Fannin a kowanne matakin Karatu. Sannan Matasan mu a waye a tari Wannan ci Gaban Akwai alfanu Sosai.
Yanxu Haka Dr yana da Iyali a ma'ana Mata a Nigeria da Germany da Kuma England.
Darasi a Rayuwar Dr.
Almajiri Dan Mallamai wadanda ake cewa suna kyamar Karatun Boko ya zama Shehun Boko Wanda duk Duniya take Kallon sa take amfanar Sa.
Maraya. Ne Amma ya mike da nemana na Kai duk da Dai yana da Masu Tallafin sa Amma Saida yayi Aiki Tukuru Don haka Muma Sai mun zage Dantse.
Mutum ne Mai taimakon na Kasa da shi musamman idan ya fahimci kana son Taimakon Kan Ka.
Allah ka Kara mana ire iren Dr Idris Ahmed.
Shawara ta Gare Shi.
Ina fatan Don Allah Dr ya rikar Samar da Ƴan Bidiyoyi Vedios Koda na mintuna 30 a mako Domin Wayar da Kan Al'ummar Nigeria mahimmancin Karatun Cryptography da Irin ci Gaban da ake samu a ƴanzu haka.
Muna fatan Allah ya Kare shi Kara masa lafiya da Nisan Kwana cike da Imani.