10/03/2024
HUƊUBAR MANZON ALLAH (S) A KAN WATAN RAMADAN
Daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
Shaikh Saduq (R) ya ruwaito da Isnadi daga Imam Ali Bin Musa Ridha (AS) daga iyayensa daga Amirul-Muminin Ali (Alaihi wa ala Auladihis salam), ya ce; Manzan Allah (S) ya yi mana huduba wata rana ya ce;
“Ya ku mutane, ga watan Allah nan ya gabato muku da albarka da rahama da gafara. Wata ne wandaa wajen Allah (T) shi ya fi sauran watanni fifiko. Ranakunsa kuma sun fi sauran ranaku falala. Dararensa sun fi sauran darare falala. Sa’o’insa sun fi sauran sa’o’i falala. Shi wata ne wanda aka kira ku izuwa liyafar Allah Ta’ala……
Sharhi:
Wato k**ar liyafa shi ne, Allah Ta’ala ya kira ku ku zo ku ci abinci, ya shirya muku, ya jera abinci iri-iri. An kira ku liyafa, k**ar ku baqin Allah ne a cikin watan Ramadan. An kira ku ya zuwa ga liyafar Allah. To, kuma an sa ku cikin ma’abota karamar Allah. Wato ma’anar wannan kiranku ya zuwa liyafar Allah, shi ne an sa muku wani lokaci da aka daukaka darajojinku. Aka ba ku damar samun lada mai yawa.Wato kenan k**ar mutum ya je liyafa ya ci abinci, ya zazzabi abinci iri-iri masu dadi. Wannan kuma shi ne ainihin nau’o’in ibadodi da zikirori da sauransu, wanda za a dinga nunnunka ladanku.
“Numfarfashinku a cikin Ramadan tasbihi ne…..
Sharhi:
Wato lokacin da ka numfasa sai a rubuta maka k**ar ka ce ‘Subahanallah’. Ka ga ko numfashin (da ka ke) yi ma idan kana barci ba ka sani ba (ana rubuta maka lada ne). Numfarfashinku tasbihi ne.
“Baccinku a cikin watannan ibada ne. Aikinku karbabbe ne. Addu’arku abin amsawa ne. Saboda haka ku roqi Allah Ubangijinku da niyyoyi na gaskiya da kuma zukata tsarkaka. Ku roqe shi ya ba ku ‘Muwafaqa’ da azuminsa (azumin watan kenan), da farlanta Alqur’aninsa (littafinsa). Domin duk shaqiyyi shi ne wanda aka haramta ma gafarar Allah a wannan wata mai girma…..
“Kuma a yayin yunwarku da qishinku a cikin watan nan, ku tuna da yunwa da qishin ranar Alqiyama. Kuma ku yi sadaka ga faqiranku da miskinanku. Kuma ku girmama tsofaffinku, ku ji tausayin yaranku, ku sada zumuncinku, ku kiyaye harsunanku, ku runtse idanunku daga abin da bai halatta ku gani ba, da kuma abin da bai halatta ku ji ba….
Sharhi:
Wato ku runtse idanunku daga abin da ganin ku bai k**ata ya je gare shi ba, kuma ku kiyaye kunnuwanku daga abin da bai hallatta ku saurara da jin ku ba.
“Kuma ku tausayawa marayu na mutane, (hakan zai sa) Allah ya tausaya mana. Ku tuba ya zuwa ga Allah daga zunubbanku. Kuma ku daga hannuwanku da addu’o’i a lokutan sallolinku, domin (lokutan salloli) sune sa’o’in da s**a fi falala, Allah (T) zai dube ku da Rahama….
Sharhi:
Allah yana duba ya zuwa ga bayinsa da Rahama kuma yana amsa musu in s**a kira shi (wato in s**a yi Munajati da shi), kuma yana amsa roqonsu in sun roqe shi.
“Ya ku mutane, rayukanku fa, jinginannu ne ya zuwa ayyukanku, saboda haka ku kame rayukanku da yin Istigfari. …..
Sharhi:
Wato an jingina rayukanku ga ayyukanku, k**ar abin da muke ce ma; jingina. Jingina shi ne; ainihin ka je ka ba da wani abu sai ka biya wani abin da yake kanka ka karba. To, ranku k**ar an ajiye ana jiran sai ka yi wani abu, ka ƙwato ran naka.
“Bayayyakin ku kuma ɗauke suke da nauyayyaki, ku sauqaqe nauyin da ke wuyayenku (na zunubai kenan) da tsawaita Sujjadodi. Ku sani cewa; Allah Ta’ala ya rantse da izzarsa, cewa; ba zai azabta masu yin sallah da sujjada ba, kuma ba zai firgita su da wuta ba a ranar Alqiyama (Yauma Yaqumun-nasu li-Rabbil Aalamin)….
“Ya ku mutane, wanda ya ciyar da mai azumi (Mumini) a wannan wata, yana da lada (a wajen Allah) daidai da ‘yanta wuya da gafara na duk zunubansa da s**a wuce."
A ka ce; "Ya Rasulallah! Ai ba kowane mumini yake da damar ya iya ciyar da masu azumi ba!”
Sai Manzan Allah (S) ya ce; “Ku ji tsoron wuta ko da da rabin Dabino ne. Ku ji tsoron wuta (wato ku kiyaye kan ku daga wuta) ko da da kurɓin ruwa ne…..
Sharhi:
Wato abin da za ka bayar ba lalai ya zama ya yawaita ba kenan, duk komai da kake da shi, komin qanqantarsa, ko da rabin dabino, in kana da dabinuwa guda xaya, sai ka tsaga ka ba da rabi. Mai ya yi sauqin wannan? Haka ma aka ce ko da kurvin ruwa ne. Kurɓib ruwa da tsagin dabino ko da wannan ne, ku yi qoqarin tseratar da kanku daga wutar Allah Ta’ala (da shi). Domin Allah Ta’ala yana ba da lada ga wanda ya yi wannan aiki qanqani, in bai samu ikon fiye da shi ba.
Mutum ne yake da ruwan da zai iya sha zai yi k***a uku sai ya ba wani kurɓi daya. Ka ga ya ba da nawa kenan na abin da yake da shi? Sulusi. Kaga duk da yake kaɗan ne, amma ya kasa uku ya ba da kurvi ɗaya, don haka ya bada da yawa. Saboda haka yana da lada mai yawa. Ɗan abin da kake da shi shi ne aka ce ka bayar. Ba a ce sai kana da dukiya mai yawa za ka bayar ba. Abin da kake da shi ko ya qaranta, to dai ka bayar.
“Ya ku mutane, wanda ya kyautata halinsa (ɗabi’o’insa) a wannan watan, zai zama qetara gare shi akan siraɗi ranar da qafafuwa za su goggoce. Wanda ya sauqaqa ma wanda ya mallaka (wanda hannunsa ya mallaka), Allah zai sauqaqa masa hisabinsa…..
Sharhi:
Wannan yana nufin in mutum yana da bawa kenan, da watan Ramadan ya sauqaqe musu aiki (hidimomi). Na’am wani lokacin mutanenmu anan tunda yanzu ba bawa da ake siyowa a kasuwa, amma akwai hadimai, ko su ma mutane ne, za a sauqaqa musu ba sai a sa su wahala ba. Musamman su ma suna azumi ai, suna ji a jika. Yawwa! To, saboda haka wanda ya sauqaqa ma wanda damansa ta mallaka, to, Allah zai sauqaqe masa hisabinsa.
“Wanda ya kiyaye sharrinsa na bakinsa da harshensa da idanunsa da kunnuwansa da qafafunsa da hannuwansa (ga mutane) a wannan watan, (k**ar tsegunguma da gulma da tura masifofi ya zuwa ga mutane), to, shi kuma Allah zai kiyaye masa fushinsa ranar da zai gamu da shi….
“Wanda ya girmama maraya (ya kyautata ma maraya), Allah zai girmama shi ranar da zai gamu da shi. Wanda ya sada zumuncinsa, Allah zai sadar da shi da rahamarSa. Wanda kuma ya yanke zumuncinsa (a Ramadan), Allah zai yanke masa rahamarSa ranar da zai gamu da shi. Wanda ya yi ‘Taɗawwa’i’ na sallah (wato sallar nafila kenan), za a rubuta mishi kuvuta daga wuta. Wanda ya bada farali, yana da daidai da wanda ya bada farali 70 a wani wata ba a cikin Ramadan ba….
Sharhi:
Wato ba da farali a Ramadan yana daidai da ba da farali Saba’in a wani wata ba shi ba. Kuma nafila bara’a ne daga wuta.
“Wanda ya yawaita Salati gareni, Allah zai nauyaya mizaninsa ranar da mizanoni za su yi rauni. Wanda ya karanta aya ɗaya ta Alqur’ani zai zama ladarsa k**ar wanda ya yi sauqar Alqur’ani ne gaba ɗaya in ba a cikin wannan watan ba.
“Ya ku mutane, qofofin Aljanna a wannan wata (na Ramadan) buɗaɗɗu ne. Ku roqi Ubangijinku (kar ya rufe muku qofofinSa na Aljanna ɗin). Kuma qofofin wuta (gidajen wuta kenan) rufaffu ne, ku roqi Ubangijinku kar ya buɗe muku su. Shaiɗanu kuma za a ɗaɗɗaure su, ku roqi Ubangijinku ka da ya sallaɗa su a kan ku”.
CIKON HUƊUBAR TA MANZON ALLAH (S)
Huɗubar na da tsawo, sai dai iyaka nan ma’abocin littafin Mafatihul-Jinan ya kawo, bai ci-gaba har qarshenta ba. Idan muka koma cikin littafin Biharul-Anwar, za mu ga cigaban (wasu sassa) na huɗubar, k**ar haka:-
Shaikh Saduq Rahimahullah ya ruwaito cewa, Annabi (S) ya kasance idan Ramadan ya shiga, yakan ‘yantar da ribatacce, ya kuma riqa bada (kyauta da sadaka ga) duk mai bara (mai tambaya). Masu nema ‘Fisabilillahi’ na abin da za su ci yau da kullum.
Har wala yau Shaikh Abbasil Qummi (R) ya kawo waɗansu bayanai a taƙaice na abin da ke cikin ruwayoyi daban-daban. Ya ce; “Watan Ramadan, shi ne; watan Allah Ubangijin talikai, shi ne kuma mafificin watanni. Watan da ake buɗe qofofin sama (wato ma’anar buɗe qofofin sama, addu’o’i na hawa, ibadodi na hawa nan da nan. Da ka yi addu’a za a kai sama kenan), ake kuma buɗe qofofin Aljanna. Ake buɗe qofofin Rahama (wato ma’ana ana saukar da rahama kenan), kuma ana rufe qofofin Jahannama.
Ma’aiki (S) ya ce; “A cikin wannan wata akwai wani dare wanda ibada a wannan daren ya fi yin ibada a wata dubu (wanda babu wannan daren kenan).
Sharhi:
In ka jera watanni dubun da babu ‘LAILATUL QADR’, to, ibadar ‘LAILATUL QADR’ ya fi yin ibada a wata dubun.
“Saboda haka ka faɗaka a cikin wannan da kanka, kuma ka buɗe idanu (wato buɗe zuciya kenan), ka duba ka ga yaya kake sarrafa darenka da ranarka da yininka a cikin Ramadan? Kuma ya za ka kiyaye gaɓuɓɓanka daga savon Ubangijinka. To, kuma a kul ɗinka kar ka zamo a cikin dararen ka ka zama kana cikin masu bacci, (wato ma’ana ka kwana kana bacci ba kai sallar (dare) ba kenan). Ko kuma a yininka ka zama gafalalle daga zikirin Ubangijinka.”
Ya zo a cikin hadisi, cewa; Allah Mai girma da ɗaukaka a ƙarshen kowane yini na Ramadana a yayin buɗa baki, yana ‘yanta wuya dubu sau dubu (1000 x 1000) daga wuta. Idan kuma a daren Juma’a ne da yininta na cikin Ramadan, a kowace sa'a Allah yana ‘yanta wuya 1000 x 1000 na wanda ya zama wajibi su shiga wuta. A daren qarshe na Ramadan kuma da yinin qarshe na Ramadan sai a ‘yanta adadin abin da duk aka ‘yanta a watan baki ɗaya.”
Sharhi:
Ma’anar 1000 x 1000, miliyan kenan. Duk qarshen yini wajen buɗa baki Allah yana ‘yanta mutum 1000 x 1000 wanda s**a cancanci shiga wuta. Idan kuma a dare da yinin Juma’a ne, kowace sa’a (ake ‘yanta mutum dubu sau dubun). Ka ga daga ranar Asabar har zuwa ranar Alhamis, duk ƙarshen yini za a ‘yanta wuya 1000 x 1000. Idan daren Juma’a ne da kuma yinin Juma’a, kowacce sa’a 1000 x 1000. Ka ga sa’a 24, 1000 x 1000 sau 24 kenan, na duk wanda s**a cancanci wuta. Sannan aka ce a daren qarshe na Ramadan da yinin qarshe sai Allah ya ‘yanta adadin abin da duk aka ‘yanta a baki ɗayan watan.
Ka ga idan ka tattara watan Ramadan kenan, ka ciccire Juma’a, sa’o’i ishirin da huɗu-huɗu na Juma’a, in an samu Juma’a 4 a cikin Ramadan, in ka cire su, kowanne yini, sauran za ka samu kwana qila 26, ko 25. Za ka samu k**ar kwana 25 ko 26, to, za a ‘yantar da 1000 x 1000 kowane yini. Sannan Juma’a kuma, huɗun nan 1000 x 1000 sau 24 sau 4. Sannan kuma yinin qarshen, shi kuma sai a nunnunka duk abin da aka ‘yanta, shi kuma sai a ‘yanta a yinin qarshe da daren qarshe da yinin qarshe na Ramadan.
Saboda haka; a kul ɗinka ya kai ɗan uwa mai girman daraja, kar ka yarda wannan watan Ramadan ya wuce alhali kana da zunubi cikin zunubai. Kuma kar ka yadda ka zama cikin masu zunubbai wanda za a haramta ma Istigfari da addu’a!
An samo daga Imam Sadiq (AS) ya ce; “Wanda duk ba a gafarta masa a watan Ramadan ba, to, ba za a gafarta masa a wani wata ba har shekara ta dawo, sai dai in ya halarci Arfa.”
To, kuma ka kare kanka daga abin da Allah ya haramta. Ka kiyayi kanka kar kai buɗa baki da haram. Ma’anar buɗa baki da haram ba yana nufin abin da aka haramta cinsa ba ne. A’a, abin da aka halasta cinsa amma kar ka samo shi ta hanyar haram. Yawwa!
Wasallallahu Ala Muhammadin Wa’aalihiɗ-Ɗaahirin.
Wannan shi ne qarshen Huɗubar Manzon Allah (S) wanda Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karanto ya yi sharhi a ranar Alhamis 28 ga watan Sha’aban 1435 (26/6/2014) a Husainiyya Baqiyyatullah Zariya.
— Cibiyar Wallafa