04/12/2024
Tatsuniya ta 38: Labarin Makauniya Da Danta
Gatanan gatanan ku
A wani ƙauye da ke yamma da Dajin Kurege, akwai wani manomi da matarsa makauniya. Suna zaune cikin ƙanƙanta, sai Allah ya ba su ɗa mai suna Zama. Uwarsa ta sha wahala wajen renonsa. Kullum sai ta je yin bara kafin ta ciyar da kanta da ɗanta. Mijinta bai bar musu dukiya ba sai shanu biyu kawai da Zama ya gada. Ita kuma mace mai tsinkaye da rikon amana, ta kai shanun nan wani garke a rugar wasu makiyaya da ke kusa da ƙauyensu. Ta yi haka ne da nufin idan yaron ya girma, kuma shanun sun yadu, za ta nuna masa abin da ubansa ya bar masa. Duk abin da danta yake so takan je ta samo masa.
Sannu a hankali, yaro ya girma ya isa aure. Wata rana bayan sun ci abincin dare, sai uwar ta kira shi ta ce: "To, Zama, da ma ina jira ne idan ka yi hankali sosai in danka maka abin da ka gada daga mahaifinka. Amma na kai su garke ne, a rugar wasu makiyaya."
Da ya ji lafazin mahaifiyarsa, sai ya tambaye ta: "Mene ne? Wane irin abu ne?"
Ta ce: "Shanu biyu ne ya bar maka, amma ban sani ba ko yanzu sun karu?" Sai ta k**a hannunsa ta ce: "Mu je inda aka kai shanun, mu jiyo labari." Ta yi masa kwatancen hanyar da za su bi; s**a k**a hanya har s**a kai.
Mai garke ya yi musu maraba s**a gaisa k**ar yadda ya k**ata, sai makauniya ta tuna masa shanun da ta kawo masa kiwo tun shekarun baya. Sai mai garke ya ce: "Haka aka yi kuwa. Ai yanzu shanu sun hayayyafa, har ma sun kai ashirin."
Da ta ji haka sai ta yi masa godiya, ta ce da shi: "To, ga magajinsu ya kawo karfi, bukatu sun taso, shi ya sa muka zo mu kora su."
Sai mai garke ya ware musu shanunsu; s**a k**a hanyar gida, Zama yana kora su har s**a je gida.
Bayan sun dan huta da kwana biyu, sai uwar ta ce da Zama: "Ya k**ata yanzu kam ka yi aure domin ina so in sami jikan da zan rinka wasa da shi."
Sai ya ce da ita: "To, amma fa ni ba zan yi aure a ƙauyen nan ba sai dai daga birni."
A kwana a tashi, wata rana sai Zama ya shiga birni, ya je kasuwa, sai ya tarar an sa wata kyakkyawar yarinya a gaba, makada na cashewa ana yi mata kirari, da wake-wake. Sai ya tambayi wani dan kallo da ke wurin: "Me ya sa aka kewaye wannan yarinya mai kyau k**ar aljana, ana yi mata kida da waka?"
Sai ya ce da shi: "Saboda kyaunta ne uwarta ta ce duk mai son ta, sai ya ba ta duk dukiyar da ya mallaka kafin ya aure ta. Duk masu dukiyar da ke garin nan kuma sun kasa."
Da ya ji haka sai ya yi tsaki, ya ce: "Ni zan aure ta." Sai ya matsa kusa, ya sa aka yi sanarwa, ya ce: "A gaya wa uwar yarinyar cewa ni zan aure ta, kuma zan ba da duk dukiyar da na mallaka."
Wani daga cikin danginta ya ce: “To me ka mallaka?"
Zama ya ce: "Ina da rikakkun shanu ashirin."
Sai dangin ya ce: "To, ka je ka kawo su za a ba ka ita."
Da Zama ya ji haka, sai kurum a cikin doki ya koma gida ya gaya wa mahaifiyarsa cewa ya sami wadda zai aura.
Uwar ta ce: "Wane sharadi iyayenta s**a sa maka?"
Sai ya ce: "Sun ce sai na ba su duk dukiyata kafin su ba ni ita."
Uwar daga farko ta yi murna, amma da ta yi tunani kadan sai ta ce: "Kai ɗan nan, wannan fa shi ne iyakar abin da ka mallaka, babu hikima a ce ka ba su ita gaba ɗaya."
Wannan magana dai ba ta shigi yaron ba. Sai kawai ya ce shi fa sai ya auri wannan yarinyar. Sai uwar ta ce: "Shi ke nan, yi abin da kake so."
Ya kora shanu, ya kai su gidan iyayen yarinyar da zai aura. S**a karba s**a kuma ba shi yarinyar, aka ɗaura aure ya dauki matarsa ya kai ta gidansu, ya je kuma ya sanar da mahaifiyarsa. Ita kuma ta ce da shi: "Ai ya k**ata ka kai ni in yi mata barka da zuwa."
Bai yi wata-wata ba ko sai ya k**a sandarta ya kai ta har dakin amaryar. Amma da ta ga mahaifiyar Zama makauniya ce, sai ta ki yi mata magana, ta nuna cewa ai ba ta yi wa makafi magana. Uwar kuma ba ta nuna damuwa a kan halayyar surukarta ba, saboda hakurin da Allah ya ba ta.
Ana nan, bayan 'yan kwanaki sai amarya ta ce da Zama: "Ni fa na gaji, ba zan iya ci gaba da girki a gidan nan ba."
Sai ya ce: "To, yaya k**e so a yi?"
Ta ce da shi: "Mai dafa abinci za ka nemo mini."
Da ya ga matarsa ta kafe a kan haka sai ya gaya wa mahaifiyarsa. Ita kuma ta ce da shi: "Ba komai, ni zan ci gaba da dafawa; ai dama tun kafin ta zo, ni nake dafawa". Haka ta ci gaba da yi musu girki, surukarta kuwa ta ci gaba da zaman ƙwambo.
Wata rana matar Zama ta tambayi mijin inda ya samo shanun da ya kai gidansu ya aure ta. Sai ya kwashe labarin yadda ya ci gadon mahaifinsa, ya gaya mata. Da ta ji haka sai ta ce: "Ai mahaifiyarka ta cuce ka domin ta boye sauran shanun. Ka je ka bincike ta da kyau, za ta gaya maka inda sauran suke."
Nan da nan ya tashi ya je ya sami mahaifiyarsa, ya fara yi mata rashin ladabi da fada, wai sai ta fito masa da sauran shanunsa. Ita kuma ta ce da shi: "Haba ɗana, ban boye maka komai ba."
Haka dai Zama ya yi ta yi wa mahaifiyarsa rashin ladabi har tsawon wasu 'yan kwanaki.
Da matar Zama ta ga bai yi wa mahaifiyarsa wulakanci k**ar yadda take so ba, sai ta ce da shi: "Ni fa zan koma gidanmu; domin na gaji da zama da makauniya a gidan nan.