BIN IDRIS

BIN IDRIS JANNAH STRIVER ❤

29/11/2024
16/11/2024

SALLAR JANA’IZAR SARKI NAJASHIY:

Daga Sheikh Dr Ibrahim JaLo Jalingo

1. Sallar da Manzon Allah صلى الله عليه وءاله وسلم tare da Sahabbansa s**a yi wa Najashiy tana tabbatar da halaccin yi wa duk musulmin da ya mutu a wata kasa sallar janaza, sawaa’un an yi masa sallar janaza a can inda ya mutun ko kuwa a’a ba a yi masa ba. Wanda kuma duk ya yi ikirarin cewa abin da ya sa Manzon Allah da Sahabbansa s**a yi wa Najashiy salla shi ne saboda babu wanda ya yi masa sallar ne a can Habashan, to wannan dole ne a ce ya kawo wa Duniya tabbataccen dalili a kan hakan; ko dai daga Alkur’ani ko kuwa daga ingantaccen Hadithi. Kuma har abada babu wanda ya isa ya kawo irin wannan dalilin.

2. Amma abin da Malaman Mazhabar Hanbaliyyah suke ce cikin المغني 2/383 da الشرح الكبير 2/355 da المبدع 2/260 da كشاف القناع 2/123 shi ne: Najashiy Sarkin Habasha ne da ya musulunta kuma Musuluncinsa ya fita fili, ke nan zai yi wuya matuka a ce babu mutum daya da ya bi shi wanda kuma zai yi masa salla bayan mutuwarsa”.

3. Hafiz Ibnu Hajar ya ce a cikin Fathul Baariy 3/188: ((Ban ga inda aka ce babu ko da mutum daya da ya yi masa salla a Habasha ba.

4. Sai dai kuma shi Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce game da shi Najashiy a cikin Maj’muu’ul Fataawaa 19/217, da kuma cikin Minhaajussunnah 5/112 : ((Mutane kadan ne s**a karbi Musulunci tare da shi; wannan shi ne ma ya sa a lokacin da ya mutu babu wanda ya yi masa salla)).

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah na tarayyar Naijeriya, ...
14/11/2024

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!

Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah na tarayyar Naijeriya, Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, na miƙa saƙon ta’aziyya a madadin ƙungiyar, na rasuwar ɗaya daga cikin dattawan Malaman ƙungiyar, babban limamin Masallacin Juma'a na Gwallaga, a garin Bauchi, Sheikh Imam Ibrahim Idris, wanda ya rasu a ƙasar Masar (Egypt) bayan fama da jinya.

Sheikh Bala Lau, yace Marigayin ya ƙare rayuwarsa gaba ɗaya wajen hidimtawa addinin Allah, ta bangaren wa’azi da ilimantarwa, muna masa kyakkyawan zato na alheri, da fatan Allah ya sanya shi a jannatul firdausi, ya gafarta masa kura-kurensa, ya albarkaci zuri’arsa.

A alhamis ɗinnan 14/11/2024 bayan sallar azahar Za’a gabatar masa da salatul Ga’ib a cikin masallacin JIBWIS na gwallaga dake garin Bauchi a jahar Bauchin Naijeriya insha Allah.

Allah Madaukakin Sarki Ya jikansa da rahama Ya gafarta masa Ya sa Aljannahce makokarsa, in tamu tazo Allah Yasa mu cika da imani.

JIBWIS NIGERIA

Alhji Abdullahi Abdulmaliq Digi National Dept Director Admin and Finance and alhji abdullahi sa'id oshoga karshi divisio...
11/11/2024

Alhji Abdullahi Abdulmaliq Digi
National Dept Director Admin and Finance and alhji abdullahi sa'id oshoga karshi divisional leader 👏
Allah ya karawa rayuwa albarka. Ameen

JJibwis NigeriaJJibwis Gwagwa Fct-AbujaJJibwis GombeMMusa H. IsahJJibwis Abuja
Div. PRO Karshi

11/11/2024

Waye kagane Cikin Hoton Nan

25/10/2024

Waazi akan amana

21/10/2024

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when BIN IDRIS posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to BIN IDRIS:

Videos

Share