Hausa News

Hausa News A farkon shekarar 2024 aka samar da kafar yada labarai ta - Hausa News

Kotu ta samu Mathias tare da wasu abokan wasan yarinta na Paul Pogba kan neman dala miliyan $14 daga wajen Pogba a ƙarsh...
20/12/2024

Kotu ta samu Mathias tare da wasu abokan wasan yarinta na Paul Pogba kan neman dala miliyan $14 daga wajen Pogba a ƙarshen 2022.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya gudanar da Umrah a yau Alhamis a ƙasa mai tsarki. Shettima ya samu kyak...
19/12/2024

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya gudanar da Umrah a yau Alhamis a ƙasa mai tsarki.

Shettima ya samu kyakkyawar tarba daga manyan jami'an gwamnatin Saudiyya kafin daga bisani ya wuce Makkah domin yin ɗawafi.

Ya kuma yi wa Najeriya addu'a a lokacin Umrah ɗin.

Yara da dama ne s**a rasa rayukansu a yankin kudu maso yammacin Nijeriya a ranar Laraba a wani turmutsitsi da aka yi a y...
18/12/2024

Yara da dama ne s**a rasa rayukansu a yankin kudu maso yammacin Nijeriya a ranar Laraba a wani turmutsitsi da aka yi a yayin bikin baje kolin hutu da wata makaranta ta shirya, in ji gwamnan yankin.

Lamarin ya faru ne a makarantar Islamic High School Basorun da ke jihar Oyo, kuma an tura jami’an tsaro domin aikin ceto da dakatar da samun ƙarin mace-mace, inji gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde.

"Muna jajantawa iyayen da farin cikinsu ya rikiɗe zuwa bakin ciki ba zato ba tsammani," in ji gwamnan.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya shaida hakan a lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya gabata...
18/12/2024

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya shaida hakan a lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2025.

Ya ce raguwar da aka samu a garkuwa da mutane da kashe ƴanbindiga 11,000 sun ƙara bayyana irin ƙoƙari da ƙwazon gwamnatin Tinubu.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kashi daya bisa uku na mutanen da girgizar kasar mai ka...
18/12/2024

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kashi daya bisa uku na mutanen da girgizar kasar mai karfin maki 7.3 ta shafa.

Masu aikin ceto a Vanuatu na fafatawa don gano wadanda s**a tsira daga wata mummunar girgizar kasa da ta kashe akalla mutane 14 a kasar tsib...

Kocin na Real Madid, Carlo Ancelotti ya yi zarra ne bayan doke Pep Guardiola na Man City, da Xabi Alonso na Bayer Leverk...
17/12/2024

Kocin na Real Madid, Carlo Ancelotti ya yi zarra ne bayan doke Pep Guardiola na Man City, da Xabi Alonso na Bayer Leverkusen, da Lionel Scaloni na Argentina da kuma Luis de la Fuente na Sifaniya.

Kemi Badenoch ta yi maganganu da dama kan Najeriya tun bayan da ta zama shugabar jam'iyyar Conservatives mai hamayya a B...
17/12/2024

Kemi Badenoch ta yi maganganu da dama kan Najeriya tun bayan da ta zama shugabar jam'iyyar Conservatives mai hamayya a Birtaniya, waɗanda ba su yi wa ƴan Najeriya da dama daɗi ba.

Kemi Badenoch ta yi maganganu da dama kan Najeriya tun bayan da ta zama shugaban jam'iyyar Conservatives a Birtaniya. Ƴan Najeriya da dama n...

Vinicius Jr ya yi zarra ne tsakanin ƴan wasa 10 da s**a haɗa da Rodri da Bellingham da Messi.Vinicius ya lashe kofin Cha...
17/12/2024

Vinicius Jr ya yi zarra ne tsakanin ƴan wasa 10 da s**a haɗa da Rodri da Bellingham da Messi.

Vinicius ya lashe kofin Champions League, da La Liga, da UEFA Super Cup, da Spanish Super Cup duk a sekarar 2024. Hausa News

Tauraron 'dan wasan kungiyar Real Madrid Vinicious Jnr ya lashe kyautar gwarzon 'dan wasan shekarar 2024 wanda hukumar F...
17/12/2024

Tauraron 'dan wasan kungiyar Real Madrid Vinicious Jnr ya lashe kyautar gwarzon 'dan wasan shekarar 2024 wanda hukumar FIFA ke bayarwa. Wannan ya kawo karshen cece kucen da aka dade anayi a harkar kwallon kafa lokacin da aka zabi Rodri na Manchester City a matsayin gwarzon shekarar da ya lashe Ballon D'or. 'Dan wasan mai shekaru 24 ya bugawa kungiyarsa wasanni 39 a wannan shekarar ya kuma ci kwallaye 24 domin taimaka mata lashe kofuna 2 na La Liga da kofin zakarun Turai. Vinicius ya taka gagarumar rawa wajen tarin nasarorin da Real Madrid ta samu a wannan shekarar. Wannan ta sa kungiyarsa ta Real Madrid ta kauracewa bikin Ballon D'or lokacin da ta samu labarin cewar ba shi za'a bai wa lambar ba.

A ci gaba da matakan da kasashen duniya ke dauka na kulla alaka da sabbin shugabannin Syria da s**a kawar da Bashar al A...
17/12/2024

A ci gaba da matakan da kasashen duniya ke dauka na kulla alaka da sabbin shugabannin Syria da s**a kawar da Bashar al Assad daga karagar mulki, shugabar kungiyar Turai Ursula von der Leyen ta ziyarci Turkiya inda ta gana da shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda ya taka rawa wajen goyawa sabbin shugabannin na Syria baya. Shugabannin biyu sun bayyana shirin aiki tare da kuma taimakawa Turkiya wajen ganin ta cimma burinta na shiga kungiyar EU.

Tsohon shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, wanda ke murnar zagayowar ranar haihuwarsa a yau Talata, ya mulki ƙasar sau ...
17/12/2024

Tsohon shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, wanda ke murnar zagayowar ranar haihuwarsa a yau Talata, ya mulki ƙasar sau biyu a matsayin soja da kuma farar hula.

A ranar Litinin ne zaɓaɓɓen shugaban Ghana, John Mahama ya kai wa shugaban Najeriya, Bola Tinubu ziyara a fadarsa da ke ...
17/12/2024

A ranar Litinin ne zaɓaɓɓen shugaban Ghana, John Mahama ya kai wa shugaban Najeriya, Bola Tinubu ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A baya-bayan nan ne hukumar zaɓen Ghana ta tabbatar da Mahama a matsayin shugaba mai jiran gado bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar.

Address

New Side Road
Abuja
900107

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa News:

Videos

Share