29/05/2024
WASU DAGA AIYUKAN MAI GIRMA GWAMNA ENGR. ABBA KABIR YUSUF A SHEKARA DAYA
BANGAREN ILIMI
1. Mayar da jarrabawar WAEC, NECO da NABTEB kyauta ga yan makarantun sakandare.
2. Zabtare kudin makarantun gaba da sakandare da kaso 50 cikin 100
3. Kai dalibai masu hazaka 1001 kasashen waje don digiri na biyu
4. Biyawa daliban wasu daga jami'o'in gwamnatin tarayya kamar BUK, FUD, da ABU kudin makaranta
5. Fara gyaran makarantun firamare da sakandare da s**a lalace a fadin jihar Kano
6. Dawo da makarantu 26 da tsohuwar gwamnati ta rufe.
7. Hadin gwiwa da Bankin Duniya don ci gaban ilimin fasaha da na sana'a (Technical and Vocational)
8. Kammala gyaran makarantar Fasahar Sadarwa da ke Kura
9. Samar da tallafin karatu ga daliban gaba da sakandare na jihar Kano
10. Raba fom din jarrabawar JAMB ga dalibai 6,500 yan jihar Kano.
11. Yarda da biyan kudi miliyan 75 domin samar da sababbin kwasa-kwasai (accreditation) a makarantun Polythechnic.
12. Dawo da kwamitin CRC a fadin jihar Kano
MANYAN AIYUKA
13. Aikin rufe babbar kwata daga Jakara zuwa Kwarin Gogau (Wuju-Wuju)
14. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a Dawakin Kudu
15. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a Gwarzo
16. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a Bebeji
17. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a Albasu
18. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a t**in Rano zuwa Rurum
19. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a Kabo
20. Aikin t**in 5 kilomita a Gezawa
21. Gyaran manyan kwalbatoci biyu da s**a hade Rano da Rurum
22. Gyarawa da canja karafan raba t**in Katsina
23. Gyaran gadojin tsallaka t**i a kusa da makarantun BUK, Sa'adatu Rimi, Legal, da sauransu.
24. Kammala gadojin tsallaka t**i na karfe a Kurna Babban Layi kusa da masallacin Kandahar.
25. Kammala gadar siminti a t**in Sheikh Ja'afar, Kwanar Dawaki, Rumfa Kwaleji, da kuma Titin Gwarzo.
26. Gyaran t**in Kuntau-Dorayi Babba.
27. Kiyayewa daga zaizayar kasa a gadar Garanga dake Bunkure.
28. Yin kwatoci a unguwar Indabawa da ke Karamar Hukumar Birni.
29. Kammala gyare-gyare a biranen Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo
30. Gyaran masallacin Idi.
31. Yin manyan kwalbatoci a Rafin Gora da Rafin Zur da ke Karamar Hukumar Rano
32. Kananun gyararraki a duka titunan jihar Kano
33. Bayar da kwantaragin biliyan uku da miliyan dari shida domin fadada t**in Zaria
34. Fara gyaran makarantun Technical a fadin jihar Kano
35. Fara yin gadar kasa a t**in Dan Agundi
36. Fara yin t**in sama a t**in Tal'udu.
37. Fara saka fitulan solar a fadin titunan jihar Kano
38. Gyaran makarantar Bagauda
39. Gyaran sakatariyar Audu Bako
40. Aikin t**in Hotoro zuwa Unguwa Uku
41. Fara gyaran duka makarantun koyon sana'a guda 22 a jihar Kano (Vocational Schools).
42. Gyaran gadar Kasa ta Muhammadu Buhari (Kabuga da Kofar Ruwa)
43. Ginin ofisoshi da masallacin mata da dakin taro a hukumar Hisbah.
44. Gyaran hukumar shari'a ta jihar Kano (Law Reform Commission)
45. Ginin gidaje guda takwas da gyaran katangar gidan gwamnatin Kano
46. Ginin bangaren buge-buge na zamani a hukumar ɗab'i ta jihar Kano
47. Sabunta makarantar kiwon dabbobi ta Bagauda.
48. Gyaran t**in Bayero-Soli da kuma samar da hanyar shiga a kusa da rukunin gidajen Ado Bayero Mall.
49. Ginin kwalbatin da ta rushe a hanyar Takai-Fajewa - Kayarda - Birnin Bako a karamar hukumar Takai.
BANGAREN LAFIYA
49. Kwacewa da gyaran asibitin yara na Hasiya Bayero
50. Bawa yara sama da 200,000 magani kyauta a asibitin Hasiya Bayero
51. Sabunta asibitin Sir Sanusi General Hospital
52. Sabunta asibitin Nuhu Bamalli.
53. Sabunta asibitin BELA
54. Samar da tsarin haihuwa kyauta
55. Yawon duba marasa lafiya a kauyukan jihar Kano
56. Kaddamar da tsarin "Abba Care" don kula da masu cutar sikila a fadin jihar Kano.
57. Gyara da sake ginin asibitin Murtala Muhammad
58. Siyan motocin ambulance don amfanin kananan hukumomi
59. Diban ma'aikatan lafiya da likitoci guda 106 a fadin jiha.
60. Daukan manyan likitoci "consultants" don su taimakawa asibitoci wajen samar da lasisin bude wasu ɓangarori kamar ENT, family medicine, gynecology da sauransu.
61. Samar da tsarin gwajin masu niyyar aure don kiyaye lafiyarsu
62. Hadin guiwa da Global Health Partners don zuwa dollar million hamsin cikin shekara uku a harkar lafiyar jihar Kano
63. Hadin gwiwa da gidauniyar Bill and Melinda Gates domin tallafawa harkar lafiya a jihar Kano
64. Biya don saka kayan ICU na zamani a asibitin Murtala Muhammad
65. Samar da motocin aiki ga bangarorin lafiya guda uku na jihar Kano
BANGAREN JIN KAI
66. Rarraba hatsi kyauta ga masu karamin karfi, taki da kayan aikin noma ga manoma a jihar don rage tasirin cire tallafin man fetur.
67. Fara kashin farko na na Auren Zaurawa
68. Raba shinkafa da masara 457,000 kilogiram 10 a matayin tallafi ga unguwanni 484 da ke jihar.
69. Shirin ba da tallafi na wata-wata ga mata na basu jarin N50,000 da yanzu ya samarwa mutane 5,200 a fadin jiha.
70. Kashi na 2, na 3 da na 4 na rabon kayan jin kai (palliative) a fadin jihar
71. Rarraba kayan amfanin gona irin su shinkafa da irin masara da akuya da injinan fanfo ruwa ga mata kusan 1000 a jihar.
AIKIN GWAMNATI
72. Biyan duk wasu basuss**an kudaden fansho na wadanda s**a yi ritaya daga aikin gwamnati na jihar Kano.
73. Dakatar da cirar da ba dole ba daga albashin ma'aikatan jihar da wadanda s**a yi ritaya.
74. Biyan kashi na biyu na bashi ga ’yan fansho da gwamnatin da ta shude ta hana biyansu na tsawon shekaru. An ware biliyan biyar don hakan.
75. Buga sakamakon taron majalisar zartarwa na mako-mako a jaridu da shafukan sada-zumunta
76. Horowa, sake horarwa, da haɓaka ingantaccen yanayin aiki don haɓaka yawan aiki da haɓaka ingancin sabis.
77. Samar da majalissar biya da bibiyar hakkin yan fanshon da s**a mutu.
RUWAN SHA
78. Amincewa da Naira Miliyan 225 don samar da ton 600 na Aluminum Sulfate (Alum) ga ma'aikatun sarrafa ruwa na jihar.
79. Sayan ƙarin injunan bututun ruwa daga Jamus waɗanda za su kasance a matsayin tsarin ajiya idan aka sami lalacewa a nan gaba.
80. Gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a kauyukan Danya da Kyallin Bula da ke karamar hukumar Bichi da Bebeji a jihar Kano bayan shafe shekaru 40 ana fama da karancin ruwa.
81. Aikin gyara na ci gaba a Hukumar Albarkatun Ruwa ta (WRECA), don kammala aikin gyarawa tun daga Tushen Ruwa na Tamburawa.
82. Ci gaba da babban gyara a bangaren tace ruwa na Challawa..
83. Gwamnatin jihar Kano ta cimma matsaya da gwamnatin Faransa na zuba jarin Yuro miliyan 63.4 domin gina kamfanin samar da ruwan sha na Kano karo na uku.
84. Gyara magudanar ruwa da ta tarwatse don hana ambaliyar ruwa ta kowace shekara a lokacin damina a fadin jiha.
NOMA
85. Samar da jimillar gidaje 500,000 don cin gajiyar shirye-shiryen Gwamnatin Jiha ta Tallafawa Noma.
86. Samar da ingantaccen kayan aikin noma ta hanyar KASCO
87. Kokarin dasa itatuwa miliyan 2.5 a jihar domin dakile tasirin sauyin yanayi
88. Dawo da shirin tallafin aiyukan kiwo
89. Gyaran asibitin dabbobi na Gwale
90. Kimanin matasa 200 ne aka horas da su tare da ba su damar gudanar da ayyukan kiwon dabbobi masu zaman kansu a kananan hukumomi 44 na jihar.
91. Haɓaka Cibiyar Insemination na Kadawa, gyara wurin da samar da kayan aiki na zamani.
92. An fara shata shataletalen hanyoyin dabbobi kusan kilomita 1,950 don magance rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya.
93. An tallafa wa mata 2,357 da raguna da tumaki da akuya domin yin kitso da hayayyafa ta hanyar aikin noma na manoma na jihar Kano (KSADP).
94. An baiwa manoman gyada 1,200 ‘Aflasafe’ a karkashin shirin sarkar darajar legumes na KNARDA domin hana asara bayan girbi.
95. Sayan famfunan ruwa guda 2,050 wanda kuma aka baiwa manoman a matsayin wani abin karfafa gwiwa.
96. Gwamnatin jiha a karkashin shirin Agro Processing and Productivity Enhancement and Livelihood Support (APPEALS) na tallafawa manoma 300 akan noman shinkafa, alkama, da tumatur mai daraja.
Bamuyi za6en tumun dare ba