Jarida Radio

Jarida Radio Kafa Mai Inganci Za a Iya Sauraron Jarida Radio Kai Tsaye Ta www.jaridaradio.com Cikin Sa'o'i 24 a Kowacce Rana.
(5)

25/04/2024

Bidiyo: Mai gidan gona ya gano yadda ma'aikata suke satar kwan kaji a gonar

Yanzu-Yanzu: Fursunoni aƙalla 118 sun tsere daga gidan yarin Suleja da ke jihar Neja bayan ruwan sama da ya rusa wani ɓa...
25/04/2024

Yanzu-Yanzu: Fursunoni aƙalla 118 sun tsere daga gidan yarin Suleja da ke jihar Neja bayan ruwan sama da ya rusa wani ɓangare na ginin gidan ranar a Laraba.

25/4/2024

17/04/2024

Bayan dakatarwar da wata babbar Kotun Jihar Kano tayi wa Dr Abdullahi Ganduje, Ya bayyana a harabar sakatariyar jam'iyyar APC dake Abuja tare da mukarraban sa.

In ba a manta ba, a makon nan ne wasu yan jam'iyyar APC na mazabar Ganduje s**a bayyana cewa sun dakatar da Dr Abdullahi Umar Ganduje daga Jam'iyyar a matakin mazaba, lamarin da ya jawo cece-kuce har Uwar jam'iyyar ta Kano ta bayyana cewa wannan wani shiri ne dake da alaƙa da gwamnatin NPP ta jihar Kano.

Hukumar EFCC ta k**a tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a gidansa dake lamba na 9, a unguwar Bengazi Street a Zone ...
17/04/2024

Hukumar EFCC ta k**a tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a gidansa dake lamba na 9, a unguwar Bengazi Street a Zone 4 Wuse Abuja.

A cewar majiyar tashar AIT hukumar EFCC tayi dirar mikiya a gidan sa da misalin karfe 9 na safiyar ranar laraba..

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki kasa ta'annuti ta EFCC ta dira a gidan tsohon gwamna Yahaya Bello da ke Abuja sak**akon zargin almundahanar Naira biliyan 84.

Ra'ayi: Wani abu da aka manta game da tashin darajar Naira. Ina tuna lokacin da ta bayyana ga ƴan Najeriya cewa mai baiw...
15/04/2024

Ra'ayi: Wani abu da aka manta game da tashin darajar Naira.

Ina tuna lokacin da ta bayyana ga ƴan Najeriya cewa mai baiwa shugaban ƙasa shawara akan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya yunƙura kan ganin cewa an daƙile tasirin da Binance ke da shi wajen ƙayyade farashin dollar da Naira, a wannan lokacin dollar ɗaya tayi tashin gauron zabi har ta kai ₦1,880.

Wasu marasa kishin ƙasa sun ta zargi da tuhumar Malam Nuhu Ribadu kan wannan yunkuri, har ta kai ga ana ta furta kalamai marasa kan gado a shafukan tuwita da Facebook, ana ta ɓaɓatun cewa kamfanin na Binance bai taka wata rawa ba wajen karya darajar Naira, aka juya akalar lamarin zuwa siyasa.

Daga baya, a ranar Talata, 5 ga watan Maris din 2024, kamfanin na Binance sun bayyana cewa sun bar gudanarwa a Najeriya, nan take bayan fitar sanarwar ta su Darajar Naira ta fara farfaɗowa a kasuwar canji ta Duniya, a yau Litinin 15 ga watan Afrilu, farashin Dollar ɗaya tana kan ₦1,135 a kasuwar bayan fage ta canji, inda kuma a babban bankin Najeriya take a ₦1,101, shin ba a ga tasirin ba yanzu?

A farkon wannan shekara ta 2024, kudin Najeriya na Naira na daga kuɗi mafi koma baya wajen daraja, amma a ranar Juma'a da ta gabata, Naira ta zama kudi mafi saurin samun daraja (Best Performing Currency) a duniya, k**ar yadda rahoton Goldman Sachs ya fitar. A matsayin mu na masu kishin ƙasa, idan ba mu gode ba ai mun yi butulci.

Ina ganin lokaci yayi da masu kishin Najeriya da cigaban ta zasu gane ina aka dosa a ƙasar nan su ajiye batun adawar siyasa sai lokacin zaɓe ya ƙarato. Zahirin abinda yake bayyana shine; Gwamnatin Shugaba Tinubu na tafiya akan turba, kuma lokaci na cigaba da yin alƙalanci.

Ban ce sai kowa ya sallamawa gwamnati ba, amma muddin aka samu cigaba da nasara, ɓoye ta ba namu bane. Da haka zamu farfaɗo da kyakkyawan fatan da muka yi wa Shugaba Tinubu tun lokacin yaƙin neman zaɓen sa, wanda akan sa ne zamu kai ga cimma muradin sa na ''Sabuwar Najeriya".

Mun gode Mallam Nuhu Ribadu!!!
Mun gode Baba Tinubu!!

11/04/2024

Bidiyo: Yan Ta'adda Sun Yi Taron Idi a Garin Munhaye Na Jihar Zamfara

Majiya: Zagazolamak**a

11/04/2024

Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya ta tabbatar da karin kudin wutar lantarki. Shin kuna samun wutar da ya k**ata ...
03/04/2024

Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya ta tabbatar da karin kudin wutar lantarki. Shin kuna samun wutar da ya k**ata a yankunanku? Everyone Highlights Myanmar 2

3/4/2024

31/03/2024

Check out Jaridaradio’s video.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yace zai tallafawa maniyyatan jihar Kano da Naira 500,000 kowannensu sak**akon ƙarin kuɗin aikin...
27/03/2024

Gwamna Abba Kabir Yusuf yace zai tallafawa maniyyatan jihar Kano da Naira 500,000 kowannensu sak**akon ƙarin kuɗin aikin hajji da aka samu.

27/3/2024

Saudiyya ta shiga gasar Miss Universe a hukumance, inda Rumy Alqahtani ta zama wakiliya ta farko daga kasar.   26/3/2024
26/03/2024

Saudiyya ta shiga gasar Miss Universe a hukumance, inda Rumy Alqahtani ta zama wakiliya ta farko daga kasar.

26/3/2024

Shin kuna ganin nadin Mustapha Rabi'u Kwankwaso dan Injiniya Rabi'u Kwankwaso (tsohon gwamnan Kano) a matsayin kwamishin...
26/03/2024

Shin kuna ganin nadin Mustapha Rabi'u Kwankwaso dan Injiniya Rabi'u Kwankwaso (tsohon gwamnan Kano) a matsayin kwamishina ya k**ata?

26/3/2024

Da Dumi-Dumi: Kotu dake zaune a jihar Kano ta yanke wa dan Chana Mr. Geng hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun shi ...
26/03/2024

Da Dumi-Dumi: Kotu dake zaune a jihar Kano ta yanke wa dan Chana Mr. Geng hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun shi da laifin kashe budurwarsa Ummulkhulsum Sani Buhari wace aka fi sani da Ummeeta.

Allah ya jikan Ummita

26/3/2024

DA DUMI-DUMIAn sako dukkan Daliban Makarantar Kuriga guda 137 da masu garkuwa da mutane s**a sace a jahar Kaduna.Gwamnan...
24/03/2024

DA DUMI-DUMI

An sako dukkan Daliban Makarantar Kuriga guda 137 da masu garkuwa da mutane s**a sace a jahar Kaduna.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ne ya sanar da hakan a shafinsa, Inda ya mika godiyarsa ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Mai bashi shawara akan tsaron kasa Malam Nuhu Ribadu bisa tsayuwar dakar da s**a yi ba dare ba rana don ganin an sako daliban.

Hukumomin kasar Isra'ila sun hana Falasdinawa daga gabar yammacin kogin Jordan shiga masallacin Kudus wato Al-Aqsa da ke...
22/03/2024

Hukumomin kasar Isra'ila sun hana Falasdinawa daga gabar yammacin kogin Jordan shiga masallacin Kudus wato Al-Aqsa da ke gabashin birnin Kudus a ranar Juma'a ta biyu a jere na watan Ramadan.

Shaidu sun shaida wa kafar Anadolu cewa, wasu maza da mata da dama ne sojojin Isra'ila s**a hana su shiga masallacin, suna masu cewa ba su samu izinin shiga masallacin ba.

Wani bafalasdinu Abdullah Hamayel mai shekaru 63 ya tabbatar cewa hukumomin Isra'ila sun hana shi shiga masallacin Kudus, yana iƙirarin cewa bai sami takardar izini ba, duk da cewa yana ɗauke da fasfo ɗinsa na Amurka.

Kafin a fara azumin watan Ramadan, gwamnatin Isra'ila ta sanar da cewa 'a duk Juma'a a duk watan Ramadan, Yahudawa da Samariya (sunan Attaura na Yammacin Kogin Jordan) a bar su su shiga birnin Kudus ba tare da samun izini na shiga da kuma tantance yanayin tsaro ba.’ Rundunar ta kara da cewa maza ne kawai masu shekaru 55, mata masu shekaru 50, da yara ‘yan kasa da shekaru 10.

Sai dai sojoji da 'yan sandan Isra'ila suna hanawa tare da hana musulmi gudanar da sallar Juma'a na mako-mako a cikin jam'i a cikin watan azumi.

Tun bayan barkewar yakin Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, 'yan sanda sun rufe dukkan shingayen binciken da ke gabashin birnin Kudus ga mazauna birnin yammacin gabar kogin Jordan.

Isra'ila ta kaddamar da yakinta akan Gaza bayan wani harin wuce gona da iri da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba. Tun daga lokacin ta kashe Falasdinawa kusan 32,000 tare da jefa yankin cikin matsananciyar yunwa.

22/3/2024

Ra'ayi: Shin in ka/ki ka samu damar isar da sako ga Shugaban Ƙasar Najeriya, Ahmad Bola Tinubu, me za ka/ki ce masa? Rub...
13/02/2024

Ra'ayi: Shin in ka/ki ka samu damar isar da sako ga Shugaban Ƙasar Najeriya, Ahmad Bola Tinubu, me za ka/ki ce masa? Rubuta mana a comment Section.

NB: A kiyaye kalaman cin mutunci da ɓatanci.

Rundunar Yan Sanda ta bayyana sunan Malamin Addinin Musuluncin nan na Jihar Bauchi, Dr Imam Idris Dutsen Tanshi a matsay...
08/02/2024

Rundunar Yan Sanda ta bayyana sunan Malamin Addinin Musuluncin nan na Jihar Bauchi, Dr Imam Idris Dutsen Tanshi a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo.

Sanarwar ta bayyana cewa rundunar yan sanda ta sanya gwagwaban lada ga duk wanda ya gano musu inda malamin yake.

Ana zargin Malamin ne da ƙin amsa kiran kotu bayan ƙarar sa da aka shigar a baya.

Equatorial Guinea 🇬🇶 ta doke masu masaukin baƙi Ivory Coast daci hudu da nema (4-0)
22/01/2024

Equatorial Guinea 🇬🇶 ta doke masu masaukin baƙi Ivory Coast daci hudu da nema (4-0)

Ɓarayin sun afka ma mutanen ƙauyen da misalin ƙarfe 08:00 na daren ranar lahadi Shigar su ƙauyen keda wuya sai s**a harb...
22/01/2024

Ɓarayin sun afka ma mutanen ƙauyen da misalin ƙarfe 08:00 na daren ranar lahadi

Shigar su ƙauyen keda wuya sai s**a harba bindiga sau biyu, sannan s**a riƙa bin mutane da gudu suna k**awa, suna cewa 'ku dakata mu maaikata ne, mun zo mu taimake ku amma kuna ta gudu, to duk wanda ya gudu za mu harbe shi'.

A lokacin wasu kuma s**a shiga gidaje zaƙulo mutane. Wannan dalilin yasa s**a samu damar tattara mutane da yawa, saboda ɓarayin sun yi shigar sojoji ta yadda duk wanda ya gansu zai amince ma'aikata ne.

Wani da ya ƙubuto daga hannun ɓarayin ya bayyana mana cewa lokacin da ɓarayin s**a isa da su wajen baburan su sai s**a ƙirga su, su talatin da ɗaya maza da mata ciki har da ƴan mata da matan aure. Sannan s**a ce kowa ya hau babur, ana cikin rige-rigen hawan babura ya samu mafita ya ƙubuce masu ya dawo gida.

Mutanen garin sun tabbatar mana da faruwar lamarin.amma hukumomin 'yan sanda sun ce suna binciken abin da ya faru.


22/1/2024

22/01/2024
Yau shekaru biyu da kisan Hanifah, wanda wani malamin su Abdulmalik Tanko yayi a jihar Kano.Ya zuwa yanzu dai babu wani ...
20/01/2024

Yau shekaru biyu da kisan Hanifah, wanda wani malamin su Abdulmalik Tanko yayi a jihar Kano.

Ya zuwa yanzu dai babu wani matakin hukunci da aka dauka kan wannan dan talikin.

Shin me zaku ce?


20/1/2024

Daruruwan masu zanga-zangar da s**a hada da ma'aikatan Google ne s**a taru a gaban ofisoshin Google na San Francisco Mas...
17/01/2024

Daruruwan masu zanga-zangar da s**a hada da ma'aikatan Google ne s**a taru a gaban ofisoshin Google na San Francisco

Masu zanga-zangar sun datse t**i tare da hana zirga-zirgar ababen hawa, suna masu neman kawo karshen ayyukan da Google ke yi da gwamnatin Isra'ila, da nuna adawa da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza.

17-01-2024

16/01/2024
An kori Jose Mourinho a matsayin kocin  AS Roma  16/1/2024
16/01/2024

An kori Jose Mourinho a matsayin kocin AS Roma


16/1/2024

A rana irin ta yau 15 ga watan Janairun, 1966 aka kashe Sir. Ahmadu Bello Sardauna da Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa.Me kuk...
15/01/2024

A rana irin ta yau 15 ga watan Janairun, 1966 aka kashe Sir. Ahmadu Bello Sardauna da Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa.

Me kuka sani dangane da mutuwar wadannan bayin Allah?

15/1/2024

Wasu gungun ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da wani mutum mai suna Alhaji Sabiu Abdulkadir tare da ‘ya’yansa mata uku a gida...
15/01/2024

Wasu gungun ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da wani mutum mai suna Alhaji Sabiu Abdulkadir tare da ‘ya’yansa mata uku a gidansu da ke unguwar Damba a Gusau babban birnin jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya.

wani mazaunin unguwar mai suna Aliyu, Ya shaida wa manema labarai cewa Alhaji Sabiu da ‘ya’yansa mata, Hadiza, Fateema da Aisha a lokacin da ‘yan ta’addan s**a mamaye yankin Damba.

Mazaunin garin ya ce ‘yan ta’addan sun tuntubi iyalan Alhaji Sabiu a ranar Asabar inda s**a bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 100 domin kubutar da mutanen.


15/1/2024

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya jaddada alkawarin gwamnatin sa na samar da ci gaba mai dorewa a yankin Neja Delta.Shugaban...
15/01/2024

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya jaddada alkawarin gwamnatin sa na samar da ci gaba mai dorewa a yankin Neja Delta.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da Abubakar Momoh, ministan raya yankin Neja Delta.

Wata sanarwa da Osigwe Omo-Ikirodah, mataimaki na musamman ga ministan ya fitar jiya a Abuja, ta ce taron ya ta’allaka ne da samar da cikakken bayanai kan ayyuka da kuma tsare-tsaren da ke gudana a ma’aikatar raya Neja Delta.

Ya ce taron an yi shi ne domin neman goyon bayan shugaban kasa da kuma jajircewarsa wajen ganin an samu ci gaba mai dorewa a yankin Neja Delta. Kazalika, ya ce a yayin taron, Momoh ya bayyana muhimman ayyuka da tsare-tsare da ma’aikatar ta yi don bunkasa yanayin zamantakewa da tattalin arzikin yankin.


15/1/2024

Gobara ta kashe mutane 7 a unguwar Tudun Wada da ke  KanoWata gobara tayi sanadiyar rasuwar mutane 8 a unguwar Tudun wad...
15/01/2024

Gobara ta kashe mutane 7 a unguwar Tudun Wada da ke Kano

Wata gobara tayi sanadiyar rasuwar mutane 8 a unguwar Tudun wada layin Mal Sani Mai Chemist dake karamar hukumar Nasarawa.

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 12 na Daren jiya Litinin a sak**akon matsalar wutar lantarki. Kuma gobarar tayi sanadiyar rasuwar mijin mai suna Shu'aibu Ahmad da matarsa Binta da kuma 'ya 'yansu guda 6 a lokacin da suke barci.

Wadanda s**a kashe gobarar sun tabbatar wa ta Jarida Radio cewa wutar lantaki ce silar faruwar gobarar, domin ta dinga jan mutane ne, kafin a samu a tsinke wayar wutar. Kuma bayan a b***e kofar dakin aka tarar da gawarwakin mutum 7, kafin ita mah ta 8 din ta rasu da safiyar yau a asibiti.

Shima shaqiqin mamacin me suna Salihu Ahmad yace babu shakka ya kadu da jin labarin kuma sun karbi wannan kaddara,kuma da fatan Allah ya karbi shahadarsu gaba-daya. Kuma tuni aka yi jana'izar mamatan k**ar yadda Addinin musulunci ya tanadar.

A mutanen unguwar sun yabawa hukumar kashe gobara ta jihar kano, dangane da gudumawar da s**a bayar wajen kashe wutar.

15/1/2024

Dan kishin kasa Comr. Shafiu Umar Wakili ya sha alwashin dawo da miliyoyin matasan Arewacin Najeriya tafiyar Kwankwasiyy...
14/01/2024

Dan kishin kasa Comr. Shafiu Umar Wakili ya sha alwashin dawo da miliyoyin matasan Arewacin Najeriya tafiyar Kwankwasiyya a siyasance.

Comr Shafiu wanda aka fi sani da "Wakilin Matasan Arewa" ya jaddada wannan manufa ce a yau, domin cimma burinsa na ba da goyon baya ga tsagin Amana a tafiyar Kwankwasiyya.

Wakilin Matasan Arewa Comr Shafiu ya kara da cewa cimma wannan burin na sa zai kawo sauyi hadi da ci gaba a fadin Najeriya.

Menene ra'ayinku, ta yaya kuke ganin zai fara?

Governor Bauchi Bala Muhammad Abdulkadir yayi Nasara a kotun Kuli amatsayin lahartatcen wanda ya lashe  zaben 2023.  12/...
12/01/2024

Governor Bauchi Bala Muhammad Abdulkadir yayi Nasara a kotun Kuli amatsayin lahartatcen wanda ya lashe zaben 2023.


12/1/2024

Address

No. 2 Morijo Close Wuse II Abuja
Abuja

Telephone

+2348038453896

Website

https://servidor13.brlogic.com:7024/live

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jarida Radio posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jarida Radio:

Videos

Share


Other Broadcasting & media production in Abuja

Show All