DA DUMI'DUMI ASIRIN ATIKU ABUBAKAR YA TONU!
Yadda Dan takarar Neman Shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar da Gwamna Tambuwal da Gwamna Okowa Suke Shirya Yadda Za suyi Maguɗin Zaɓe Gobe.
Ku saurara a wannan sautin muryar za ku ji har yadda suka shiryar yadda suka hada kai da gwamnan babban bankin Najeriya don biyan buƙatar kan su....
Ko Kun San Waye Bola Ahmed Tinubu?
#Arewa4Asiwaju
Saƙon marigayi mai martaba sarkin Katsina, Alh. Dr. Muhammadu Kabir Usman akan siyasa.
Daga Comr Nura Siniya
BIDIYO: Ƙungiyar marubutan Arewa "Arewa Media Writers" ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, da shugaban ƙungiyar na jihar Bauchi Malam Adamu Badamasi, za ta gudanar da gagarumin taron karawa juna sani "National Seminar" na tsawon kwanaki biyu tare da bikin cikar kungiyar shekara biyu.
Ƙungiyar za ta horar da marubutan Arewa sama da 500 game da yadda ake rubutu, aikin jarida da yadda ake amfani da kafofin sada zumunta tare da basu takaddar shaidar karɓar horo (certificate).
Za'a fara gudanar da gagarumin taron ne a ranar jumma'a mai zuwa 15 ga watan July da misalin karfe 3 na yamma, a babban ɗakin taro mai suna Banquet Hall, dake Zaranda Hotel, cikin kwaryar jihar Bauchi.
Za'a rufe a ranar Lahadi 17 ga watan July da misalin ƙarfe 10 na safe idan Allah ya kaimu.
Ƙungiyar "Arewa Media Writers" tana gayyatar dukkannin Marubutan Arewa dama masu sha'awar zama Marubuta da dukkannin kungiyoyin sakai da daidaikun Al-umma baki daya.
Shugaban taro; Mai girma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar, Shattiman Zamfara.
Mai masaukin baki; Mai girma gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Kauran Bauchi.
Manyan baki masu gabatar da jawabi;
Mai girma gwamnan jihar Zamfara Hon. (Dr) Bello Mohammed, (Shatiman Sokoto, Barden Kasar Hausa, Matawallen Maradun).
Mai girma gwamnan jihar Gombe
Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya,
Danmajen Gombe.
Mai girma Ministan Sadarwa Farfesa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.
Mai girma tsohon shugaban hafsan sojin saman Najeriya
Ambassador Sadiq Baba Abubakar.
Mai girma mataimakin Gwamnan jihar Jigawa
Mal. Umar Namadi.
Mai girma shugaban hukumar fasahar sadarwa ta Najeriya, NITDA
Alhaji Kashif Inuwa.
Uban Taro
Mai martaba Sarkin Bauchi
(Dr) Rilwanu Sulaiman Adamu.
Da sauran manyan baki daga sassan Najeriya.
Sanarwa📢📢📢
Daga Ofishin Sakataran Ƙungiyar Na Ƙasa,
Comr Haidar Hasheem Kano.
ICEN DA YA YI KAMA, DA SHI AKE KOTA
Gwamna Bala Ne Dan Takarar Shugaban Kasa Da Ya Kamata Deliget Din PDP Su Zaba
Babu shakka idan muka yi duba da irin ayyukan da Gwamna Bala ya shimfida a jihar Bauchi, za mu iya kafa hujja da hakan wajen ganin ya fi kowane dan takara cancanta da a jefa masa kuri’a yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a matakin takarar shugaban kasa.
Idan kuka saurari wannan bidiyo za ku ji irin hujjojin da aka gabatar wanda hakan ya sa ya fi dacewa da daliget din PDP su kada masa kuri’a a yayin zaben fidda gwani.
Shifa Comrade Ba Abun Rainawa Bane, Marigayi Sheikh Albani Zaria Ma Tsohon Comrade Ne
Maciji Ba Ya Cizon Mumini Musulmi Na Kwarai A Rami Daya Sau Uku Inji Annabi Muhammad (SAW)
Daga Al-mansoor Gusau
Muna da Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin a Kananan Hukumomi, Gwamnati a jiha mu ka shiga zabe a shekara ta 2019, Kotun Kolin Nijeriya 🇳🇬 ta yi Hukuncin da ya karbe dikkanin zababbun kujerun Jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara His Excellency, Hon.(Dr.) Abdul’aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) ya tara magoya bayansa ya fada masu cewa, kaddara ce daga gurin Allah (SWT) kowa ya karba ya yi hakuri.
A al’adar siyasar Nijeriya 🇳🇬, Gwamnatin Tarayya na duba jihohin da ba su kafa Gwamnati a jihohinsu ba a lokacin da za ta raba mukamanta na Ministoci da manyan mukamanta a matakin Tarayya, dik da kaddarar da ta fadawa magoya bayan Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, Gwamnatin Tarayya ba ta baiwa kowa mukamin da za a iya rike al’umma da shi ba, Mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara His Excellency, Hon.(Dr.)Abdul’aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) ya fadawa magoya bayansa cewa, kowa ya yi hakuri haka Allah (SWT) ya kaddara kuma kowa ya yi hakuri.
Mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara His Excellency, Hon.(Dr.)Abdul’aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) ya cigaba da rike magoya bayan Jam’iyyar APC ba tare da kasawa ko daya ba, haka zalika ba tare da samun taimako ko gudunmuwa ko daya ba daga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ba, a haka ya gina Jam’iyyar APC ya dinke dikkanin barakar dake cikin Jam’iyyar APC Sen.Kabiru Garba Marafa tare da Dr.Dauda Lawan Dare aka hadu guri daya aka dinke, al’ummar jihar Zamfara da Nijeriya magoya bayan Jam’iyyar APC ku ne shaidar wannan magana.
Daga karshe Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a karkashin tutar Jam’iyyar APC ta aiko ma Mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara His Excellency,Hon.(Dr.) Abdul’aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) da sakon cewa, Gwamnan jihar Zamfara na Jam’iyyar PDP zai shigo Jam’iyyar APC, Mai girma (Shattiman Zamfara) ya ce ya amince
LABARI CIKIN BIDIYO: Yadda Mata Suka Nuna Kaunarsu Ga Sheikh Dakta Abdallahi Gadon Kaya, A Lokacin Da Ya Gudanar Da Wa'azi A Garin Geidam Dake Jihar Yobe A Ranar Litinin Da Ta Gabata.
Daga Comr Abba Sani Pantami
HAUKA KO GIDADANCI?
Yadda Wani Masoyin Benzima Yayi Wanka Da Ruwan Kwata Tare Da Sha Don Nuna Farin Cikinshi Akan Kwallo Ukun Da Banzima Ya Zura A Wasan Jiya.
Me zakuce?
Daga Comr Abba Sani Pantami
LABARI CIKIN BIDIYO: Isowar Sabon Shugaban Riko Na Jam'iyyar APC Ta Kasa Gwamna Abu Lolo Na Jihar Neja, Hedikwatar Jam'iyyar APC Ta Kasa.
Daga Comr Abba Sani Pantami
Wallahi Ni Musulmine Domin Ina Sallah, Kuma Wallahi Bello Yabo Karya Yake Mun Bai Taba Zama Dani A Kurkuku Har Ya Karantar Dani Ba, Cewar Bello Turji
Daga Comr Abba Sani Pantami
Bello Turji ya mayar da martani ga kalaman Shaikh Bello Yabo da ke cewa 'yan fashin daji ba Musulmi ba ne.
Bello turji ya maida wannan kakkausan martanine a cikin wata tattaunawa da yayi da manema labarai wanda jaridar Aminiya ta wallafa a wannan safiyar ta ranar Litinin.
Inda Bello Turji ya shaidawa Duniya cewa shi musulmine domin yana Sallah, ya kars da cews Bello Yabo karya yake mishi bai taba zama dashi a kurkuku ba, balle har ya karantar dashi ba.
Ku saurari bidiyon tattaunawar Bello Turji da manema labarai, sai ku bayyana mana ra'ayoyinku?
Duk Wani Farin Mutum A Najeriya Ko Afrika To Wallahi Dan Bleaching Ne Ba Hasken Shi Bane, Cewar Wannan Matashin.
Ku Saurari Hujjojinshi Ku Bayyana Mana Ra'ayoyinku....
Daga Comr Abba Sani Pantami