19/11/2023
Shugaban Hukumar Ecowas ko Cedeao, Dakta. Omar Alieu Touray, ya taya murna ga zaɓaɓɓen Shugaban Liberiya.
"Cikin sanarwar da ya fitar ranar 18 ga Nuwamba, Shugaban Hukumar Ecowas ko Cedeao, Dakta. Omar Alieu Touray, ya taya Joseph Nyuma Boakai murnar, bayan zaɓensa a matsayin Shugaban Ƙasar Liberiya".
"Shugaba Touray, ya tabbatar wa sabon zaɓaɓɓen Shugaban Liberiya, cewa Ecowas ko Cedeao, za ta ci gaba da taimaka wa "mutanen Liberiya" wajen inganta zaman lafiya, da tsaro, da demokaraɗiyya da ƙarfafa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a ƙasar, " in ji sanarwar da aka wallafa ranar 18 ga Nuwamba, a shafin Facebook na Ecowas/Cedeao.
Sak**akon, da Hukumar Zaɓen Ƙasar, ta wallafa ranar juma'a, bayan karɓar kuru'un rumfunan zaɓen fiye da 99%, ya nuna cewa, ɗan takarar jam'iyyar adawa ta Unity Party, Joseph Nyuma Boakai, mai shekaru (78), ya samu kaso 50,89%, yayin da Shugaban ƙasa, George Weah, da ke neman wa'adi na 2, ya samu ƙashi 49,11%.
Ɗan adawar, ya bai wa ɗan takarar -jam'iyyar CDC mai mulki, George Weah, ratar kuri'a 28.000, bayan tattara kuri'u Miliyan 1,6 na zaɓen shugaban ƙasar zagaye na 2, da aka yi ranar 14 ga Nuwamban, 2023.
Shugaba Weah, ya amince da shan ƙayi, inda ya ƙira abokin ƙarawarsa, Joseph Boakai, ta wayar tarho domin taya shi murnar, bayan zaɓensa a matsayin sabon shugaban ƙasar Liberiya.
M. Joseph Boakai, ya riƙe muk**ai da dama cikin har da na mataimakin shugaban ƙasa, ƙarƙashin mulkin tsohuwar shugabar Liberiya, Ellen Johnson Sirleaf, daga (2005 zuwa 2017.