![Wannan shine Uranium.A Nijar a na haƙar wanda farashin sa ya kai kimanin 5500.Milliards a ko wace shekara. Amma Nijar ba...](https://img5.medioq.com/116/792/282558871167920.jpg)
29/08/2023
Wannan shine Uranium.
A Nijar a na haƙar wanda farashin sa ya kai kimanin 5500.Milliards a ko wace shekara. Amma Nijar ba abinda take samu cikin wannan zunzurutun kuɗin face 86. Milliards kaɗai 👌.
Alhali Bajat ɗin Nijar na ko wace shekara 2908.Milliards ne, shi yasa dole sai taci bashi ga wasu ƙasashe ko a bankin duniya kafin ta samu ta tafiyar da harkokin da albashin ma'aikata na ko wace shekara.
Wanda da'ace tana samun cikakken kuɗin Uranium ɗinta na ko wace shekara to babu zancen ciyo bashi, kai harma sai an raga mai yawa, wanda za'ayi wasu ayyukan raya ƙasa dasu.
Ku tayamu Lissafi : 5500-2908=2592.
Ma'ana da ace Nijar na samun kudin ta yadda ya yadace, to babu maganar Talauci a Nijar sam sam, saboda ko rabin kudin da ake samu a shekara bamu cinye wa.
Za'a gina ƙasa da sauran kuɗin, za'a haɓɓaka sauran ɓangarori daban-daban, kamar Ilimi, noma, kasuwanci, kere-kere da sauransu.
Kuma za'a samarwa Matasa ayyukan yi a cikin ƙasa, babu Maganar zaman banza, babu zancen tafiya wasu ƙasashe neman aiki.
Amma inaaaaaa.... Faransa 🇲🇫 tayi kaka gida. Shiyasa kar kuyi mamaki irin yadda ta kafe ta cije ta Turje babu inda zata, saboda tasan abinda kenan.
Duk ɗan Siyasar da ya nuna zai koresu to Tabbass sai sunyi yadda zasu yi su kifar dashi. Baba TANJA MAMADOU Misali ne. Kai hatta da shi BAZOUM da yawa daga cikin yan ƙasa sun ganin yana daga cikin dalilin kifar dashi saboda ya fara turjiya ne ga wasu manufofi ne na Faransa, ba ya zartar da lamura kamar yadda Faransa ke so.
A gaskiya babu wanda zai iya korar Faransa daga Nijar in ba Mulkin Soja ba. Shi yasa kar kuyi mamaki yadda ƴan Nijar s**a nuna goyon bayansu gaba ɗaya, neman ƴanci ne.