27/05/2021
SHAWARA CE¶¶¶
Akwai buƙatar Maza su rinƙa ƙara Aure, domin abun ya fi ƙarfin wasa. Wallahi idan ka shiga gidaje da dama za ka tarar 'yan mata sun cika gidan, za ka ga Budurwa na da ƙanne mata 4 ko 5 kuma duk sun isa aure, ga kuma wasu 'yan saffa kusan 8 suna rige-rigen tasowa don a dama da su. Wannan ai abun baƙin ciki ne ga iyaye a ce sun tara 'yan mata rigis a gabansu ba tare da manema ba, duk wanda ke da tausayi dole ya tausaya. Kamata ya yi a fito da wani tsari don wayar da kan maza game da lamarin nan.
Sannan a fito da wani tsari na wayar da kan mata don su daina hana Mazajensu ƙaro Aure, ko su rinƙa ganin Abokiyar zama a matsayin Kishiya abar yin gaba.
Sannan a fito da wani tsari don wayar da kan iyaye game da tsawwalawa duk wanda ya zo neman Auren 'ya'yansu.
Kuma a fito da wani tsari don wayar da kan samari da 'yan mata game da buri, kwaɗayi, da kuma yaudara.
Duk waɗannan su ne abubuwan da ya kamata a tsaya a duba don magance yawaitar taruwar 'yan mata a cikin gidajen iyayensu, da kuma magance matsalolin da ke haifar da haka.