30/11/2024
✍️🔵🔴 | TARIHIN ƘUNGIYAR FC BARCELONA!
❤️ “A yau ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona take bikin cikarta shekara 125 da kafuwa.
— A rana mai kamar ta yau 29 ga watan Nuwamba a shekarar 1899 aka kafa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ƙarƙashin jagorancin wani mutum ɗan asalin ƙasar Switzerland wanda ake kira da tareda haɗin gwiwar wasu mutane daga ƙasar England dakuma wasu ƴan wasa daga Catalonia.
Tin daga lokacin da Hans Gamper yafara tinanin ya za'ai yakafa ƙungiya a birnin Barcelona, Saiya fara gayyatar manyan abokansa kan suzo su zauna akan wannan batu.
A ranar 22 gawatan October a shekarar 1899 Hans Gamper da abokansa s**ayi zama na ƙarshe kuma s**a tabbatar dazasu buɗe ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona.
A wannan lokaci ansamu ƴan wasa 11 Wanda s**a hada da Lluís d'Ossó, Bartomeu Terradas , Otto Kunzle, Otto Maier, Enric Ducal, Pere Cabot, Carles Pujol, Josep Llobet, John Parsons, Haɗeda William Parsons ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na farko wato President ɗinsu na farko Walter Wild saide a lokacin Barcelona ta fara buga wasanta na farko da yan wasa 9 Inda take buga tsarin 2-3-3.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta fara wasaninta da ƙafar dama daga matakin na farko inda tafara buga kofin Campionat
de Catalunya dakuma Copa del Rey.
A ranar 1902 Barcelona ta fara ɗaukar kofinta na farko Copa Macaya, kuma a shekarar tafara zuwa wasan ƙarshe Na Copa Delrey saide tayi rashin nasara daci 2-1.
A ranar 1908 Joan Gamper yazama President din kungiyar Inda yakarbi kungiyar a lokacin da s**a shiga cikin wani hali na rashin dedeto dakuma matsalar kudi gamida kamfar daukar Kofi tindaga 1905 harzuwa 1908, awannan lokaci Joan Gamper ya karbi kungiyar Inda alokacin yakira taron domin zama na gaggawa, Inda a wajen taron Joan Gamper yayimusu bayani mai ratsa cikin zuciya dakuma ƙarfafa musu gwiwa daga cikin bayanansa Joan Gamper yafadi cewa "Barcelona bazata mutuba kuma bazata taɓa mutuwa ba, koda babu Wanda zai tallafa, Ni zan dauki nauyi tafiyar da ƙungiyar daga YANZU."
Tinda wannan shekarar 1908 harzuwa 1925 Joan Gamper yake jagoranta kungiyar Inda a 1909 Joan Gamper Yayi ƙoƙarin ganin sun Gina sabon filin wasa Wanda ake kira da (Camp de la Indústria) Wanda yake ɗaukar mutane 8000 a shekarar 1922 aka ƙara girman filin zuwa kujeru 20,000 daga nan kuma aka ƙara fadadashi zuwa kujeru 30'000 kafin a shekarar 1940 aka fadadashi zuwa kujeru 60'000 yayin da a yanzu filin ke daukar mutum 99,359 kafin a kammala gyaran dazai ɗauki ƴan kallo sama da 100k.
Tabbas karkashin jagoran Joan Gamper Barcelona tasamu nasarori da dama cikin tsawon shekaru 20 da ya jagoranci ƙungiyar.
Cikin shekaru 125 da kafuwar Barcelona Kungiyar tasamu nasarori da dama inda ta lashe kofuna.
Gasar La Liga 27.
Copa del Rey 31.
Super Copa de Espana 14.
Copa de la Liga 2.
Champions League 5.
UEFA Cup Winners Cup 4.
UEFA Super Cup 5.
FIFA Club World Cup 3.
Dan wasan dayafi yawan buga wasa a tarihi shine Xavi Hernandez 767.
Mafi yawan zura ƙwallaye a tarihin ƙungiyar Lionel Messi 672.
Ɗan wasa mafi samun nasara a tarihin shine Lionel Messi Kofuna 35.
Mai horaswa mafi nasara a tarihi Pep Guardiola Kofuna 14.
Ɗan wasa mafi daraja da tsada a tarihin kungiyar shine Philippe Coutinho $144m.
Kasancewar rubutun yayi tsayi anan zamu dakata saikuma wani lokacin idan da hali zamuci gaba.
✍️ Daga: Shamsu Dini Gama