Mahmoud Adam

Mahmoud Adam humble and gentle

Jami'in ɗan sandan da Shugaba Buhari ya karrama saboda ya ƙi karɓar cin hancin dala $200,000 a 2022, ya karɓi musulunci ...
09/01/2025

Jami'in ɗan sandan da Shugaba Buhari ya karrama saboda ya ƙi karɓar cin hancin dala $200,000 a 2022, ya karɓi musulunci

ACP Daniel Amah a baya, yanzu ya koma Muhammad, kuma ya karɓi musulunci ne a fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a ranar Talata da ta gabata.

Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya nada mawaka da masu wasan barkwanci har ma da masu bukata ta musamman sama da 50 a ma...
06/01/2025

Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya nada mawaka da masu wasan barkwanci har ma da masu bukata ta musamman sama da 50 a matsayin mataimaka na musamman.

Wace gudummuwa kuke hasashen zasu bayar wajen gyara tarbiyya a jihar?

Kungiyar Dattawan Arewa ta "League of Northern Democrats" karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekara...
06/01/2025

Kungiyar Dattawan Arewa ta "League of Northern Democrats" karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ta shirye sauya manufa zuwa jam'iyyar siyasa a Najeriya.

DA ƊUMI-ƊUMI: Hukumar tace finafinai da ɗab'i ta jihar Kano ta dakatar da jaruma Sahma M. Inuwa daga shiga harkar fim na...
04/01/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Hukumar tace finafinai da ɗab'i ta jihar Kano ta dakatar da jaruma Sahma M. Inuwa daga shiga harkar fim na tsawon shekara ɗaya, tare da ƙwace shaidarta ta zama halastacciyar 'yar fim.

Hakan k**ar yadda sanarwa daga jami'in yaɗa labaran hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ta ce ya biyo bayan zargin jarumar da shigar bąɲza da kuma furta wasu kálamąi da ake ganin sun saɓa addiɲi da al'adar Hausawa.

Me zaku ce?

Shugaban mulkin sojin Nijar janar Abdoulrahamane Tiani ya gana da wasu kungiyoyin Bokayen Nijar da na AfrikaA yayin gana...
03/01/2025

Shugaban mulkin sojin Nijar janar Abdoulrahamane Tiani ya gana da wasu kungiyoyin Bokayen Nijar da na Afrika

A yayin ganawar ta su kungiyoyin Bokayen sun yi alkawari ga janar Tiani za suyi amfani da gungun aljanu wajen afkawa duk wasu kasashe da ke yi wa Nijar din zagon kasa

01/01/2025

🤣😂🤣😂🤣😂🤣

Gwamnatin kasar Côte d’Ivoire ta sanar da kudurinta na katse alakar soja da Faransa, inda sojojin Faransa za su fice a c...
01/01/2025

Gwamnatin kasar Côte d’Ivoire ta sanar da kudurinta na katse alakar soja da Faransa, inda sojojin Faransa za su fice a cikin watan nan na Janairu, a cewar hukumomi a birnin Abidjan

Bola Tinubu ya zo na uku cikin jerin masu cin hanci da rashawa na duniya, da  masu aikata laifuka na shekarar 2024Kungiy...
31/12/2024

Bola Tinubu ya zo na uku cikin jerin masu cin hanci da rashawa na duniya, da masu aikata laifuka na shekarar 2024

Kungiyar Organized Crime and Corruption Reporting Project (OCCRP), wata ƙungiya ce ta binciken masu cin hanci da rashawa da masu aikata laifuka ta duniya, kungiyar ta sanar da jerin sunayen manyan mutane masu cin hanci na shekarar 2024. A wannan jerin, an sanya sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Wanda shine ya zo na uku a cikin jaddawalin.

OCCRP ta gudanar da zaɓen ne ta hanyar karɓar ƙuri’u daga mutane daban-daban a duniya, don gano wadanda s**a taka rawa sosai wajen haɓaka cin hanci, rashin gaskiya, da ƙara talauci a ƙasashen su.

A jerin wannan shekara, Shugaba Tinubu ya samu matsayi na uku, bayan tsohon shugaban Indonesia, Joko Widodo. Shugaban Kenya, William Ruto, ne ya samu ƙuri’u mafi yawa a jerin. Amma babban lambar yabo ta "Person of the Year" an ba tsohon shugaban Siriya, Bashar al-Assad, wanda aka ce ya gudu zuwa Rasha bayan shekara da shekaru yana sace dukiyar ƙasarsa.

Fitaccen Dan fafutukar kare hakkin bil'adama dake Ƙasar Jamus Dr. Idris Ahmed  ya bayyana rashin jin  dadinsa akan k**a ...
30/12/2024

Fitaccen Dan fafutukar kare hakkin bil'adama dake Ƙasar Jamus Dr. Idris Ahmed ya bayyana rashin jin dadinsa akan k**a fitaccen dan gwagwarmaya Malam Mahadi Shehu.

A cewar Idris "Ikon Allah sai kallo! Abin kunya baya karewa a Najeriya. DSS sun gagara k**a babban dan ta'adda, Bello Turji. Amma don rainin wayo, babban dan kishin Arewa, Dr Mahdi Shehu, shine wanda aka k**a shi
Allah wadan naka ya lalace!

Ahmad ya bukaci a gaggauta sake Mahadi Shehu k**ar yadda bayyana cikin alamar

Gwamnatin Tinubu ta karɓi bashin Bankin Duniya bayan cika sharaɗin cire tallafin mai 🤔🤔🤔🤔🤔
30/12/2024

Gwamnatin Tinubu ta karɓi bashin Bankin Duniya bayan cika sharaɗin cire tallafin mai 🤔🤔🤔🤔🤔

A Najeriya akalla mutane 13 sun mutu sak**akon wani hatsarin mota a jihar Ondo. Hatsarin ya afku ne tsakanin wasu motoci...
29/12/2024

A Najeriya akalla mutane 13 sun mutu sak**akon wani hatsarin mota a jihar Ondo. Hatsarin ya afku ne tsakanin wasu motocin bas na safa-safa biyu a kan babban hanyar Owo/Ikare-Akoko.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa hatsarin ya wakana ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Asabar. Mutane 13 sun ƙone ƙurmus yayin da aka ceto wani guda da ya samu munanan raunuka.

📷Daily Trust

Abinda ya faru yau a birnin Niamey na Jimhuriyyar Nijar inda masu zanga zanga s**a dinga ambatar sunan shugaban Najeriya...
29/12/2024

Abinda ya faru yau a birnin Niamey na Jimhuriyyar Nijar inda masu zanga zanga s**a dinga ambatar sunan shugaban Najeriya suna aibata shi tare da yin zanen hotunansa suna munana shi su sani, wannan babban abin kunya ne da takaici, zagin Shugaba Tinubu a wajen 'yan Nijar su sani zagin dukkan 'yan Najeriya ne, domin a yanzu haka Bola Ahmed Tinubu shi je shugaban dukkan 'yan Najeriya.

Abinda s**a yi ya saɓa da ƙa'idar 'yan uwantaka da kuma mutuntaka dama maƙwabtaka. Ya k**ata mutanan Jimhuriyyar Nijar su sani saɓani ba aibu bane. Akwai wata ƙa"ida ta rayuwa da ta ke cewa:

“Zan iya faɗa da ɗan uwana, amma akansa zan iya faɗa da duniya”. Wannan shine taken ‘yan uwantaka. Sabani a tsakanin ‘yan uwa ɗabi’a ce da ɗan Adam ba ya iya guje mata, sai dai abin so shi ne kiyayewa da kuma ɗaukar matakin sassauta saɓanin domin wanzuwar ‘yan uwantaka.

Najeriya (musamman Arewa) da Jimhuriyyar Nijar ‘yan uwa ne da s**a haɗu a wasu abubuwa da yawa, k**a daga addini, al’ada, harshe, kasuwanci, kan iyaka, tarihi da zumuncin auratayya. A ɗabi’ance waɗannan sune abebaden da s**a fi haɗa kan bani-adama.

A ɗabi’ance, abu ne maimatuƙar wahala a ga ƙani ya fito duniya yana cin zarafin wansa saboda wani saɓani da ya shiga tsakaninsu, duk saɓanin da ba za a iya sulhunta shi a cikin gida ba, ba shakka babu amfanin fitowa da shi duniya a yayata shi matuƙar sulhu da fahimtar juna ake nema. Saboda haka, ba zai zo da mamaki ba idan makwabtan juna s**a samu sabani, sai dai babban abin nema a irin wannan hali shi ne, nuna dattako, sanin ya k**ata da hangen nesa domin akwai gobe.

Amma sam shugabannin mulkin sojan Nijar basu san haka ba, sun yi amfani da jahilcin mutanansu s**a ingazasu akan ƙiyayyar mutanan Najeriya, domin zagin shugaban Najeriya zagin baki ɗayan 'yan Najeriya ne. Allah yasa su gane.

Yasir Ramadan Gwale
28.12.2024

Wanda aka sabunta Mintuna 11 da s**a wuceHukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu ta aƙalla mutum 167 ne s**a mutu a hatsa...
29/12/2024

Wanda aka sabunta Mintuna 11 da s**a wuce

Hukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu ta aƙalla mutum 167 ne s**a mutu a hatsarin jirgin saman ƙasar bayan da wani jirgin saman fasinja ya kauce daga titinsa yayin da yake sauka a filin jirgin sama a Koriya ta Kudu.

Jirgin kirar Boeing 7-3-7 ya sauka kenan, bayan dawowa gida daga Bangkok na kasar Thailand, dauke da fasinjoji 175 da ma'aikatansa shida.

Saukar ta sa ke da wuya ne ya kwace ya saki titinsa ya kutsa ta cikin wani gini, kana ya k**a da wuta.

Shaidu sun ce sun ji karar fashewar wani abu mai karfi bayan faruwar lamarin.

Gwanin Burgewa:Wata Matashiya Ta Lashe Kyautar Mota A Musabakar Alkur'ani Mai Girma, ta Shekarar 2024.
29/12/2024

Gwanin Burgewa:

Wata Matashiya Ta Lashe Kyautar Mota A Musabakar Alkur'ani Mai Girma, ta Shekarar 2024.

MAI WASAN BARKWANCI VDM YANA FUSKANTAR S**A BIYO BAYAN SANAR DA SACE MILIYAN 180 DA AKA TARA DON TAIMAKAWA GAJIYAYYU A A...
28/12/2024

MAI WASAN BARKWANCI VDM YANA FUSKANTAR S**A BIYO BAYAN SANAR DA SACE MILIYAN 180 DA AKA TARA DON TAIMAKAWA GAJIYAYYU A AKAWUNT ƊINSA

Shahararren mai wasan barkwanci a shafukan sadarwa, Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan (VDM), ya ce an yi kutse a asusun ƙungiyar tallafawa al'umma da ya kafa.

Ya bayyana cewa wannan kutse ya haifar da sace sama da naira miliyan 180 da aka tarawa ƙungiyar don rabawa marasa ƙarfi a faɗin Nijeriya.

Daily Trust ta rawaito cewa Otse ya kaddamar da gidauniyar taimakon al'umma mai suna Martins Vincent Osei Initiative a watan Oktoba.

Gidauniyar ta samu gudunmowa mai yawa, ciki har da naira miliyan 35 cikin awanni kadan, da kuma naira miliyan 100 daga wani fitaccen mai shirya wakoki, Michael Collins Ajereh, wanda aka fi sani da Don Jazzy.

A wani faifen bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram a yau Juma’a, Otse ya bayyana cewa an karkatar da kudin zuwa wani asusu da ba a sani ba.

A cewarsa, an k**a wani mutum da ake zargi, sannan an rufe asusun domin hana karin barna.

VeryDarkMan ya ce: “Gaskiya, ba ni da nutsuwa kwanan nan. Wani ya yi wa asusun gidauniyar mu kutse, kuma naira miliyan 180 sun bace amma mun bi sawun wanda ya aikata hakan, kuma an k**a wani da ake zargi," in ji shi.

Alhamdu lil Laahi!Rumaisa'u Dahir Ibrahim ta zama Gwarzuwar Shekara a Al-Qur'ani. Mun godewa Allah, kuma muna adduah, Al...
28/12/2024

Alhamdu lil Laahi!
Rumaisa'u Dahir Ibrahim ta zama Gwarzuwar Shekara a Al-Qur'ani.
Mun godewa Allah, kuma muna adduah, Allah Ya sa Al-Qur'ani Ya cecemu gobe Kiyama.

SURE
28/12/2024

SURE

Masha Allah
14/09/2024

Masha Allah

Indirizzo

Via Unione Sovietica Carpi Modena
Bologna
41012

Telefono

+393716164432

Sito Web

Notifiche

Lasciando la tua email puoi essere il primo a sapere quando Mahmoud Adam pubblica notizie e promozioni. Il tuo indirizzo email non verrà utilizzato per nessun altro scopo e potrai annullare l'iscrizione in qualsiasi momento.

Contatta L'azienda

Invia un messaggio a Mahmoud Adam:

Video

Condividi