DW Hausa

DW Hausa Muna gabatar da labarai daga Jamus da Afirka da ma duniya gaba daya. Muna bukatar shawarwarinku. Legal notice: http://bit.ly/dwlegalnotice

Deutsche Welle, tashar da ke watsa shirye-shiryenta zuwa ƙetare, tana gabatar da labarai da rahotanni ta yanar-gizo da rediyo domin baiyanar da yadda ƙasashen Turai suke kallon al'amura ga masu sauraro a ko'ina cikin duniya. Burinmu shi ne: "Mu ƙarfafa fahimtar yadda Jamus take a matsayin 'yantacciyar ƙasa da tushenta yake tare da al'adun Turai, kuma a matsayinta na ƙasa mai matsakaicin ra'ayi, ta

demokradiyya, mai bin dokokin tsarin mulki da shari'a. Shirye-shiryen DW suna isa ga masu sauraro da masu kallo miliyan 86 a ko'ina cikin duniya.

Watanni shida bayan hawa kujerar mulki, miliyoyin 'yan Najeriya na zaman jiran sanin kaddarorin Shugaba Bola Ahmed Tinub...
11/12/2023

Watanni shida bayan hawa kujerar mulki, miliyoyin 'yan Najeriya na zaman jiran sanin kaddarorin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda har kawo i yanzu bai kai ga bayyana su ba.

Wattani shida bayan hawa bisa kujerar mulki miliyoyi a cikin Najeriya na zaman jiran sanin kaddarori na shugaba Bola Ahmed Tinubu.

11/12/2023

Shirin Yamma

Barkanmu da yammacin Litinin. Shirinmu da ke tafe na wannan maraice, ya yi muku tanadin wadannan rahotanni:Shugaban Naje...
11/12/2023

Barkanmu da yammacin Litinin. Shirinmu da ke tafe na wannan maraice, ya yi muku tanadin wadannan rahotanni:

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kai wata ziyara aiki ta kwana guda a jihar Borno inda ya gana da masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro da kuma al’ummar jihar domin duba yadda za a magance matsalolin tsaro da jihar da sauran sassan arewa maso gabas ke ciki.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma Ecowas na fuskantar kalubalen hadin kai a tsakanin kasashen mambobinta, inda uku daga cikin kasashen da sojoji ke mulki s**a kafa sabon kawance na tsaro. Shin yaya karfin wannan barazana ga wanzuwar kungiyar a wannan lokaci?

A Jamhuriyar Nijar bayan zaman taron kungiyar CEDEAO ko ECOWAS da ya jaddada takunkumin karya btattalin narzikin da ke kan kasar, al“umma da sauran manazarta na yin kira ga shugabannin kasashe uku na AES na yankin Sahel da su dauki matakai na raba gari da wannan kungiya da s**a ce ta zamana yar amshin shatar kasashen yamma.

Bayan kwashe sama da watanni bakwai ana gwabza yaki, bangarorin masu gaba da juna a rikicin kasar Sudan sun lamunta da ganawar keke-da-keke da nufin tattauna matakan cimma yarjejeniyar dakatar da buda wuta mai dorewa, lamarin da ke ci gaba da jawo martani mabambanta daga masharhanta dama ‘yan kasar.

Yayin da ake taro kan sauyin yanayi na duniya a birnin Dubai na Hadaddiyar Daulan Larabawa, kasar Afirka ta Kudu na shan matsin lamba game da kawo karshen amfani da mak**ashin kwal da ta dogara a kai 100 bisa 100.

Faransa na tsara wata sabuwar doka da ta ce za ta takaita kwararar bakin haure amma kuma za ta karbi ma'aikata 'yan ci rani da ake bukata. Sai dai a waje guda 'yan ciranin na baiyana damuwa cewa dokar za ta kara mayar da su saniyar ware ne kawai.

Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da manya da kananan motoci 107 masu amfani da lantarki da kuma iskar gas irinsu na farko...
11/12/2023

Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da manya da kananan motoci 107 masu amfani da lantarki da kuma iskar gas irinsu na farko a Najeriya, wadanda gwamnatin Gwamna Babagana Umara Zulum ya samar domin rage wa talakawa radadin tsadar sufuri a jihar Borno.

📸 Borno News Daily

A kokarin rage tsadar mak**ashin girki da jama’a ke amfani da shi a Najeriya, gwamnatin kasar da soke batun biyan harajı...
11/12/2023

A kokarin rage tsadar mak**ashin girki da jama’a ke amfani da shi a Najeriya, gwamnatin kasar da soke batun biyan harajın VAT da ma karbar kudin fito daga dillalan da ke shigo da iskar daga kasashen waje.

Ko kuna ganin hakan zai sauko da farashin gas din na girkin a kasuwanni?

11/12/2023

A wannan makon ne za mu fara gabatar muku da sabon shirinmu na KALLABI wanda zai rika duba lamuran da s**a shafi mata a yanayin zamantawar kasar Hausa.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalai da dangi da abokan aikin tsohuwar ma'aikaciyar talab...
11/12/2023

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalai da dangi da abokan aikin tsohuwar ma'aikaciyar talabijin ta kasa NTA, Hajiya Aisha Bello Mustapha.

Miliyoyin 'yan Najeriyar ne ke alhinin rashin sananniyar fuskar, wadda ta yi ritaya a bara, bayan kwashe shekaru 35 tana aiki.

Tuni aka yi jana'izar marigayiya Hajiya Aisha a Abuja babban birnin kasar.

11/12/2023

Shirin Rana

Barkanmu da wannan lokaci. Ga rahotannin da shirinmu na rana ke kunshe da su:Shugaban gwamnatin soja a Nijar Janar Abdou...
11/12/2023

Barkanmu da wannan lokaci. Ga rahotannin da shirinmu na rana ke kunshe da su:

Shugaban gwamnatin soja a Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ya nuna rashin jin dadinsa da matsayin taron shugabannin kungiyar ECOWAS na jaddada takunkumin tattalin arzikin da s**a saka wa kasar yayin da da kasar ke kokarin ganin an janye mata shi. Ana dai samun ‘yan Nijar din da ke goyon bayan matakin ECOWAS yayın kuma da masu ke yin tir.

Yayin da ‘yan majalisar dattawan Najeriya s**a ba da Naira miliyan 109 dan tallafa wa wadanda harin bama-bamai a Kaduna ya rutsa da su, wata kungiyar lauyoyin arewacin kasar mai mambobi 601 ta bukaci gwamnatin ta biya diyyar Naira miliyan 200 a kan kowane rai da aka rasa a lamarin na Tudun Biri.

A Najeriyar har yanzu shugaban kasar Bola Tinubu bai bayyana kadarorin da ya mallaka ba, watanni shida da hawansa kan karagar mulki.

Yayin da Falasdinawa a Gabas ta Tsakiya ke matsayi daban-daban na shari'a da matakan zamantakewa, babban abin da galibin su ke bukata shi ne kafa kasashe biyu na Isra’ila da Falasdinu da cikakken ‘yanci.

Kungiyar ECOWAS wadda ta nuna bacin rai a kan ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed da iyalansa, ta ce Nijar za ta ci ...
11/12/2023

Kungiyar ECOWAS wadda ta nuna bacin rai a kan ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed da iyalansa, ta ce Nijar za ta ci gaba da zama cikin takunkumi muddin dai sojojin juyin mulki s**a gaza bin ka'idojin da shugabannin kasashen uku da ke kwamitin da ta kafa s**a bayar.

'Yan majalisar dattawan Najeriya su 109 sun ziyarci yankin Tudun Biri da sojoji suda sakar wa bama-bamai, kuma s**a sana...
11/12/2023

'Yan majalisar dattawan Najeriya su 109 sun ziyarci yankin Tudun Biri da sojoji suda sakar wa bama-bamai, kuma s**a sanar da sadaukar da albashinsu na wata guda.

Karo na 16 ke nan da ake samun irin wannan hari da ake cewa bisa kuskure ne.

Me za ku ce game da matakan da hukumomin Najeriya ke cewa za su duka kan lamari, ya zuwa yanzu?

Firmanistan gwamnatin Bazoum ne kan kujerar da aka kebe wa Nijar a taron ECOWAS. Ouhoumoudou Mahamadou na tare da wasu t...
10/12/2023

Firmanistan gwamnatin Bazoum ne kan kujerar da aka kebe wa Nijar a taron ECOWAS.

Ouhoumoudou Mahamadou na tare da wasu tsoffin gwamnatin Bazoum a taron shugabannin kungiyar ECOWAS da ke shirin duba mataki na gaba kan juyin mulki a kasashen yammacin Afrika.

Tun bayan kifar da gwamnatin Bazoum, ECOWAS ta shiga takon saka da sabuwar gwamnatin Nijar ta Janar Tchiani.

📸Ubale Musa

10/12/2023

A ranar yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yancin dan Adam, sai dai duk da gwgwarmayyar da ake ta yi haƙƙin ɗan Adam na fuskantar matsin lamba fiye da kowane lokaci musamman a Najeriya. Ga bidiyon tattaunawar da shugaban kungiyar Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi, ya yi da wakilinmu a Najeriya Uwais Idris. Shin ya abin yake a yankunanku? Ana mutunta hakkin dan Adam?

09/12/2023

Rashin adalci ne a bukaci Tinubu ya yi murabus kan kisan sojoji a Kaduna - Fadar Shugaban Kasa

An tafi hutun rabin lokaci ba wanda ya zura kwallo a raga tsakanin Wolfsburg da Freiburg
09/12/2023

An tafi hutun rabin lokaci ba wanda ya zura kwallo a raga tsakanin Wolfsburg da Freiburg

Bayern Munich na diban kida a hannun Frankfurt ga sak**akon 👇'yan wasan da s**a saka kwallo su ne---- Hugo Larsson 36'- ...
09/12/2023

Bayern Munich na diban kida a hannun Frankfurt ga sak**akon 👇
'yan wasan da s**a saka kwallo su ne---

- Hugo Larsson 36'
- Éric Dina Ebimbe 31'
- Omar Marmoush 12'

Har yanzu babu nasara a kwallon da ke gudana a tsakanin Freiburg da WolfsburgA wasu sauran filayen wasa ana cin Bayern 2...
09/12/2023

Har yanzu babu nasara a kwallon da ke gudana a tsakanin Freiburg da Wolfsburg

A wasu sauran filayen wasa ana cin Bayern 2-0
Union Berlin na cin Mönchengladbach 1-0

A yanzu kungiyar Wolfsburg ta fi kuzari a wasan d ake fafatwa kai tsaye  yanzu, to amma kuma ta barar d kwallo a gaban m...
09/12/2023

A yanzu kungiyar Wolfsburg ta fi kuzari a wasan d ake fafatwa kai tsaye yanzu, to amma kuma ta barar d kwallo a gaban mai tsaron gidan Freiburg

Freiburg na kai hari, amma kuma ba nasarar saka kwallo a ragar Wolfsburg
09/12/2023

Freiburg na kai hari, amma kuma ba nasarar saka kwallo a ragar Wolfsburg

An fara wasa tsakanin Wolfsburg da Freiburg
09/12/2023

An fara wasa tsakanin Wolfsburg da Freiburg

Nan gaba kadan Sulaiman Babayo tare da Abdulkarim Muhammad Abdulkarim za su kasance tare da ku kai tsaye a shirinmu na B...
09/12/2023

Nan gaba kadan Sulaiman Babayo tare da Abdulkarim Muhammad Abdulkarim za su kasance tare da ku kai tsaye a shirinmu na Bundesliga live

09/12/2023

Barkanku da safiya. Kuna iya aiko mana da sakonninku wadanda za mu iya karantowa a wasikun rana. Muna dakon su.

Harin sojoji kan 'yan Maulidi ya fito da bukatar yin sulhu da 'yan bindiga - Sheikh Gumi
09/12/2023

Harin sojoji kan 'yan Maulidi ya fito da bukatar yin sulhu da 'yan bindiga - Sheikh Gumi

Sulhu da 'yan bindiga shi ne zai hana sojoji sake kai wa fararen hula hari bisa kuskure - Sheikh Gumi

08/12/2023

Labarin kisan da jirgin soji ya yi wa masu Maulidi a Najeriya da dokar da aka yi a Denmark da ta haramta yaga Al-Qur'ari mai tsarki sun dau hankalin ma'aboda soshiyar midiya a wannan makon.

Barkanmu da wannan yammaci. In an jima cikin shirinmu na karfe bakwai agogon Najeriya da Nijar, za a ji mu da wadannan r...
08/12/2023

Barkanmu da wannan yammaci. In an jima cikin shirinmu na karfe bakwai agogon Najeriya da Nijar, za a ji mu da wadannan rahotanni:

Minitocin kula da harkokin wajen kungiyar kasashen Afrika ta yamma ta ECOWAS sun kammala taronsu a Abuja inda s**a tattauna halin siyasar yankin da kuma tsaro. Taro ne da ya za daidai lokacin da mulkin dimukurdiyya ke fuskantar kalubale a yammacin na Afirka.

Yayin da ake ranar yaki da cin hangi da rashawa a duniya, za mu je Najeriya domin jin yadda ‘yan kasar ke bayyana damuwa kan karuwar matsalar da ke neman zama tarnaki ga ci gaban Najeriyar.

Daga Nijar ma za a ji halin da ake ciki dangane da yaki da cin hangi da rashawa a kasar da ke karkshin ikon soja a yanzu, bayan hambare gwamnatin dimukuradiyya.

A wannan jumma’a ce shugaban mulkin soji a Nijar Birgediya Janar Abdourahamane Tchiani, ya kai wata ziyarar aiki a birnin Lome na kasar Togo inda ya gana da shugaban kasar ta Togo Faure Ngnassingbe.

Yayin da mutuncin Shugaba Abdel Fattah el-Sissi na Masar ya soma gyaruwa, masu lura da al'amura na fargabar cewa ba za a iya warware matsalar tattalin arzikin Masar da kuma batun hakkin bil adama ba, ganin cewa abubuwa ne da s**a yi muni a kasar tun bayan da ya karbi mulki.

08/12/2023

Duk da illolin da ke tattare da cin farar kasa ga lafiyar dan Adam, mata masu rainon ciki, na ci gaba da cin farar kasar a Ghana da ma a sauran kasashen Afirka.

Ku kasance tare da mu an jima a tasharmu ta YouTube don kawo muku hira da mai magana da yawun shugaban Najeriya kan kisa...
08/12/2023

Ku kasance tare da mu an jima a tasharmu ta YouTube don kawo muku hira da mai magana da yawun shugaban Najeriya kan kisan da sojoji s**a yi a Kaduna.

Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi II da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai sun...
08/12/2023

Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi II da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai sun kai ziyarar jaje kauyen Tudun Biri, inda sojoji s**a jefa bama-bamai kan masu Maulidi.

Haka tawagar ‘ya’ya da kuma almajiran jagoran darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta ziyarci wajen a wannan Juma’a.

Babban bankin Najeriya ya nanata cewar da tsoffi da sababbin manyan takardun kudaden kasar za su ci gaba da aiki har sai...
08/12/2023

Babban bankin Najeriya ya nanata cewar da tsoffi da sababbin manyan takardun kudaden kasar za su ci gaba da aiki har sai illa ma sha Allahu.

Wani hali ake ciki game da samun takardun kudi daga bankuna da kuma POS a inda kuke a Najeriya?

Barkanmu da wannan lokaci. Shirinmu na rana daga birnin Bonn, na tafe da wadannan rahotanni:Al'umomin wasu unguwanni a K...
08/12/2023

Barkanmu da wannan lokaci. Shirinmu na rana daga birnin Bonn, na tafe da wadannan rahotanni:

Al'umomin wasu unguwanni a Kanon Najeriya, sun yi zanga-zanga a shelkwatar ‘yan sanda domin neman yadda za a kawo karshen sake salo da gungun ‘yan daba s**a yi na tsarin bin gida-gida suna fashi.

A Nijar, a kokarin kauce wa matsin takunkumin ECOWAS da s**a hada da rufe iyaka da hana kai kawo tsakanin kasar da Najeriya, ‘yan kasuwar birnin Maradi sun raja'a ga amfani da hanyoyin sadarwar zamani dan ci gaba da harkokin kasuwancinsu.

A Chadi ana fuskantar karancin tururuwar masu zuwa karbar katunan zabensu ne a kasar, a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulki cikin kwanaki masu zuwa.

Akwai kuma sharhunan jaridun Jamus da muka saba kawowa a ranakun Juma’a.

Kasar Denmark ta haramta kona Alkur’ani mai tsarki. A zaman da ta yi a jiya Alhamis, majalisar dokokin kasar ta ce laifi...
08/12/2023

Kasar Denmark ta haramta kona Alkur’ani mai tsarki.

A zaman da ta yi a jiya Alhamis, majalisar dokokin kasar ta ce laifi ne a waulakanta rubuce-rubuce da wasu al'umomi mabiya addini ke girmamawa.

Ta tanadi tara da kuma daurin shekaru biyu ga duk wanda aka k**a ya kona ko kuma yaga littafi mai tsarki da wasu ke darajawa.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta jihar Kaduna, sun ce za a hukunta wadanda ke da hannu cikin ta'adın da sojojin kasar s...
08/12/2023

Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta jihar Kaduna, sun ce za a hukunta wadanda ke da hannu cikin ta'adın da sojojin kasar s**a yi na kisan fararen hula a Tudun Biri. Gwamnatocin sun yi alkwarin kyautata rayuwar mazauna yankin, kuma daga ciki har da daukar nauyin marayun da aka bari; sannan akwai biyan diyya.

Hafsan hafsoshin Najeriya ya sake jaddada cewa kasar ba za ta sake ganin wani kusukure daga sojojinta ba, lokacin da yak...
08/12/2023

Hafsan hafsoshin Najeriya ya sake jaddada cewa kasar ba za ta sake ganin wani kusukure daga sojojinta ba, lokacin da yake magana game da bama-baman da sojoji s**a sako da s**a yi sanadin mutuwar masu Maulidi sama da mutum 100 a Kaduna.

07/12/2023

Wani mai lalurar gani a Najeriya da ya kwashe shekaru kusan 40 yana sana'ar kanikanci a Abuja. Babban mai dogaro da kansa ne idan aka yi la'akari da yadda wasu masu nakasa ke barace-barace a kasar. Me za ku ce?

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima ya bayana shirin gwamnatin Tarayyar Najeriya na gudanar binci...
07/12/2023

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima ya bayana shirin gwamnatin Tarayyar Najeriya na gudanar bincike domin zakulo wadanda suda saki bama-bamai a kan fararen hula a kauyen Tudun Biri da ke Kaduna, wanda ya kashe mutane fiye da 100.

Sanata Shettima ya fadi hakan ne a ziyadar da ya kai asibitin da wadanda s**a jikkata a lamarin ke kwance a yau Alhamis.

Barkanmu da yammaci. Shirinmu na karma bakwai agogo Najeriya da Nijar tare da Abdulkarim Muhammad Abdulkarim, na tafe da...
07/12/2023

Barkanmu da yammaci. Shirinmu na karma bakwai agogo Najeriya da Nijar tare da Abdulkarim Muhammad Abdulkarim, na tafe da wadannan batutuwa:

Manyan jami'iyyun adawa a Najeriya sun yanke shawarar hadewa da nufin kwace iko daga hannun jam'iyyar APC da ke kan karaga a yanzu, bayan kwashe lokaci suna ta korafin cewa APC na gasa wa al'ummar kasar aya a hannu.

Kotun kasashen yamacın Afirka ta Ecowas ta yi watsi da karar da gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar da wasu mutane tara s**a shigar inda s**a bukaci da ta tilasta wa shugabanin kungiyar ECOWAS din su janye takunkumin da s**a sanya wa kasar bayan juyin mulki.

A Jamhuriyar Nijar, 'yan kasar sun byyana ra'ayoyinsu mabambanta dangane da hukuncin kotun ECOWAS da ta kori karar da gwamnatin mulkin sojin kasar.

A Nijar din masana da ma 'yan kasar na tsokaci dangane da matakin da gwamnatin mulkin soji ta dauka na soke kwantaragin sayar da kamfanin sarrafa ruwan sha SEEN, tare da mayar da shi mallakarta.

Kungiyoyin agaji sun bayyana tagayyarar al'umma da ke faruwa a Sudan a matsayin babban rikici na wannan zamani da aka manta da shi. Mutane kimanin miliyan 24 ne dai ke bukatar agajin gaggawa na ceton rai.

A daidai lokacin da dakarun Isra'ila ke ikirarin yi wa shugaban Hamas Yahya Sinwar kofar rago a Khan Yunus da s**a yi wa kawanya, ana nuna fargabar abin da zai je ya komo idan har s**a yi nasarar kashe shi.

07/12/2023

Bana ma k**ar kowace shekara, an kaddamar da alawar Kirsimeti da tsohuwar ma’aikaciyar Sashen Hausa Edda Görke ta bar wasiyyar a ci gaba da yi yadda ta saba lokacin da take raye.

Bikin ya samu halartar Editar DW a Washington na Amurka, Ines Pohl da tsohon shugaban Sashen Hausa Malam Thomas Mösch da Shugaban sashen na yanzu Mohammad Nasir Awal da mataimakansa Hilke Fischer da Zainab Mohammed Abubakar da kuma sauran ma’aikata.

Adresse

Bonn
53113

Benachrichtigungen

Lassen Sie sich von uns eine E-Mail senden und seien Sie der erste der Neuigkeiten und Aktionen von DW Hausa erfährt. Ihre E-Mail-Adresse wird nicht für andere Zwecke verwendet und Sie können sich jederzeit abmelden.

Service Kontaktieren

Nachricht an DW Hausa senden:

Videos

Teilen

Our Story

Deutsche Welle, tashar da ke watsa shirye-shiryenta zuwa ƙetare, tana gabatar da labarai da rahotanni ta yanar-gizo da rediyo domin baiyanar da yadda ƙasashen Turai suke kallon al'amura ga masu sauraro a ko'ina cikin duniya. Burinmu shi ne: "Mu ƙarfafa fahimtar yadda Jamus take a matsayin 'yantacciyar ƙasa da tushenta yake tare da al'adun Turai, kuma a matsayinta na ƙasa mai matsakaicin ra'ayi, ta demokradiyya, mai bin dokokin tsarin mulki da shari'a. Shirye-shiryen DW suna isa ga masu sauraro da masu kallo miliyan 86 a ko'ina cikin duniya. Legal notice: http://bit.ly/dwlegalnotice


Andere Rundfunk & Medienproduktion in Bonn

Alles Anzeigen