WIGAN F.C BAURE

  • Home
  • WIGAN F.C BAURE

WIGAN F.C BAURE Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from WIGAN F.C BAURE, Newspaper, .

12/06/2017

Gwamnan jihar Kaduna da ke
arewacin Najeriya Mallam Nasir
Ahmad El-Rufai ya ce
gwamnatinsa ta soke dagatai da
masu unguwanni 390 da aka
nada a shekarar 2001. Wata sanarwar da ofishin gwaman
ya wallafa a Twitter ta ce an dauki
matakin ne domin rage nauyin da
kirkirar masarautun dagatan ta yi
a kan asusun kananan hukumomin
jihar. A cewarsa, "Yin garanbawul ga
gundumomi da kauyukan zai bai
wa kananan hukumomi damar
gudanar da manyan ayyuka da ci
gaban al'umma". Gwamna El-Rufai ya kara da cewa
yanzu gwamnatinsa ta dawo da
tsarin da aka sani gabanin 2011 na
dagatai 77 da masu unguwa 1,429. An sako mutanen da aka yi
garkuwa da su a Kaduna Ya ce sun dauki matakin ne bayan
da s**a tuntubi majalisar sarakuna
ta jihar, wacce ta bayar da hoton
bayanta. "Kirkirar mazabu 313 da aka yi
daga shekarar 2001 ta kara yawan
dagatai zuwa 390, wanda kuma
idan aka hada da ma'aikatansu sun
zama 2700 kuma kananan
hukumomi ne ke biyansu albashi", in ji Gwamna El-Rufai. Ya yi kira ga al'umar jihar su goyi
bayan matakin da ya dauka saboda
hakan zai inganta ayyukan da
kananan hukumomi ke gudanarwa. A cewarsa, "Kamar yadda muka sha
fada a baya, an zabi wannan
gwamnati ne domin ta dauki
matakai masu tsauri amma masu
muhimmanci, wadanda za su rage
barnar kudi sai dai za su inganta yadda ake gudanar da ayyuka da
mulki a kowanne mataki".

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when WIGAN F.C BAURE posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share