13/11/2022
ALLAH YAKARA MANA ALBARKAN MAHAIFIYA
Wata Rana Wani Saurayi Suna Zaune Da Mahaifiyarsa A Tsakar Gida Sai Wani Tsuntsu Ya Sauka Akan Taga,
Sai Uwar Ta Tambaye Shi Miye Wancan?
Sai Saurayin Yace Mata Tsuntsu Ne, Da Aka
Jima Sai Ta Sake Tambayarsa Miye Wancan?
Sai Saurayin Yace
Yanzun Nan Fa Kika Tambaye Ni Nace Miki Tsuntsu Ne.
Bayan Wani Ɗan Lokaci Sai Ta Kara Tambayarsa Menene Wancan??
Kawai Sai Saurayin Nan Ya Hauta Da Faɗa, "Kin Tambaye Ni Nace Miki Tsuntsu Ne Kin Sake Tambaya Ta Nace Tsuntsu Ne, Wallahi Idan Kika Sake Tambaya Ta Ba Zan Amsa Ba.
Sai Tsohuwar Nan Ta Fashe Da Kuka
Mai Tsanani Da Kyar Dai Ya Rarrashe Ta,
Shi Ne Take Fada Masa Cewa, Ka Ga Wannan Tsuntsun Da Kake Gani, Ya Taɓa Sauka Akan Wannan Tagar, A Lokacin Kana Yaro Kuma Sai Da Kayi Min Wannan Tambayar Da Nayi Maka Yanzu Sau 27 Kuma Duk Saida Na Amsa Maka Ban Gaji Ba,
Amma Kai Yau Gashi Sau Uku Kawai Na Tambaye Ka Amma Har Ka Ƙosa.
Mu Duba Irin Yanda Iyayenmu Suke Fama Da Mu Tun Muna Yara Qanana,
Idan Bamu Lafiya Ba Su Iya Yin Barci,
Su Sanya Kayan Su Na Ado Mu Fitsare Da Kasaye Masu Ba Tare Da Sun Fasa Daukar Mu Ba
Ya Allah Ka Bamu Juriya Da Hakuri Akan Iyayen Mu Kuma Ka Raba Mu Da Su Lafiya