07/12/2023
Girls Child and Orphans Initiative Foundation Ta Koya Ma Dalibai Mata Sama da (60 ) Sana'oi kala Uku Kyau ta.
Shugabar Foundation Dr. Amina Saleh Mande(PT) ta yi kira ga Dalibai da su mai da hankali wajen karatun su da kuma koyan Sana'oin hannu domin dogoro da kawun su. Tace gwamnati ba za ba iya ba kowa aiki ba, amma idan s**a dage s**a koyi sana'a za su zama ma su samar da aiki yi da koma samar ma gwamnati kudin shiga ta hanyar biyan haraji domin ayyukan gina kasa. Sannan ta Kara da cewa Sana'oin hannu suna taimaka wa wajen rage ayyukan ta'addanci saboda rashin ayyukan yi suna da ga cikin abubuwan da hadasa ta'addanci.
Ana shi jawabin Babban Bako Mal. Abubakar Umar Principal Na Community Day Secondary Dandume Ya kira da Dalibai su maida hankali domin koyan wannan Sana'oi saboda yanzu maza je gajiya da su ke da yawan rako. Sannan ya yi jinjina ga Foundation Ta Girls Child And Orphans Initiative Foundation.
Ana shi jawabin Shugaban Zama Mal. Shamsudden Ja'afar Ibrahim Jiruwa principal Govt Day Pilot Sec School Dandume wanda ya wakilci Hakimi Dandume Katikan Katsina Alh. Ja'afaru Ibrahim, ya yi godiya ga wannan foundation din, sannan ya ce masaurata a shirye ta ke wajen ba da gudunmuwa wajen ayyukan da za su kawo cigaba a wannan gari da jahar katsina baki daya, sannan ya yi addua Allah ya sa a yi taro lafiya a kuma gama lafiya.
Sana'oin da aka Koyar su ne; Sabulun Karas, Sabulun Ele (Medicate Soap) da man kitso mai maganin amosani da cututtukan fata. Wadda ta Koyar da Sana'oin ita ce Malama Nafisa Abubakar wadda aka fi Sani da Marnaf Abubakar mai kamfanin Marnaf Global DIY.
Taron ya guduna a GDPSS Dandume ranar 06/12/2023