04/03/2024
KAJI TSORON ALLAH A CIKIN ABIN DA ZA KA TURAWA MUTANE.
-
"Kaji tsoron Allah a cikin dukkanin abin da za ka turawa mutane a social media ko kuma za ka faɗa musu a zahirance, kada kayi abu don ka burge, kada kayi ƙarya don ka sami wata ƴar ɗaukakar duniya ko tarin wasu ƴan tsirarun mabiya, haƙiƙa duk wanda yayi koyi dakai cikin abin da ka koyar da ƙarya, to haƙiƙa kaima kana da gwaggwaɓan ladan da zai yi maka matuƙar nauyi wajen ɗaukarsa a ranar ƙiyamah"
-
"Kada ka sake son zuciya yasa ka dinga yin da'awa cikin ɓata ko neman ɗaukaka, kada ka bari shaiɗan yasa ka dinga aikata abin da za ka kwashi alhakin jama'a a gadon bayanka a ranar ƙiyamah, haƙiƙa za ka tozarta a filin hisabi"
-
Manzon Allah ﷺ, ya ce: "Duk wanda yayi kira izuwa ga ɓata/ƙarya, to haƙiƙa ya kasance yana da zunubi irin zunubin wanda ya bi shi yayi koyi dashi, ba tare da an rage na daga zunubin su da komai ba" Sahih Muslim (2674).
-
Telegram channel
https://t.me/TAFARKINRAYUWARMUSULMI