08/11/2024
GASKIYAR LAMARI AKAN TIRKA TIRKAR SHUGABANCIN KARAMAR HUKUMAR KUMBOTSO.
Daga: Musa Ibrahim Danbare
A farko Jagora Kwankwaso ya bawa Yantakara na Karamar Hukumar Kumbotso dama su fitar da mutum daya a cikinsu. Bayan sun shiga daki s**a fito s**a shaida masa cewa sun gaza fitar da mutum daya a cikin su, Mutum 26 cikin 30 s**a ce masa sun yadda ya shi da kansa ya zabi dantakara a cikin su, amma basu yadda ya bawa jagororin Karamar Hukumar dama su zaba ba, yantakara sun kara da cewa already jagorori suna da yantakarar su saboda haka idan ya basu dama s**a zaba baza suyi adalci ba.
Duk da wannan roko da yan takara s**ayi amma Madugu ya bawa Jagoranci dama s**a zaba. Bayan zaben dukkanin yantakara s**a hakura s**a bi hardworker.
Tun a ranar da aka ce an ayyanna shi mutane da yawa s**a rubuta petition (korafin cewa yana da matsalar takardar makaranta bai kammala sakandare ba).
Wannan shi yaja hankalin kwamitin fitar da yan takara na jiha aka ya yi bincike wanda a karshe bincike ya zama gaske cewa Hardwoker bai Kammala makarantar Gundutse Secondary School ba k**ar yadda ya rubuta da hannunsa a jikin form din screening na takara.
Wannan dalilin yasa Madugu yace da yantakara da Jagororin Karamar Hukumar su dawo a sake zabar wani , bayan doguwar muhawara Jagoranci na Karamar Hukumar s**a zabo mutum 4 wanda aciki aka cimma matsaya akan Basaf.
A gidan Jagora Kwankwaso shi Ali Musa Hardworker da kansa ya yarda yana da matsalar takarda kuma ya ce da bakin sa ya karbi Hukuncin da aka yanke. Inda madugu yayi masa alkawarin zai sa Gwamna ya yi masa appointment.
Tun daga ranar da aka yi abin ake neman hardworker a waya amma yaki samùwa anje har gidansa amma an kasa samunsa. Kwatsam ba zato ba tsammani sai ji akai ya kai kara kotu wai shine dantakara. Kuma Ana zargin wani Danmajalisar Jiha da na tarayya ne s**a hada kai da wani tsohon Chairman da kuma jigo a gwamnati wajen zugawa da tsayawa shi Ali Musa yakai kara.
Abin da mutane ya k**ata su sani shine:
Shi fa hardworker babu inda Jam'iyya tace shine Dantakara Bashi da wata shaida a hukumance da tace shine dantakara. Kuma ikirarin da yake an canza sunan sa ba haka bane, tunda dama can ba akai sunansa KANSIEC ba, Sunan Abdullahi Ghali Basaf kawai Jam'iyya takai, kuma Basaf kadai Jam'iyya ta bawa Nomination Form. Basaf Gwamna ya bawa tuta, Sannan Basaf ne yayi Screening a KANSIEC kuma sunan sa KANSIEC s**a fitar a matsayin Dantakara kuma shi s**a sanar a matsayin wanda yaci zabe.
To Don Allah bisa Adalci ta ina Hardworker ya zama Shugaban Karamar Hukuma?
Kuma ko a shari'ance, idan Jam'iyya tace wane shine Dantakara to dole shine Dantakara, anyi case kuma anyi hukunci irin wannan akan Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma Ahmed Lawal tsohon Shugaban Majalisar Dattawa. In da Kotu tace Jam'iyya ce take da hurumin tsaida Dantakara, saboda haka Jam'iyya tace Basaf ne Dantakar ta.