Kaduna Post

Kaduna Post Don Kawo Muku Labarai Da Dumi Dumin Su.

KADUNA
15/10/2024

KADUNA

Na samu tarba abinda ke sunan tarba daga maimartaba sarkin Agadez Alh ummaru Ibrahim ummaruIdan baku mantaba jiya sati d...
24/01/2024

Na samu tarba abinda ke sunan tarba daga maimartaba sarkin Agadez Alh ummaru Ibrahim ummaru

Idan baku mantaba jiya sati daya kenan da na bar garin Abuja kai tsaye zuwa Agadez domin ziyaratan sarkin Agadez
Cikin yardar Allah da ikon sa yau na isa gaban maimartaba sarkin Agadez kuma na samu tarba iya tarba kamar yadda labarin ziyarata ya rigani isowa wannan fada mai albarka
Sarki ya sakama dan larabawa Albarka an kuma ba dan labara daman zagayawa cikin aminchi
Fatan Allah ya kara iya mana da iyawarsa 🤲

Wannan rubutu a takaiche kenan

Ku kasanche tare dani domin ji da ganewa idanun ku

HOTO: Gwamna Uba sani na cigaba da zaman makoki a gidan Gwamnatin Jihar Kaduna.A yau ma Gwamna Uba Sani ya karbi bakunci...
10/12/2023

HOTO: Gwamna Uba sani na cigaba da zaman makoki a gidan Gwamnatin Jihar Kaduna.

A yau ma Gwamna Uba Sani ya karbi bakuncin tawagar majalisar dattawa karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibril a zauren taron gidan Gwamnatin Sir Kashim Ibrahim Kaduna. Tawagar ta hada da Sanata Lawal Adamu Usman mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya Ziyarar ta su Zuwa jihar Kaduna domin jajantawa kan aukuwar harin Bom na Tudun Biri wanda sojojin s**a yi amatsayin kuskure wanda ya yi sanadin asarar rayuka sama da mutun 120 da jikkata wasu wanda yanzu haka s**a karbar magani a asibiti.

DA DUMI-DUMI: Mataimakin Shugaban kasa da Ministan tsaro da Malamai da Sarakuna sun shiga ganawa kan kis*an gilla da soj...
07/12/2023

DA DUMI-DUMI: Mataimakin Shugaban kasa da Ministan tsaro da Malamai da Sarakuna sun shiga ganawa kan kis*an gilla da sojoji s**a yiwa jama'a a Kaduna

Kashim Shettima na ganawa da Shuwagabannin Addini da Sarakunan Gargajiya a Kaduna domin tausasa su game da ki*san kiyashi da aka yiwa jama'a a Tudun Biri

Cikin jiga-jigan dake tare da Shettima akawi Gwamnan Kaduna Uba Sani, Kakakin majalisar Dokoki ta Najeriya, Abbas Tajuddeen, Babban Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar da kuma shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Dubban masu zanga-zanga sun fantsama titunan Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya, a wani mataki na nuna bacin rai kan ...
07/12/2023

Dubban masu zanga-zanga sun fantsama titunan Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya, a wani mataki na nuna bacin rai kan kashe sama da mutane 120 da ke bikin maulidi Manzon Allah SAW a wani kauye da ke Tundun Biri na karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Masu zanga-zangar suna kira da a tsige ministocin tsaro tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

Ga wasu hotunan zanga-zangar da wakilinmu na Abuja Mohammed Kabir Yusuf ya aiko mana.

DW HAUSA

Da dumi’dumi: Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya sauka a kaduna domin ta’aziyyar ‘yan Maulidi da sojojin s**a k...
07/12/2023

Da dumi’dumi: Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya sauka a kaduna domin ta’aziyyar ‘yan Maulidi da sojojin s**a kashe a jihar.

DA DUMI-DUMI| Bangarori Uku Shi'a, Izala da Darika sun hada kansu a Kano, Akan harin 'Tudun Biri'.Bangaren Yan Shi'a Alm...
07/12/2023

DA DUMI-DUMI| Bangarori Uku Shi'a, Izala da Darika sun hada kansu a Kano, Akan harin 'Tudun Biri'.

Bangaren Yan Shi'a Almajiran Sheikh Zakzaky da Izala da Yan Darika Sun Kira Taron Manema Labarai Akan Harin Tudun Biri KADUNA.

Lokacin Taron Sun Bayyanawa Manema Labarai Cewa Al'ummar Musulmi Ba Zasu Yarda Da Wannan Harin Ba, Kuma Suna Kira a Dauki Mataki Da Gaggawa.

HOTO: Gwamnatin jihar Kaduna ta fara kai kayan agajin gaggawa domin rabawa iyalan wadanda harin bom na sojoji ya rutsa d...
06/12/2023

HOTO: Gwamnatin jihar Kaduna ta fara kai kayan agajin gaggawa domin rabawa iyalan wadanda harin bom na sojoji ya rutsa dasu a Tudun Biri.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna ta kai kashin farko na kayan agajin da s**a hada da abinci, man girki, katifu da barguna da dai sauransu.

A cewar babbar sakatariyar hukumar ta SEMA, Dr Hayatu Mazadu na ci gaba da gudanar da karin kayan bukata ne domin kai daukin gaggawa ga al’ummomin da abin ya shafa.

Masu Maulidi ba Shahada su ka yi ba saboda sun mutu a wajen aikata saɓon Allah ne bidi'a.  - “Inji Dr. Idris Dutsen Tans...
06/12/2023

Masu Maulidi ba Shahada su ka yi ba saboda sun mutu a wajen aikata saɓon Allah ne bidi'a. - “Inji Dr. Idris Dutsen Tanshi

Zazzagawa baku san Tsoro ba..Zanga-zangar Lumana na Gudanawa a Zaria..Ko mu Rayu ko mu mutu sai anyi Adalci...We Moveeee...
06/12/2023

Zazzagawa baku san Tsoro ba..

Zanga-zangar Lumana na Gudanawa a Zaria..

Ko mu Rayu ko mu mutu sai anyi Adalci...

We Moveeeee.


Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja, ya je ta'aziya kan harin bam da Rundunar Sojin Ƙas...
05/12/2023

Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja, ya je ta'aziya kan harin bam da Rundunar Sojin Ƙasar ta ce ta kai bisa 'kuskure' a jihar Kaduna.

📸 - Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya

Yanzu Yanzu: Bam Ya Tashi dlDa Masu Mauludi A KadunaRahotannin da jaridar Daily Trust ta samu sun nuna cewa ana kyautata...
04/12/2023

Yanzu Yanzu: Bam Ya Tashi dlDa Masu Mauludi A Kaduna

Rahotannin da jaridar Daily Trust ta samu sun nuna cewa ana kyautata zaton mutane da yawa sun mutu bayan da ake zargin cewa wani jirgin sojin saman Nijeriya ya jefa bam ga wasu mutane da ke bikin Mauludi a kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Duk da dai babu cikakken bayanin yadda lamarin ya faru, amma dai wasu rahotanni sun ce mutane kusan 30 sun mutu bayan jefa bam din da misalin karfe 9 na dare.

Mazauna kauyen sun sanar cewa jirgin ya yi ruwan bama-baman ne a lokacin da mutanen kauyen s**a tattaru domin su gudanar da bikin murnar haihuwar fiyayyen halitta, manzon tsira 'SAW'.

Ana dai fargabar ban gaba yawan wadanda s**a rasu su ya karu.

Ta bangaren gwamnati, Samuel Aruwan da ke kula da ma'aikatar tsaron cikin gida ta jihar Kaduna, ya ce za su yi taron manema labarai nan gaba.

A Jihar Kano Karamar Hukumar Kumbotso Jami'an Tsaron 'Yan Sanda Sunyi Nasarar Kame Barayin Magunan Bayin AllahKai Jama'a...
01/12/2023

A Jihar Kano Karamar Hukumar Kumbotso Jami'an Tsaron 'Yan Sanda Sunyi Nasarar Kame Barayin Magunan Bayin Allah

Kai Jama'a Yanzu Fisabilillahi Idan Banda Maita Irin Ta Wasu Mutanen Me Mutum Zai Ci a Jikin Mage/Kyanwa Tur

01/12/2023

Yada jama'a jahar Kaduna s**a yi murna samun nasara Mallam Uba Sani.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da Sarki Charles III gabanin taron sauyin yanayi na COP28 da aka buÉ—e yau a Dubai....
30/11/2023

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da Sarki Charles III gabanin taron sauyin yanayi na COP28 da aka buÉ—e yau a Dubai.

📸 BBC Hausa

Yan Keke Napep sun kulle Baban Hanya  ( Nnamdi Azikiwe Expressway bypass Kaduna ) musamman U/Muazu , Kabala West da kuma...
29/11/2023

Yan Keke Napep sun kulle Baban Hanya ( Nnamdi Azikiwe Expressway bypass Kaduna ) musamman U/Muazu , Kabala West da kuma Dutsenma Junction. Sakamakon aika aikan da yan sanda s**a yi.

Matafiya na cikin wani hali, ya kamata Gwamnati ta shigo cikin lamarin.

Allah Ya kyauta,

Bin Shehu dolene ne idan ba haka ba wallahi zaka wuta - Sheikh Tanimu Mairawani Zariya
16/11/2023

Bin Shehu dolene ne idan ba haka ba wallahi zaka wuta - Sheikh Tanimu Mairawani Zariya

'Yan Kannywood na shirin maka Abdallah Amdaz a kotu Kilu ta ja bau, a inda wasu jaruman Kannywood s**a yi barazanar maka...
16/11/2023

'Yan Kannywood na shirin maka Abdallah Amdaz a kotu

Kilu ta ja bau, a inda wasu jaruman Kannywood s**a yi barazanar maka Abdallah Amdaz a kotu kan bata musu suna, ko kuma ya yi wa duniya karin haske kan kalaman da ya yi a lokacin taron wasu 'yan Kannywood da hukumar Hisbah ta kira.

Me za ku ce?

Address


Telephone

08026873480

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kaduna Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share