07/05/2023
Yadda mata ke rasa budurcinsu a lokacin bukukuwan murna.
Kes ɗin da ake samu yanzu ya fara yawaita a ofishin mu na Hisba a yanzu shi ne a kan yadda mata suke rasa budurcinsu sakamakon wasu bukukuwa da ake gabatarwa lokacin murna. Mafi yawan ƴan mata a wajen bikin yawon sallah ne suke rasa budurcinsu.
A ya yi zantawar wakilin mu Mustapha Muhammad tare da Kwamandan Hisba na Unguwar gabas da kewaye Shaikh Abdullahi Usman ya yi mana bayanin yadda kesa-kesan da ya fara yawaita a ofisoshinsu sune yadda samari ke amfani da damar su a kan ƴan mata a lokacin bukukuwan Sallah ko na biki ko na suna su lalata wa yarinya budurcinta.
Ya ci gaba da cewa, mun samu wani kes daga cikin Garin Zariya yadda wata yarinya ta kai wa Saurayinta ziyarar barka da Sallah tare da ƙawarta zuwa ɗakin saurayin a ya yin yawon Sallah, shi kuma ya yi amfani da wannan damar, wannan abin takaici har ina.
Daga ƙarshe Kwamandan Hisban ya yi kira ga Iyaye ta hanyar basu shawara inda yake cewa, ya kamata Iyaye kusa ido a kan hakan, daga ƙarshe muna Addu'a a kan Allah ya shirya mana zuri'a.
-Cewar Kwamandan Hisba Shaikh Abdullahi Usman yankin Unguwar Gabas Sabon Garin.
Daga Mustapha Muhammad.