10/12/2024
Taron Wata-wata karo na 55 na kamfanin IBIS 📡
Taron Wata-wata karo na 55 na kamfanin IBIS 🏢
Shugaban Kamfanin IBIS kuma Babban Jami'in Gudanarwa na rukunin kamfanonin IBIS, Mallam Abdulhadi Ya’u Maikawo, ya jagoranci taron Wata-wata karo na 55 na kamfanin ta yanar gizo. 🌐 Taron ya mayar da hankali kan tattauna batutuwan da s**a shafi ci gaban kamfanin, warware matsaloli, kafa tsare-tsare, da tabbatar da adalci da hadin kai wajen gudanar da ayyukan kamfanin. 🤝
Yayin Jawabin Shugaban kamfanin ya jinjina wa Jami'an da suke nuna jajircewa wajen ganin an cimma burin kamfanin, tare da yin kira ga waɗanda ke nuna rashin himma da su gyara halayensu don samun ci gaba. 📈
Rahotanni daga Manyan Jami'ai: 📝
Wasu daga cikin Jami'ai sun gabatar da Rahotanni:
1. Babban Jami'in Gudanarwar Harkokin Kasuwanci (COO): Ya bayyana manyan nasarorin da aka samu, musamman a bangarorin Sewing Solution Store 🧵 da Global Harvest Trade 🌍. Ya bayyana cewa Batch "A" na Global Harvest Trade ya riga ya fara, yayin da ake ci gaba da shiri don ƙaddamar da sauran batches. 🚀
• Duk da matsalolin dake bijirowa yau da kullum waɗanda ake fuskanta, ya tabbatar da cewa suna iya ƙoƙarin su wajen magance su da yardar Allah. 🙏
2. Babban Jami'in Kudi (CFO): Ya gabatar da cikakken rahoto kan matsayin kuɗin kamfanin, tare da bayanin yadda ake raba hannun jarin. 💰 Haka kuma, ya bayyana kashi-kashi na hannun jari na kowane memba a cikin dukkan harkokin kamfanin.
• Dangane da Ci gaban Biyan Kuɗi: Ya bayyana karuwar kaso 36.8% na biyan kuɗaɗe da aka samu a watan Nuwamban nan na 2024, wanda ya nuna jajircewar membobin wajen tallafa wa harkar Global Harvest Trade wadda ake ciki. 📊
Dangane da ƙalubale kuwa: Ya nuna damuwa kan rashin biyan kuɗaɗe daga wasu membobi tsawon lokaci wanda hakan bai dace ba, wanda ya ce yana kawo cikas ga ci gaban kamfanin. ⚠️
3. Babban Jami'in Siyayyar Kaya (CPO): Bai samu Halarta ba, duk da cewa rahotonsa yana da matukar muhimmanci, musamman a wannan lokaci da ake siyan kayayyaki da yawa, bai halarci taron ba, saboda wasu dalilai. ⛔
Jawaban Sabbin Daraktocin Zartarwa: 🏅
Sabbin Daraktocin Zartarwa guda biyu da aka ba su sabbin mukamai sun nuna godiyarsu ga kamfanin bisa amincewa da su:
1. Daraktan Zartarwa na Zakka, Kula da Dokoki, da kuma Bunƙasa Taimakon Al’umma:
Daraktan ya yi alkawarin jajircewa wajen ciyar da kamfanin gaba. 🌱 Ya yi kira ga ci gaba da yi masa addu’o’i, tare da neman a dawo da tarurrukan horaswa ta yanar gizo da ake yi a baya don koyarwa da horarwa ga Jami'ai don cin nasarar kamfanin. 🎓
2. Daraktan Zartarwa na Harkokin Ƙasashe da Ƙulla Hulɗa:
Daraktan ya bayyana godiyarsa bisa ga amintakar da kamfani yayi dashi kan wannan matsayi tare da yin alkawarin wuce tsammani wajen gudanar da ayyukansa. 💼 Ya ce ƙofarsa a bude take don karɓar shawara daga membobi, tare da yin kira ga yi masa addu’o’i domin samun nasararsa. 🙌
Jawaban Shugaban Kamfani: 🗣️
Shugaban kamfanin, Mallam Abdulhadi Ya’u Maikawo, ya jaddada burin IBIS na zama babban kamfani a Najeriya da ma sauran sassan nahiyar Afirka. 🌟 Ya yi kira ga membobi da su kara zage damtse wajen hada kai da bayar da gudummawa don cimma wannan buri. 💪
Kwamitici da Aka Kafa Domin tabbatar da aiki tare da Inganta Gudanarwa:
Shugaban ya bayyana wasu kwamitoci da aka kafa domin tabbatar da adalci da hadin kai da kuma aiki da tare, ciki har da:
• Kwamitin Bada Shawarwari kan Haɗin-gwiwa na IBIS 🧑💼
• Kwamitin Warware Rikice-Rikice da Tabbatar da Bin Doka da oda na IBIS ⚖️
• Kwamitocin wurin-gadi kan Shirin AGM na 7 da na 8 🗓️
• Kwamitin wurin-gadi kan Inganta Biyan kuɗaɗe da Magance Matsalolin Biyan kuɗaɗen ✅
Ya kuma yaba dangane da jajircewar Babban Jami'in Gudanarwar Harkokin Kasuwanci da ayyukan yau da kullum (COO) da kuma Babban Jami'in Kudi (CFO), tare da bayyana shirin aiwatar da wasu manufofi masu kyau don ƙarfafawa ma’aikatan kamfanin, musamman masu Jajurcewa. 🎯
Nuna Damuwa daga Babban Sakatare:
Babban Sakataren kamfanin, Mallam Abubakar Yusuf (Maru), ya nuna damuwarsa kan rashin halartar tarurruka daga wasu membobi ba tare da wasu ƙwararan Dalilai ba, da kuma wasu da ke shiga taron amma ba sa bayar da gudummawa a yayin tattaunawa. 🤔
Dawo da Tarurrukan Horarwa ga Jami'an Kamfani: 📘
Shugaban kamfanin ya tabbatar da cewa za a dawo da tarurruka da horarwa da aka saba yi can baya don bunkasa basirar ma’aikatan kamfanin. 🌟
Sa Hannu:
Abubakar Yusuf (Maru) ✍️
Babban Sakatare,
IBIS Company Ltd