17/07/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!
Cikin hukuncin Allah yau Mamarmu, Hajiya Zainab B Takko ta samu rakiyar dumbin masoya da magoya baya domin zuwa siyan takardan nagani, ina so (Declaration of Interest form).
Wannan shine yake nuna tabbacin Mama, Haj Zainab Baban takko zata shiga takaran kujeran shugaban karamar hukumar Bauchi wanda za ayi nan ba da jumawa, inn shaa Allahu.
Tabbas wannan rana, ta zamo rana mai cike da tarihi da alkairori, duba da yanda mutane sukayi chin-chirindo duk da wannan lamari yazo a kurarren lokaci.
Da wannan soyayya da kuma wannan rana ta Ashura muke tawassuli, tare da kamun kafa da alfarman annabin rahama, Allah Ubangiji ya tabbatar mana da dukkan alkairorinsa dake cikin wannan tafiya ya kuma karemu daga dukkan sharruka dake ciki.
Muna godiya wa mai girman gwamna Senator Bala Abdulkadir Mohammed da ya bamu dama a lokuta mabambanta. Muna kuma masu tabbatar masa da jajircewa da biyayya a koda yaushe.
A karshe muna masu mika sakon ban gajiya da godiya wa daukacin al'ummar karamar hukumar Bauchi, da fatan kowa ya koma gida lafiya.
✍️ ZBTmediateam 📸
16th July, 2024