04/02/2024
ZIYARA.
Alhamdulillah! Wannan Kungiya ta Bauchi Orphans Support Association (BOSA), ta ziyarci asibitin MDGs dake Inkil, Gombe Road, Bauchi, jahar Bauchi.
Makasudin wannan ziyara dai shi ne, domin gaida marassa lafiyan da suke kwance a asibitin, tare da fadakar da su akan Jarrabawan da Allah Ya dora masu na rashin lafiya.
Shugaban kungiyar Malam Isma'il Hashim (Ibn Hashim), yace: wannan aiki na ziyartar marassa lafiya a asibiti, daya ne cikin manufofin wannan kungiya. Yace: kuma haka zamu ci gaba da fafatawa har karshen rayuwar mu da ikon Allah.
Yace: burin mu shi ne: 'ya'yan mu su gaji wannan aiki da mukeyi.
Sannan yayi kira ga kungiyoyi da kuma dai-daikun mutani da su ringa sauke haqqin da yake kan su musamman abinda ya shafi gaida maras lafiya a gida ko asibiti. Yace aiki ne da mutani suke ganin yana da wahala amma da zaran an fara yana da sauki sosai, domin kuwa lamari ne na had'in kai, idan har jama'a zasu had'a kan su, to lallai zasu samu sauki cikin gudanar da aikin.
Shugaban ya bayyana farin cikin sa ganin yanda akayi ziyarar cikin annashuwa da bada cikekken goyon baya wurin halartar asibitin.
Daga karshe maziyartan sunyi Addu'o'in alkhairi wa marassa lafiyan, tare da jinjina ta musamman ga ma'aikatan asibitin.
Zakariyya Yunusa Madaki
Secretary General ✍️
Bauchi Orphans Support Association.
04/02/2024.