18/01/2024
Ka je Mahaifiyarka Ta Yi Maka Adduโa:
Al-Imam Sulaim dan Ayyub Ar-Razi, daya daga cikin manyan malaman Mazhabar Shafiโiyya (Ya rasu a shekara ta 447 BH). Yana cewa:
โLokacin da nake yaro karami dan shekar goma a garinmu (Ar-Rayy) (Cikin kasar Iran a yanzu), sai wani bakon malami ya ziyarci garin yana koya wa yara karatun Alkurโani. Sai ya ce min: โMatso kai ma ka karantaโ. Sai matsa, na yi ta kokarin in karanta Fatiha amma na kasa, domin harshena ya yi nauyi sosai. Sai ya ce min: โShin kana da mahaifiya a raye?โ Sai na ce masa, e, ina da ita. Sai ya ce: โKa je wurinta ta yi maka adduโa Allah ya arzutaka da karatun Alkuraโni da na ilimiโ. Sai na ce, to. Sai na koma gida na roke ta ta yi mini adduโa, sai ta yi min.
Sai ga shi na girma har na tafi garin Bagdaza na yi karatun harshen Larbaci da na Fikihu, sannan na dawo garinmu Ar-Rayy.
Wata rana ina zaune a masallacin Jumaโa, muna karanta littafin โMuhktasarโ na Muzani, sai ga malamin nan mai koyar da karatun Alkurโani ya shigo masallacin, ya nufo inda muke ya yi mana sallama, muka amsa masa, amma bai gane ni ko wane ne ba, don ya manta abin da ya faru a can baya da jimawa. Ya ga muna karatun Mukhtasar na Muzani, shi kuma ga shi ba zai iya karantawa ba, sai ya tambaye ni cewa yaushe ne mutum zai iya koyon irin wannan ilimin? Sai na ji kamar in ce masa idan mahaifiyarsa tana nan raye ya je ta yi masa adduโa, to amma sai na ji kunya na kasa fada masa.โ
Kyakkyawar adduโa ta iyaye tana da albarka matuka.
Wannan mashahurin malami Al-Imam Sulaimu ya fara neman ilimi ne bayan ya haura shekara arbaiโin a duniya. Amma ya zama daya daga cikin hamshakan malamai a zamaninsa.
[Dubi, Az-Zahabi, Siyar Al-Aโlam, Juziโi na 3, Shafi na 18-19].
โ๐ป Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo