30/09/2024
MAƘIYA SUN YI ABIN DA ZA SU IYA YI NA KARSHE!
- Inji Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky a yayin isar da ta’aziyyarsa na rashin Sayd Nas* ral-lah.
Daga Cibiyar Wallafa
Da yake gabatar da ta’aziyya, ta hanyar wani bidiyo mai mintoci 9:34 da shafin ofishinsa ya wallafa a ranar Lahadi 29/9/2024, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana ki*san Sayd Nas* ral-lah a matsayin ki*san mugunta da kiyayya, wanda ba a ga irinshi a kurkusa a wannan lokacin namu ba.
Yace: “Duk wani abu da za ku iya yi ba za ku yi wanda ya wuce shi ba. Kuma insha Allahu karshenku ne ya zo, insha Allahul Azeem da wadannan jinane masu tsarki ne za a kai ga nasara.”
Jagora ya bayyana cewa: “Sayyid yana nan raye, kuma ya dinga farautanku kenan, kuma farautan nan har izuwa nasara. Insha Allahu kuma kun yi abin da za ku iya yi na karshe.”
Yace: “Tabbas mun koka, kuma mun ji zafi, kuma mun girgiza, kuma har yanzu ba mu tashi daga wannan girgiza da muke ciki ba, amma kuma a lokaci guda mun san cewa Shahada ya yi, kuma wadanda suka yi shahada tare da shi Shahada suka yi. Mun san kuma wannan kyakkyawan karshe ne.
“Dama muna gidan gwaji ne, ba a kaddara wa mutum dauwama ba, gwaji ne. Kuma Alhamdulillah Sayyid tun kafin a daura mashi alhakin jago’rancin Mu* kawaman Hiz* bvl-lah, - muna iya cewa kusan shekaru 40 a kidayar Qamariyya, - dare da rana, wannan bawan Allah bai huta ba, aiki yake yi, ba ji ba gani. Yakan je har fagen fama a fafata da shi ya dawo.
“Haka nan tun wannan shekarun suna ta bidansa ne, amma Allah Ta’ala ya hana musu (cimma)shi, Ya katange shi, Ya kare shi, har sai da ya i-da aikin da Allah Ta’ala Ya bashi daman yi, har kuma lokacin da yanzu Allah Ya kaddara mashi ya huta.” Inji Jagora.
Shaikh Zakzaky ya kara da cewa: “(makiya) sun yi murnar abin da suka yi, har da raye-raye da bukukuwa, wanda ya yi kama da Shahadar Abi Abdullahil Husain (AS), wanda makiya shi ma suka yi murna. Shammacin makiya yana daga abin da yake girmama lada, da kuma kambama al’amari. Kuma kamar yadda makiya suka yi shammati a wajen kashe Imam Husain (AS), ba da jimawa ba farin cikinsu ya koma bakin ciki, to su ma wannan haka muke musu fata, ba da jimawa ba farin cikinsu zai koma bakin ciki.”
Tun da farko, sai da Jagora ya isar da ta’aziyyarsa ga Sahibul Asr (AS) da Sayyidul Qa’id (H) da daukacin ‘yan Mu*kawama na Lebanon, Palasdin, Syria, Iraq, da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma na Yemen akan abin da ya kira shi da babban rashi. Tare da yin addu’ar Allah Ta’ala ya amshi shahadarsa, ya riskar da shi da Shuhadan Karbala tare da Sayyidus Shuhada Abi Abdullahil Husain (AS) kakansa.
Ya kuma jajantawa dukkan al’ummar da wannan abu ya shafa. Yace: “Muna jajantawa dukkan al’ummar da wannan abu ya shafa, ba kawai al’ummar Lub-nan da Palas*dinu da ‘yan Mu*kawama ba, har ma da dukkan ‘yantattun mutanen duniya bakidaya, domin kuwa al’amarin kwatan ‘yanci abu ne da kowannenmu yake hankoro.” Ya jaddada cewa: “wannan al’amari zai kawo karshe. Tabbas mu alkawari ne a gare mu, cewa akwai mafita tana nan tafe. Muna fatan Allah Ta’ala ya gaggauta bayyanan Sahibul Asr Waz Zaman (ALF).”
Ya kuma isar da jajensa ga musamman makusantan Shahid. “Muna jajantawa ‘khususan’ iyalan Sayyid na kusa, da kuma yi musu albishir da cewa, karshe ne wanda yake mai kyau, bamu ga wani abu ba illa mai kyau. Wannan tafarki ne na gidanku, tafarkin Abi Abdullahil Husain ne, haka nan abin ya gada.”
Sannan ya karkare da kira ga sauran al’umma, da cewa: “kun ga yadda duniya ta dare biyu; tsakanin azzalumai da wanda ake zalunta, yanzu ku sai ku dauka ma kanku wanda kuka gani. Za ku kasance da azzalumai ne, wanda ku ma ana zaluntarku? Ko za ku kasance da masu gogormaya domin kwatan ‘yancin wanda aka zalunta?” Inda ya karkare da albishir din cewa: “Insha Allahul Azeem kuma azzalumai ba za su taba nasara ba!”
— Cibiyar Wallafa