01/02/2022
"Zan Dau Matakin Shari'a Akan Dan Maifadan Akko Idan Yaki Takarar Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Akko
Daga. Asma'u Muhammad Bala
Matashi mai fafutuka, marubuci kuma Mai Tasiri A kafafen Watsa Labarai
Muhammad Chigari Kumo, ya sha alwashin ja da Alh. Dokta Usman Ardo Kumo (Dan Mai-Fadan Akko) a gaban kotu idan ya ki amincewa da kirar mutanen mazabarsa da s**a kira shi da ya nemi kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Akko A majalisar Tarayya
Cigari ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kumo.
Ya ce dalilin da ya sa ya tsaya shi ne dimbin ayyukan da Dakta Ardo ya aiwatar wadanda s**a taimaka matuka gaya wajen daukaka al’ummarsa.
“Dukkanmu shaidu ne kan yadda wannan mutumin ya dauki nauyin jinyar marasa lafiyan ido daruruwan mutanen da ke fama da matsalar ido, s**a Amfana ya sayi mashaya mai suna 'V-Mark' s**a mayar da ita makaranta, sun gina gadoji, masallatai da kuma daidaita kudaden magani ga marasa galihu, suna ba da tallafin karatu ga ɗalibai marasa galihu da sauran abubuwa masu kyau a wannan lokacin. ko kuma sarari bazai bar ni in ambata ba" Cigari yace.
“Ya kamata a lura cewa Dan Mai-Fadan Akko ya yi duk wadannan abubuwa ba tare da rike wani mukami na gwamnati ko na siyasa ba, to me kuke tsammani idan za a ba shi damar zama mamba mai wakiltar mutanensa nagari?
Da aka tambaye shi game da jam'iyyar zai so Dr Usman Ardo ya tsaya takara. Kumo ya ce, “ba wai jam’iyya ba ce, mutum ne da mutuntaka ne, cancanta, kwarjini da sanya mutane a zuciya.
"Wace jam'iyyar zai dace da shi shine ra'ayinsa. Amma rokonmu shi ne ya shiga takara".
Ya kake gani in Ardo Kumo ya ki amincewa da rokon mutane, Muhammad Cigari ya ce "Ina da kwarin gwiwa cewa ba zai yi watsi da wadannan kararrakin ba. Wannan mutumin ba zai taba yasar da jama'arsa ba, yana kuma kawo musu dauki a lokacin da suke bukata".
Cigari ya yi kira ga kowa da kowa, musamman matasa da su guji tashin hankali, su rungumi siyasar zaman lafiya da Dan Mai-Fadan Akko a koda yau