10/01/2024
Wani Matashi A Jihar Gombe Ya Kirikiri Injin Bayin Ruwa Wanda Baya Amfani Da Man Fetur Ko Hasken Rana
Daga Muhammad Kwairi Waziri
Matashin mai suna Malik Muhammad Kumo, ɗan asalin jihar Gombe ya zabi samar da injin bayin ne domin hucewa al'ummar yankunan karkara takaicin tsadar man fetur da kuma tsadar inji mai amfani da hasken rana.
Malik Muhammad dai ya hada irin wannan inji da ke samar da ruwa ta hanyar amfani da batirin mota da wasu injuna da koyel, inji yana tashi da key kamar yadda ake tada mota, yana diri yana chajin batir har lokacin da ka gaji ka kashe shi, yana awa a shirin da huɗu bai mutu ba, a jikin sa harda wajen saka chaji na waya.
Wannan mataki nasa ya sa mutane da dama a yankunan karkara sha'awar noman rani, wanda ya zama sana'a a wajen mutane.
A cewar Malik Muhammad Kumo, abun alfahari ne a gare shi, wanda hakan wata babbar nasara ce da yake alfahari da ita ta sanadin mahaifinsa.
Sai dai duk da cewa wannan matashin ya ce ya samu nasarori masu yawa a baya a irin wannan fannin kirkire-kirkire, sai dai kuma akwai tarin kalubale da yake fuskanta musamman rashin kuɗi, wanda yasa ya share tsawon wata uku yana fama wajen ganin ya haɗa wannan injin a cewar sa.
Daga karshe dai yayi kira ga matasa da su yi amfani da basirar da suke da ita wajen dogoro da kansu ba tare da sai gomnati ta basu aiki ba.
Mai Buƙata Ko Ƙarin Bayani Yayi Mana Magana Ta Inbox.
07037611969