Muryar Arewa News

  • Home
  • Muryar Arewa News

Muryar Arewa News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muryar Arewa News, Media/News Company, .

Ana fargabar mutane 30 sun rasa rayukansu sakamakon ruftawar ramin hakar ma'adinai a kauyen Galkogo da ke karamar hukuma...
04/06/2024

Ana fargabar mutane 30 sun rasa rayukansu sakamakon ruftawar ramin hakar ma'adinai a kauyen Galkogo da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Bayan kungiyar kwad**o ta janye yajin aikin sai Baba Ta Gani da ta tsunduma, Ko an dawo muku da wutar nefa yanzu a yanku...
04/06/2024

Bayan kungiyar kwad**o ta janye yajin aikin sai Baba Ta Gani da ta tsunduma, Ko an dawo muku da wutar nefa yanzu a yankunan da kuke?

Ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan masarufi a Nijeriya.Nawa farashin kwanon masara yake a inda kuke?
29/05/2024

Ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan masarufi a Nijeriya.

Nawa farashin kwanon masara yake a inda kuke?

DA DUMI-DUMI: An fara zaman jimamin mutum 28 da s**a ƙone bayan wani ya garƙame ƙofofin masallaci ya banka wuta a Kano Y...
15/05/2024

DA DUMI-DUMI: An fara zaman jimamin mutum 28 da s**a ƙone bayan wani ya garƙame ƙofofin masallaci ya banka wuta a Kano

Yanzu haka dai an kwashe su zuwa asibitin murtala dake Kano domin basu kulawar gaggawa...

Sai dai rahotannin baya-bayan nan suna nuna cewa wani abu ne ya fashe a masallacin amma dai ana jiran sanarwar yan sanda game da aukuwar lamarin....

Me kuke bayar da shawarar ayi akai?

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!!! Tsohuwar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Musa ...
11/05/2024

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!!!

Tsohuwar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Musa Waziri wadda ke amsa sunan Laila Masu Gonar Naira a tsohon shirin Labarina Series da ya gabata, ta gamu da mummunar hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya tare da mijinta, Tijjani Babangida wadda tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriya ne, da d'an ta Muhammad Fadeel da kuma kanin mijinta, Ibrahim Babangida a ranar Alhamis.

Kanin mijinta, Ibrahim Babangida, shi ya ke tuka motar da su ke ciki lokacin da hatsarin ya faru, wadda kuma a take Allah Ya karbi rayuwar sa, in da aka garzaya da ita kuma Maryam da d'anta da mijinta zuwa Asibiti don kula da lafiyar su.

Sai dai kwana daya da hatsarin (wato a daren jiya kenan) Allah Ya yi wa karamin d'an na ta, Fadeel rasuwa shima sakamakon buguwar da ya yi.

A yanzu haka dai a cikin mutum 4 da su ka yi hatsarin, Maryam da mijinta ne su ka saura, in da su ke karbar magani a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Shika a Zariya.

Daga cikin abun da wannan hatsari ya jawowa tsohuwar tauraruwa Maryam Waziri shine rasa bangare daya na fuskar ta: 😢

Ta rasa ido daya
Ta rasa kunne daya
Bangaren hancin ta ya gutsire
Gefen bakin ta ma ya gutsire 😥😥

Da fatan Allah Ya jikan Ibrahim da Fadeel, Ya gafarta musu. Ya bawa Maryam da Tijjani Babangida lafiya. Amin.

Daga Ahmad Nagudu

-

ƁAƘAR SAFIYA: Malama yau naga bakar safiya, ba fada ba komai mijina bayan yayi sallar Asuba ya mikomin takardar saki, ku...
29/04/2024

ƁAƘAR SAFIYA: Malama yau naga bakar safiya, ba fada ba komai mijina bayan yayi sallar Asuba ya mikomin takardar saki, kuma Wallahi lafiya lau muke, jiya tare muka ci Abincin dare muna cu muna hira ina ta saka shi nishada da walwala, don kwanan nan sai Naga ya zauna shi kadai Yana tunani kamar Yana da damuwa in na tambaye shi sai yace ba komai.

Da na karanta takardar na d**o kai muka hada ido idanuwa na cike da kwalla nace masa wane mai nayi Maka ?
Mai yayi zafi haka?
Sai yace min zama ne ya kare kawai .
Nayi hakuri.

Da ya ga kukana ya tsanan ta sai yace wance kiyi hakuri ba son kine bana yiba, Amman Malamai na sun tabbatar min da cewa in har ina tare dake bazantaɓa yin arziki ba, sai dai na samu mai suna Safiyyya na aura shine burujin sunan mu zai haɗu.

Malama Ya zanyi?
Ni marainiyata ce , yarana uku,yanzu ma watana biyu da haihuwa ta ukun. Babata da babana duk sun rasu na rasa yadda zanyi.😭

-Daga Umma Suleiman Ƴan Awaki

Irin wadannan yaran muke nema zamu yi masu aiki kyauta magani kyauta,transport kyauta a taimaka ayi sharing pls Idan an ...
28/04/2024

Irin wadannan yaran muke nema zamu yi masu aiki kyauta magani kyauta,transport kyauta a taimaka ayi sharing pls Idan an samu sai a tuntubi wannan number din 08067215846

Yadda Wani Ɗan Agajin JIBWIS Ya Shafe Wata Da Watanni Kwance Yana Neman Agaji.Dan uwa malam Abubakar da'awa ('Dan agaji ...
27/04/2024

Yadda Wani Ɗan Agajin JIBWIS Ya Shafe Wata Da Watanni Kwance Yana Neman Agaji.

Dan uwa malam Abubakar da'awa ('Dan agaji Yana Neman taimako) tin bayanda muka maidoshi daga asibiti, Alhamdulillahi jiki yana kyau.

Dayazo zaiyi magana sai kuka idanunshi, Wallahi abunda nafahimta tinkafin yafadimun, Abun yabani tsoro, wallahi wani daga cikin yaranshi hakanan yadauko tukunya Yana kankara( tinaninshi akwai abinchi aciki) Wani yaron kuma yagama kukan yunwa yagaji yakwanta Babu abinchi, wata Yarinyar kuma ruwa ta'debo tanasha amadadin abinchi , Natarar dika matanshi 2 sunfita Nemoma yara abinchi ko asamo koba a samoba .

Banyi tinanin yanda natarardashiba wallahi magungunan sun 'Kare, Gashi Babu kudin saye, garashin abinchi, gashi lokachinda likita yace akoma yawuce, Wai yanajin kunyar sake Neman taimakon al'umma.

Ga mata 2 ga Yara 8 'kananu ga makarantar Yaran tatsaya Sakamakon yunwa.

Danhaka Dan Allah Dan Annabi Muhammad (SAW) kutaimakeshi dakayan abinchi ,dakuma abunda zai rinka sayen magani da dressin.

Dan Allah ga numbershi Nan ta waya
👇🏽
0802 928 8032

Gamasu son taimakonshi kutaimakeshi ta wannan account din
👇🏽
Acct: 3025591926
First bank
Sadiq Umar

Kokuma kukira 07060937266 Sadiq Umar yari domin Jin Karin bayani, Allah yasa mugama da duniya lafia Ameen mungode kwarai dagaske

22/04/2024

Shin Daga Ina kuke Bibiyar wannan Shafi Namu ??

Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta gina gidaje 100 ga masu karamin karfi a kowace karamar hukuma a fadin kasar.
22/04/2024

Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta gina gidaje 100 ga masu karamin karfi a kowace karamar hukuma a fadin kasar.

Ba Zan taɓa iya Auren Ba Ko Zama da wanda ba ya Son Sana’ar dana ke yi ba na Harkan Fim - Cewar Jaruma Asmee Wakili
22/04/2024

Ba Zan taɓa iya Auren Ba Ko Zama da wanda ba ya Son Sana’ar dana ke yi ba na Harkan Fim - Cewar Jaruma Asmee Wakili

Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Ƙaddamar Da Taron Yaƙi Da Ta'addanci Na Afrika.A gobe Litinin 22 ga watan Afrilu idan Alla...
22/04/2024

Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Ƙaddamar Da Taron Yaƙi Da Ta'addanci Na Afrika.

A gobe Litinin 22 ga watan Afrilu idan Allah Ya kai mu, shugaban kasa Bola Tinubu zai bude taron yaki da ta’addanci a Afrika wanda za a yi a Abuja.

Najeriya tare da goyon bayan ofishin yaki da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya (UNOCT), ce ta shirya wannan taro wanda aka yi masa lakabi da "Karfafa Dangantakar Nahiyar Afirka Don Gina Cibiyoyin Taron Dangin Magance Barazanar Ta'addanci''

Makasudin taron na kwana daya shi ne inganta hadin gwiwar yaki da ta'addanci a bangarori daban-daban tsakanin kasashen yankin, tare da sake fasalin rawar da kasashen duniya ke takawa kan batun na ta'addanci a nahiyar, kazalika taron zai jaddada mahimmancin bai wa Nahiyar damar nemo hanyoyin magance matsalolin ta da kanta ba tare da an mata katsalandan ba.

Taron dai zai samar da wani dandali na yin nazari don tantance girman barazanar da ta'addanci ke yi wa nahiyar, da nufin cimma matsaya ta bai-daya kan muhimman matakan shawo kan matsalar.

Har ila yau, taron zai tattauna wasu batutuwan da s**a shafi hadin kan nahiyar da habaka karfin fada-ajin kasashen dake mambobin kungiyar, da samar da damar yin musayar ilmi da ayyukan ci gaban yankin.

Ana sa ran shugabannin kasashe da gwamnatoci da manyan jami'an gwamnati a fadin Afirka, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyi daban-daban, da wakilan jami'an diflomasiyya, da na kungiyoyin fararen hula za su halarci taron.

Malama Amina Mohammed, Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, na cikin wadanda za su halarci taron. Kazalika Mallam Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, da Mr. Vladimir Voronkov, mataimakin sakatare-janar a kan yaki da ta'addanci na kungiyar UNOCT, na cikin masu gabatar da jawabi a karshen taron.

Mahara sun yanka wa jama'a harajin zama lafiya a ZamfaraA Najeriya, yayin da ake cika kwanaki bakwai da 'yan bindiga s**...
21/04/2024

Mahara sun yanka wa jama'a harajin zama lafiya a Zamfara

A Najeriya, yayin da ake cika kwanaki bakwai da 'yan bindiga s**a yi dirar mikiya a garin Gidan Dan Zara na yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, maharan sun bukaci ragowar jama'ar garin su biya kudin fansar mutanen da ake garkuwa da su, kuma su biya wa garin harajin zama lafiya.

'Yan bindigan da s**a kai hari garin Gidan Dan-Zara na yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara a makon da ya gabata, inda s**a kona gidaje da masallatai da sauran kadarori, kuma s**a sace mutum 64, a yanzu sun kara jefa garin da ’yan ragowar jama'arsa cikin wani sabon tashin hankali kamar yadda wani mazaunin garin ya yi karin haske:

''Mutanen nan su na can hannun wa'dannan muane kuma sun bukaci ku'da'den fansa, wanda in ba a bayar ba su na ikirarin za su kashe su, shi kan shi garin kuma sun bukaci cewa akwai kudi da za a biya na sasanci kan garin, kamar shi ma ya zama kudin fansa kenan su na barazanar tashin garin gaba daya''.

Dangane da wannan batu BBC ta tuntuɓi Sulaiman Bala Idris, mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, da ASP Yazid Abubakar jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar.

Sai dai a wani abu mai tangan da arashi, dukkansu sun yi alkawarin bincikawa, kuma su sake kiran mu, amma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba mu ji daga gare su ba.

Sharuddan da 'yan bindigan s**a gindaya dai, suna zuwa ne yayin da mutane garin na Gidan Dan-Zara suke kokowar gyara ta'adin da maharan s**a tafka a makon da ya gabata. Ga kuma abin da mutumin garin ke cewa:

''Ana nan dai ana gyare-gyaren ta'adin da aka samu da kuma asarar gidaje da rumbuna, amma masallatai da gidaje ba za a iya gyaru ba a yanzu, masallatai wurare ne na Ibada tilas sai hankalin jama'a ya kwanta sannan za suyi maganar gyara, Sallar ma a waje ake yin ta. Idan ba a biya wadannan kudade ba su na barazanar cewar''.

Yanzu dai kallo ya koma ne ga batun yadda hukumomin da abin ya shafa asu fuskanci wannan wala-gigi da 'yan bindi

NAFDAC ta ƙwace jabun kayayyaki da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 50 a kantunan Abuja
21/04/2024

NAFDAC ta ƙwace jabun kayayyaki da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 50 a kantunan Abuja

Yaya Farashin Kayan Masarufi Ayanzu a Inda kuke Shin Farashin Ya Fara Sauka ? Muryar Arewa News
21/04/2024

Yaya Farashin Kayan Masarufi Ayanzu a Inda kuke Shin Farashin Ya Fara Sauka ? Muryar Arewa News

Makusantan fitacciyar ƴar Kannywood ɗin sun ce ta rasu ne bayan ta ɗauki sahur na azumin yau Talata.Za a yi jana'izarta ...
09/04/2024

Makusantan fitacciyar ƴar Kannywood ɗin sun ce ta rasu ne bayan ta ɗauki sahur na azumin yau Talata.

Za a yi jana'izarta bayan sallar la'asar a birnin Kano.

Fadar Sarkin Musulmi Ta Fitar Da Lambar Wayoyin Da Jama'a Za Su Kira Idan Sun Ga Jinjirin Watan Shawwal A Yammacin Yau"A...
08/04/2024

Fadar Sarkin Musulmi Ta Fitar Da Lambar Wayoyin Da Jama'a Za Su Kira Idan Sun Ga Jinjirin Watan Shawwal A Yammacin Yau

"A fito a duba jinjiriń watan karamar Sallah da kyau sannan duk wanda zai duba watan kada ya duba shi kadai su taru su da yawa su duba, domin samun ingantaccén shaida", sakon fadar Sarkin Musulmi ga musulmań Nijeriya.

Duk wanda ya ga jinjirin watan karamar Sallah zai iya tuntubar daya daga cikin wakilan mai alfarma Sarkin Musulmi kai tsaye ta wadannan lambonin dake kasa, domin ya shaida musu;

1, 08037157100
2, 07067416900
3, 08066303077
4, 08036149757
5, 08035965322
6, 08099945903

A taimaka a yada (sharing) domin sakon ya isa ga al'umma.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Fadar Sarkin Musulmi a Nijeriya ta ce a fara duba jinjirin watan Shawwal daga ranar Litinin.
07/04/2024

Fadar Sarkin Musulmi a Nijeriya ta ce a fara duba jinjirin watan Shawwal daga ranar Litinin.

Hukuncin tsokanar marasa lafiyar kwakwalwa ya kai shekara ɗaya a gidan yari ko tarar N500,000. Jama’a mu kiyaye. Babu ra...
03/04/2024

Hukuncin tsokanar marasa lafiyar kwakwalwa ya kai shekara ɗaya a gidan yari ko tarar N500,000. Jama’a mu kiyaye.

Babu ranar da mutane baza suyi tagging ɗina akan abunda ake yiwa wannan bawan Allahn ba. Yau wani likita ya biyo ni har inbox ya ɓuƙaci a ƙara jan hankalin masu tsokanarsa saboda lafiyarsa.

Kwanakin baya nayi magana akan sa inda na roki masu tsokanarsa su daina duba da cewa akwai rashin lafiya a tare da shi, kuma ashariyar da ake sawa yana yi domin saka wasu nishaɗi ba abun so bane, amma sai masu amfana da rashin lafiyarsa s**a sa shi yayi min video yana cewa “shi video yanzu ma aka fara yi masa”. Saboda na lura daga shi har masu tsokanar tasa suna amfana da rashin lafiyarsa.

To har yanzu dai ina kara kira a gare mu baki ɗaya. Na tabbataba idan ɗan’uwanmu ne baza muso abunda ke faruwa ba.

Idan zamu taimake shi saboda Allah muyi. Amma wannan abun bai dace ba. Amma lallai in ba’a daina ba zamu dau matakin da ya dace. Abba Hikima

Wanted !! Wanted!! Wanted!!Wannan da kuke gani azzalumi ne kuma yaci amanar mu ansamu wrong transfer na kudi da yakai du...
03/04/2024

Wanted !! Wanted!! Wanted!!

Wannan da kuke gani azzalumi ne kuma yaci amanar mu ansamu wrong transfer na kudi da yakai dubu dari biyar 500,000 a account dinshi munkirashi da niyar yataimaka yamaida kudin abashi nashi goro yace yaji ya amince Amma dan allah ayi hakuri saboda transfer dinshi ba yayi kuma yanzu baya kusa da bank Amma gobe zaije yayi withdraw na kudin ya turo a haka muka jirashi mun zata mai yiwa allah ne bamu sa anyi blocking din account dinshi ba , haka yaje yacire kudin kaff yanzu ma ku munkirashi baya daga waya
Ahaka muke neman taimakon jamaa duk wanda ya sanshi ko ya ganshi yataimaka ya kira number na da zan aje
Kuma ataimaka da share saboda wasu su gani
Kuma Akwai 50,000 ga wanda ya ganshi yataimaka muka kamashi.

Ina son matar da zan yi alfahari da ita duniya da lahira, ina so idan na aure ta ya zama mutuwa ce kawai za ta raba.
02/04/2024

Ina son matar da zan yi alfahari da ita duniya da lahira, ina so idan na aure ta ya zama mutuwa ce kawai za ta raba.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Madina - Allah ya karawa Annabi Daraja.
31/03/2024

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Madina - Allah ya karawa Annabi Daraja.

Bobrisky ya ci gasar sarauniyar kyau a sashin kamfanin Nollywood na Movie Premier da aka gudanar, inda ta doke sauran ƴa...
26/03/2024

Bobrisky ya ci gasar sarauniyar kyau a sashin kamfanin Nollywood na Movie Premier da aka gudanar, inda ta doke sauran ƴan mata.

A cikin wata sanarwa, shugaban ya kuma bayar da umarnin ɗage duk wasu takunkuman da Najeriya ta ƙaƙaba wa ƙasar kamar ya...
13/03/2024

A cikin wata sanarwa, shugaban ya kuma bayar da umarnin ɗage duk wasu takunkuman da Najeriya ta ƙaƙaba wa ƙasar kamar yanke wa ƙasar wutar lantarki da kuma riƙe kadarorinta.

An fita fara duba jinjirin watan Ramadana a Saudiyya. 📷 Inside the Haramain
10/03/2024

An fita fara duba jinjirin watan Ramadana a Saudiyya.

📷 Inside the Haramain

Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya ce a yayin ganawarsu da Malaman Kano, ya jinjina wa sheikh daurawa da hukum...
05/03/2024

Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya ce a yayin ganawarsu da Malaman Kano, ya jinjina wa sheikh daurawa da hukumar hisbah kan kokarinsu na kawar da badala da samar da zaman lafiya a Kano.

Rahotanni da muke samu yanzu na cewa fitaccen dan wasan barkwanci na fina-finan kudancin Nijeriya Mista Ibu ya mutu.
02/03/2024

Rahotanni da muke samu yanzu na cewa fitaccen dan wasan barkwanci na fina-finan kudancin Nijeriya Mista Ibu ya mutu.

DA ƊUMI ƊUMI: Wata majiya me tushe ta shaida cewa; akwai yiwuwar Malam Aminu Daurawa zai koma karagar kujerar sa na shug...
02/03/2024

DA ƊUMI ƊUMI: Wata majiya me tushe ta shaida cewa; akwai yiwuwar Malam Aminu Daurawa zai koma karagar kujerar sa na shugaban Hisba na Jihar Kano.

Gwamnatin Tinubu ta ce ba wani malami da zai fara tafsiri a watan Ramadan face sai yana da lasisi a bisa tsari na dokoki...
28/02/2024

Gwamnatin Tinubu ta ce ba wani malami da zai fara tafsiri a watan Ramadan face sai yana da lasisi a bisa tsari na dokokin ƙasa.

Ana ta samun bullar rahotan saukar Farashin kayayyaki abinci a kasuwanni musamman na Arewa, yaya Farashin shinkafa da Su...
26/02/2024

Ana ta samun bullar rahotan saukar Farashin kayayyaki abinci a kasuwanni musamman na Arewa, yaya Farashin shinkafa da Sukari da Masara a inda kuke?

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Arewa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share