12/02/2024
Akwai karancin masana ilimin cybersecurity a duniya bayan kuma shine skills din da duk duniya take nema, a duniya munada kwararrun masana ilimin cybersecurity (Experts) wadanda sun kai adadin 8.1m a cikin wannan adadin asalin expert kwararrun bawai masu basics knowledge ba ko intermediate ba, kwararru adadin su shine 4.7m globally. Wannan adadin yayi karanci kwarai dagaske.
Mai Gidanmu Professor of cybersecurity na farko a arewa, Professor Isa Ali Pantami yana cewa:" Kasamu Certificate din Information System Security Professionals (ISSP) a kalla a karkashin wannan certificate din ace kanada working experiance na a kalla shekara 5 (5years) sannan Prof yace wadanda kuma suke lower level suyi certificate din "Offensive security certified professional (OSCP)".
Malam ya kara da cewa: wadannan certifications guda biyun sunada matikar muhimmanci amma akwai courses sama da 100 da ake bukatarsu a bangaren cybersecurity.
A duk duniya ana neman masana cybersecurity, tun daga Africa, Asia har zuwa Arab domin a basu aiki ko ayi aiki dasu, malam yace akwai courses guda 15 a cikin cybersecurity ko information security da lallai idan ka karance su kuma ka kware kai tsaye za'a daukeka aiki a kasashen duniya.
Yan'uwa yakamata mu dage domin shiga cikin wadannan 4.7million experts din da suke a duniya.
Shin wane mataki kake yanzu a bangaren cybersecurity, akwai shiri na musamman da nakeso muyi a Arewacin nigeria, zamu hada gaggarumin taro na masana da daliban cybersecurity domin tattaunawa da kuma kara kwarin guiwa ga matasa akan skills. Kuma zamuyi kokari babban bakonmu ya kasance ubanmu kuma maigidanmu Professor of cybersecurity domin yazo yaga yadda yayansa suke himma da kokari akan field dinsa.
Wannan kadan daga cikin Mentorship da muke samu daga wurin mentor dinmu kenan.
Allah yasa mana Albarka, yayi ma rayuwarmu Albarka....🙏
©Salisu Abdurrazak Saheel, Special Assistant To Professor Isa Ali Pantami (S.A In Cybersecurity)