SHI'A Reporters

  • Home
  • SHI'A Reporters

SHI'A Reporters Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from SHI'A Reporters, Media/News Company, .

12/12/2023

Mahukuntar ƙasar Saudiyya Ce Kan Gaba Wurin Kisan Ƴan uwa Musulmai a Zaria jihar Kaduna 12 December 2015 bisa jagorancin Muhammadu Buhari (L) da Nasir El-Rufai (L)

Alhamdulillah 🎉✨Allah ya azurta ɗan gidan Shahed Sheikh Qasim Umar Sokoto da samun ɗiya mace, Allah Ubangiji ya raya, Al...
02/12/2023

Alhamdulillah 🎉✨

Allah ya azurta ɗan gidan Shahed Sheikh Qasim Umar Sokoto da samun ɗiya mace, Allah Ubangiji ya raya, Allah ya sanya mata albarka Albarkacin Annabi (S)

JA🔴: Ya na wakiltar shahidai da dama da sadaukarwar al'ummar Palasɗinu. BAƘI⚫: na wakiltar zalunci da tauye hakkin Falas...
23/11/2023

JA🔴: Ya na wakiltar shahidai da dama da sadaukarwar al'ummar Palasɗinu.

BAƘI⚫: na wakiltar zalunci da tauye hakkin Falasdinawa da s**a sha na tsawon shekaru marasa adadi.

FARI⚪: alamar aminci da soyayya, da tsarkin saƙon da aka aiko kowane Annabi da su zuwa ƙasar Falasdinu mai alfarma.

KORE🟢: yana nufin wadata, albarka, da bege ga kyakkyawar makoma.

— Dr Saliadeen Sicey

Wannan bawan Allah Abdurrabba Idris Yahaya  mutumin kirki ne, Course Mate dinane tare mukai karatu a Jami’ar Bayero dake...
22/11/2023

Wannan bawan Allah Abdurrabba Idris Yahaya mutumin kirki ne, Course Mate dinane tare mukai karatu a Jami’ar Bayero dake nan Kano, a halin yanzu yana fama da cutar cancer wadda taci karfin sa har takai idanun sa baya gani sai da daya, a madadin Abdulrabba ina neman masa taimako gun al'ummar Annabi.

Abdulrabba yana daga cikin best Graduating Student na set dinmu! Guru ne a Chemistry kuma mutum ne mai kokari da taimakon abokan karatun sa! Nakan tuna yanda ya taimakeni a wajen koyamin Chemistry courses har nai passing. Kwarewarsa wajen iya koyarda chemistry tasa duk dakikantar mutum idan ya koya ma saika fahimta. Ya taimaki ɗalibai da yawa, ciki har da ni.

Abin tausayi, ciwon yanzu ya yi tsanani har takai rashin kudin aikin da za'ai masa yasa sun koma gida da zama, cutar duk ta cinye abinda suke dashi, a halin yanzu suna buƙatar taimako don biyan kuɗin aikin da za'ai masa.

Ina roƙonku da ku taimakawa Abdulrabba domin a samu ai masa aiki. Kowacce gudumawa, komai kankantarta, za ta kawo gagarumin sauyi a rayuwarsa.

Idan kuna son ba da gudummawar ku, ga lambar account dinsa a kasa:

Account Number: 3142608608
Bank Name: First bank
Account Name: Abdurrabba Idris Yahaya
Phone No: 07066711067

Har ila yau, ina roƙonku da kuyi sharing wannan post din ga abokai, dangi, da yan uwa domin ceto Abdul.

Zaku iya tuntuba ta ko lambar sa dake sama idan kuna da wasu tambayoyi ko kuna son ƙarin bayani.

Nagode,
Amina Sani Hussain

SHI'A Reporters Muna miƙa sakon ta'aziyya zuwa ga Sheikh Dr Abduljabbar Kabara (H) tare da ƴan uwa da Iyalan Marigayi Ma...
21/11/2023

SHI'A Reporters Muna miƙa sakon ta'aziyya zuwa ga Sheikh Dr Abduljabbar Kabara (H) tare da ƴan uwa da Iyalan Marigayi Malam Aminu, Allah Ubangiji ya gafarta masa Allah ya sada shi da masoyansa Ahlulbait (As)

🇵🇸

Bayan Mutum Yasamu Ruwa Mai Tsarki Ya Wanke Inda Keda Najasa A Jikinsa Da Inda Najasa Yataɓa.1 - Mutum Zaiyi Niyyah 2 - ...
20/11/2023

Bayan Mutum Yasamu Ruwa Mai Tsarki
Ya Wanke Inda Keda Najasa A Jikinsa Da Inda Najasa Yataɓa.

1 - Mutum Zaiyi Niyyah

2 - Zai Wanke Kansa Zuwa Wuyansa, Yaɗan Shiga Jikinsa Kaɗan

3 - Wanke Tsagin Dama Na Jikinsa, Yaɗan Shiga Hagu Kaɗan

4 - Yawanke Tsagin Hagu Na Jikinsa, Yaɗan Shiga Dama Kaɗan

Ana Shiga Kowani Ɓangarene Wajen Wankewa Ta Yadda Zaizama Mai Wanka Yasamu Tabbacin Wanke Dukkan Inda Ake Buqata.

📚Fatawan Sayyid Khamna'i

✍ Abdullahi Dahiru

Ɗaya daga cikin mutum biyu da jami'an tsaron Nijeriya s**a kashe wurin zanga-zangar lumana na nuna goyon baya ga Al'umma...
18/11/2023

Ɗaya daga cikin mutum biyu da jami'an tsaron Nijeriya s**a kashe wurin zanga-zangar lumana na nuna goyon baya ga Al'ummar Falasɗinu.

Shariff Anas Usman ya wallafa wannan rubutun a dandalin sada zumunta na manhajar facebook a daidai lokacin da yake shirin fita, Ya ce: "IKON ALLAH A LOKACIN DA MUMINI KE QOQARIN NEMEMMUKU YANCI AMMA SHI FASIQI BATANCI KAWAI YA SANI GA MUMININ."

— Shaheed sayyid Anas Umar
— Shaheed Muhseen

17/11/2023

Jami'an tsaron Nijeriya sun afkawa masu jerin gwanon nuna goyon baya ga Falasɗinu a Kaduna.

A jiya ranar Alhamis Almajiran Sheikh Ibrahim Ya'qoub El Zakzaky (H) sun fito zanga-zangar lumana na nuna goyon baya ga Falasɗinu da nuna rashin amincewarsu ga haramtacciyar kasar Isr*'ila, kamar yadda sassan ƙasashen duniya Amurka, England, France suke fitowa kan tituna suna nuna baƙin ciki da alhinin su ga al'ummar Falasɗinu.

Wakilin SAR Reporters ya tabbatar da cewa mutum biyu daga cikin Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun rasa rayuwar su a daidai lokacin da Jami'an tsaron Nijeriya s**a buɗe wuta, kuma wannan ya jayo silar mutuwan wasu mutum biyu dake gefen titin.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SHI'A Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to SHI'A Reporters:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share