15/10/2023
Innalillahiwainailaihirrajun
Babbar Mota ta bige dattijo, Driver ya gudu be tsaya ba.
Wannan bawan Allah wani tsoho ne mai yawan shekaru wanda tsautsayi ya sa mota ta bigeshi anan kan titin wudil. Sai dai anyi rashin sa'a mai motar ya gudu bai tsaya ba.
A yanzu haka wannan tsoho an kaishi babban asibitin wudil sashin emergency ya samu karaya a hannunsa da kuma raunuka.
A halin da ake ciki yanzu wannan tsoho yau kwanansa 3 a asibitin wudil ba tare da mun samu iyalansa ba. Munyi iya kokarin mu wajen neman iyalansa amma ba a samu ko mutum daya ba wanda ya san su.
Sai dai wannan tsoho ya bude baki jiya ya furta cewa shi dan AJINGI ne, daga baya kuma yace shi dan SOKOTO ne, wanda hakan ya nuna cewa har yanzu bai gama sanin halin da yake ciki ba ko kuma ya samu matsala da tunaninsa sakamakon buguwar da yayi.
A yanzu haka kungiyar WUFF WUFF DEVELOPMENT ASSOCIATION tana kokarin neman sahalewar hukumar yan sanda da ta dama a dauki nauyin gyaran karayar da take hannun a wacce ba a gyara ta ba yau tsahon kwana 3 sannan a baa baa dama sama masa magani ba.
A yanzu haka wannan bawan Allah yana samun abinci ne daga wajen wata baiwar Allah anan cikin asibitin na Wudil.
Dan Allah jama'a duk wanda ya san wanan bawan Allah ko yasan wani wanda yake a ajingi LG ko SOKOTO yayi kokari ya nuna masa hotan sa ko Allah zaisa a samu iyalansa..
Allah ubangiji ya bashi lapiya, shi kuma direban da ya bigeshi ya gudu Allah yayi masa abinda ya dace dashi.
Source: Khalifa Ali Ado
Secretary for Wuff Wuff Development Association Wudil
Rahoto 📷: Mujahid Saleh Saad - Dan maliki Mujahid Saleh Saad