19/07/2014
ADDU’A MAKAMIN MUMINI
FALALAR SALATI GA MANZO DA IYALAN GIDANSA (AS)
Tera da Abubakar Isah
[email protected]
Allah (SWT) yana cewa: LALLAl ALLAH DA MALA 'IKUNSA SUNA YI WA MANZO SALATl, YA KU WADANDA KUKA YI IMANI KU YI MASA SALATI DA TASLIMI.
Ya zo a cikin tafsirin Almizan Sayyid Tabataba'i yana cewa: Salatin Allah ga Manzonsa a nan shi ne ludufin Allah da rahamarsa yanke ba tare da wani kaidi ba ga Manzonsa. Sannan Salatin Mala'iku ga Manzon Allah (S) a nan shi ne tazkiyya da nema masa gafara a gurin Allah. Sannan salatin muminai ga Manzo a nan shi ne addu'a da k*ma rahama.
Salatin Allah (T) da Mala'ikunsa (AS) ga Manzo, kafin umurtan muminai dalili shi ne akan yin koyi da Allah da Mala'iku wajen yi wa Manzo salati.
A nan mai karatu yana iya ganin cewa babu wata ibada wace Muminai suke yi wacce take koyi ne ga Allah da Mala’ikunsa, in banda salatin Manzo (S). Ke nan ba mai yiwuwa bane mutum ya iya kirdadon matsayin yin salati ga Manzon Allah (S) da iyalan gidansa.
Ya zo a cikin Durrul Mansur na Imam Suyudi yana cewa: An ruwaito daga Ibn Abi Shaiba. Ahmad, Abdu Ibn Hamid, Bukhari, Muslim. Abu Dauda, Tirmizi. Nisa'i. Ibn Hajari yana cewa: Wani mutum ya tambayi Manzo cewa: Ya Manzon Allah. yi maka sallama wannan mun sani. Amma yaya salati a gare ka yake? Sai Manzo (S) ya ce: "Ku ce: “ Allahumma salli ala Muhammad wa ali-Muhammad k**a sallaita ala Ibrahima wa ali-Ibrahima, Allahumma barik ala Muhammad wa ali-Muhammad k**a barakta ala Ibrahima wa ali-Ibrahima, innaka hamidun majid".
Ya zo a cikin Yanabi'ul Muwadda cewa: An ruwaito daga Manzon Allah yana cewa kada ku yi min salati yankakke. Sai sahabbai s**a ce wane irin salati ne yankakke ya Manzon Allah? '' Sai ya ce: salati yankakke shi ne ku ce: Allahumma salli ala Muhammad. sai ku yi shiru ku ki }arasawa. In za ku yi min salati ku ce: Allahumma salli ala Muhammad wa ali-Muhammad.
Ya zo a cikinYanabi’ul Muwadda cewa Abu Nu’aim Alhafiz da wasu jama'a daga Malaman tafsiri. sun ruwaito daga Mujahid da Abu Salih daga Ibn Abbas (RA) yana cewa Ali-yasin. sune Ali-Muhammad, domin Yasin suna ne daga sunayen Muhammad (S).
Falalar salati ga Manzo da iyalan gidansa, wannan ba abu ne wanda wani alkalami zai iya rubuta shi ba. ko wani harshe zai iya furuci da shi ba. a nan kawai za mu ]an zo ne da wasu daga cikin hadisan Manzo (s) ne, alabashi mai karatu sai ya yi kokari ya fadada ko ta nan Allah zai dube shi da idon rahma.
Ya zo a cikin Kanzul Ummal, Manzo yana cewa: salati a kaina haske ne a kan sira]i gobe kiyama.
An ruwaito daga Abdullahi Ibn Nu'uman yana cewa: Wata rana na gaya wa Baban Abdullah (Imam Sadiq) cewa na shiga dakin Ka'aba, amma ban sami komai na addu'a ba sai dai kawai salatin Manzo. Sai ya ce: Lallai babu wani wanda ya fito da abin da ka fito da shi na falala da alheri.
Imam Sadiq (AS) ya ruwaito daga Imani Baqir (AS) yana cewa: Mafi nauyin abin da za a daura a mizani ran kiyama shi ne salatin Manzon Allah (S).
An ruwaito daga Anas Ibn Malik yana cewa: Manzon Allah (S) yana cewa: Duk wanda aka ambace ni a gunsa, to ya yi min salati. domin kuwa wanda ya yi min salati sau daya, Allah Mabuwayi da daukaka zai yi masa salati sau goma.
An ruwaito cikin Sunan Abi Dawud da Nisa'i daga Aus Ibn Aus yana cewa: Manzon Allah (S) yana cewa: Mafificin rana daga cikin ranakunku shi ne Juma’a. saboda haka ku yawaita yi min salati a cikinta. domin ana bijiro min da salatinku.
Ya zo a cikin Attawassul na Shaikh Ja'afar Subhani yana cewa: Manzo ya ce: Allah (T) yana da Mala’iku masu kewayawa ko'ina a doron }asa. suna isar da salatin alummata a gare ni.
Manzo (S) yana cewa: Babu wani mutum wanda zai yi min salati face Allah ya mayar mani da ruhina na mai da masa da sallama.
"'Duk wanda ya yi min salati a kabarina zan ji shi. Wanda ya yi min daga nesa za a isar min."
"Ku yi min salati domin salatinku yana isowa gare ni daga duk inda kuke.
"Duk wanda ya ziyarce ni bayan wafatina ya yi min sallama, zan mai da masa har sau goma. K*ma Mala'iku goma za su ziyarce shi suna masu sallama a gare shi."
An ruwaito daga Amirul muminina Aliyu (AS) cikin Nahajul Balaga yana cewa: Idan kana da wata bu}ata gurin Allah ka fara da salatin Manzo, sannan ka ambaci bukatarka. Domin Allah mafi karimci ne akan a tambaye shi abu biyu ya biya daya ya bar dayan.
Saboda haka, da wadannan takaitattun Hadisan zamu fahimci tasiri da matsayi na garabasar da ke tattare da salati ga fiyayyen halitta da iyalan gidansa tsarkaka.
K*ma zamu iya ]aukar Jamhuriyar muslunci ta Iran a matsayin misali akan yanda s**a muhimmantar da salati ga Annabi Muhammad (S) a matsayin jagoran lamurransu, domin, bincike ya nuna cewa. A kasar Iran babu wani taro wanda mutane za su taru ko na sha’anin addini ko bukukuwa, ko ziyara ko cin abinci face sun yawaita yi wa Manzo salati kafin su watse. wannan ana yin sa ne a matsayin hakkin zama ko taro.
"A duk lokacin da Liman yake hu]uba ko karatu cikin sallah. ko wani mai wa'azi ya ambaci Muhammad (S), to ka’ida ne ya tsaya har sai an yi wa Manzo salati kafin ya ci gaba.
idan kuwa ya zama ranar maulidin haihuwar Manzo ne, wannan ranar babu wata ranar buki a kasar wacce ta kai ta ko ta yi kusa da ita. Mutane gaba ]ayansu za su fito da manyan fitilu su jera su da filawowi da manya-manyan kayan kwalliya da na alatu su jera su a gefen t**i har sai ya zamo k**ar ba za ka iya bambance tsakanin dare da rana ba.
Mai bukata saboda murna da haihuwar Manzon Allah (S). A wannan rana sai ka ga mutane suna zagayawa ko'ina suna murna suna yawaita salati don murna da zagayowar ranar da aka haifi Shugaban Manzanni da halittu baki daya.