08/09/2023
Da dumi'dumi:
Gwamna Abba K Yusuf ya amince da fitar N3,577,288,540 ga ma’aikatar ilimi mai zurfi don daukar nauyin dalibai Dari biyar da Hamisin 550; ’yan asalin jihar da s**a cancanci yin karatun digiri na biyu a kasashen waje, yayin da aka amince da N544,321,168 ga ma’aikatar ilimi don biyan wasu makudan kudade dangane da ciyar da daliban makarantun kwana.
An kuma amince da fitar da N79,284,537, domin saukaka gyara makarantun kwana 11 da aka rufe a jihar, yayin da aka amince da fitar da N131,500,000 don gudanar da jarrabawar cikin gida ta 2023 (BECE/BEICE AND SSQE/SAISQ/TAHFEEZ da TAJWEE).
Daga Ibrahim Adam.