26/10/2023
LOKACINKA NE..
Bidiyo da aka nuna Rarara a gaban 'yan jarida yana zagin Shugaba Buhari cewa shine ya kashe kasa gaskiya ne bidiyon
Lallai ko a mafarki banyi zaton Rarara zai juya wa Shugaba Buhari baya ba, domin duk abinda Rarara ya samu na arziki sanadin Buhari ne, amma da yake butulu ne yau Buhari yake zagi
Dama haka dabi'ar mawaka, maroka da karuwai suke, suna bin wanda suke tunanin zasu tatsi kudi daga gareshi ne
To amma ni kaf a cikin maganganun Rarara babu wanda ya bata min rai kamar cewa da yayi wai Wallahi wata ukun Bola Tinubu yafi shekara 8 din Buhari
Rarara nace a gidan Babarka kenan?
Shin Rarara kana da imani da cikakken hankali kuwa?
Ka dubi halin bala'in yunya da talauci da aka jefa talakawan Arewa sakamakon janye tallafin man fetur da Tinubu yayi amma a haka kake cewa wai wata uku yafi shekaru 8 din Gwamnatin Buhari
Wallahi na dena ganin laifin 'yan Kwankwasiyya da suke caccakar Rarara, tabbas sun yi daidai, kuma da ina yin ashar tabbas Wallahi da sai na dura wa Rarara buhun ashar yau din nan ko zan ji sanyi a raina, mugu kawai marar imani da tausayi
Babu abinda zamu ce tsakanin mu da wanda yake cewa wata ukun Tinubu yafi Shekara 8 din Buhari sai Allah Ya isa
Ina Ministocin Buhari wadanda s**a yi ta janyo Rarara cikin ofis dinsu suna bashi kwangiloli Kukayi watsi da masayoyan Buhari na gaskiya? to yau ga sakamakon nan
Rarara lokacinka ne, amma kana da iyaka watan watarana, sai dai zai yi wahala kayi kyakkyawan karshe da wannan halin naka