DAN FODIO TV

DAN FODIO TV Education

"Amadadin dukkan Adimis na Wannan Shafi na " Abu Abdirrahman Assalafy KanoMuna Miko Sakon Barka da Sallah ga dukkanin Da...
10/04/2024

"Amadadin dukkan Adimis na Wannan Shafi na " Abu Abdirrahman Assalafy Kano

Muna Miko Sakon Barka da Sallah ga dukkanin Daukacin Musulman Duniya da Fatan Allah ya Karbi Ibadun Mu"

" اللهم تقبل منا صالح الأعمال "

Ranim Alkanawiy

08/04/2024

Daga 'karshe dai ya tabbata Dr. Idris AbdulAziz Dutsen Tanshi yau 'din nan zai sauka a tashar saukan jirgi na Bauchi. 'Dan'uwa Datti Assalafiy ya kira ni ya shaida min yanzu haka.

Muna rokon Allah da ya dawo da Mallam lafiya ya Kuma 'kara ba Mallam kariya daga sharrin masharranta da Kuma miyagun Malaman Sunnah dana bidi'a.

Engr Abu-Ameena Bn Khamis

HUKUMAR HISBAH TA FITAR DA KA'IDOJI GA MASU  GIDAJEN WASANNI DA ZA SU KIYAYE A LOKUTAN  BUKUKUWAN SALLAH KARAMA.1 Ba'a Y...
08/04/2024

HUKUMAR HISBAH TA FITAR DA KA'IDOJI GA MASU GIDAJEN WASANNI DA ZA SU KIYAYE A LOKUTAN BUKUKUWAN SALLAH KARAMA.

1 Ba'a Yarda Da Shigar Da Kananan Yara Gidajen Wasanni Ba.
2 Ba'a Yarda Da Chakuduwar Maza Da Mata Ba.
3 Duk Lokacin Sallah Za'a Dakatar Da Wasa Domin Yin Sallah.
4 Ba'a Yarda Da Shiga Da Duk Wani Nau'in Makamiba.
5 Ba'a Yarda Da Sayarda Kayan Maye Kosha a Gidan Wasa Ba.
6 Ba'a Yarda Da Shigar Banza Ba Daga Bangaran Maza Ko Mata.
7 Ba'a Yarda a Bawa Yan Daudu Damar Gabatar Da Ko Wane Irin Wasa Ba.
8 Dolane a Kaucewa Sanya Wakokin Batsa Ko Mak**ancin Haka.
9 Ba'a Yarda Da Rawar Mace Da Namijiba.
10 Dole Duk Gidan Wasa Su Tashi Kafin Lokacin Salar Magariba.

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (10)Da yawa daga cikin masu Azumi ba su da lada sai yunwa!Ya tabbata Annabi (...
07/04/2024

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (10)

Da yawa daga cikin masu Azumi ba su da lada sai yunwa!

Ya tabbata Annabi (saw) ya ce:
"رب صائم ليس له من صيامه إلا الجوع، ورب قائم ليس له من قيامه إلا السهر".

سنن ابن ماجه ت الأرنؤوط (2/ 591) صحيح ابن خزيمة ط 3 (2/ 959)، المستدرك على الصحيحين للحاكم (1/ 596)، مسند أحمد ط الرسالة (14/ 445)

"Da yawa daga cikin masu Azumi ba shi da komai a Azuminsa sai yunwa. Haka da yawa daga cikin masu Sallar dare ba shi da komai a Sallar tasa sai rashin bacci".

Wannan duka yana kara tabbatar mana da cewa; Allah Madaukaki ba ibada ta zahiri kawai yake so ba, a'a, ibada mai ruhi, mai samar da Taqwa da tsoronsa yake so k**ar yadda ya ce:
{ يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ } [البقرة: 183]

"Ya ku wadanda s**a yi imani, an wajabta muku Azumi k**ar yadda aka wajabta ma wadanda s**a gabace ku, don ku ji tsoron Allah, ku samar da Taqwa".

Shi ya sa Shaikhul Islami bayan ya ambaci Hadisin sai ya ce:
يقول: إنه تعب ولم يحصل له منفعة، لكن برئت ذمته، فسلم من العقاب فكان على حاله لم يزدد بذلك خيرا.
والصوم إنما شرع لتحصيل التقوى
منهاج السنة النبوية (5/ 196)

"Annabi (saw) yana fadin cewa; mai Azumin ya yi wahalar banza, Azumi da Sallar daren nasa ba su yi masa amfani ba, duk da cewa; ya sauke wajibin Azumin da ya hau kansa, kuma ya kubuta daga azaba. Saboda yana nan k**ar yadda yake a da, bai kara ma kansa aikin lada ba. Da ma shi Azumi an shar'anta shi ne don samar da Taqwa da jin tsoron Allah".

A wani wajen kuma ya ce:
الكذب والغيبة والنميمة إذا وجدت من الصائم فمذهب الأئمة أنه لا يفطر ومعناه أنه لا يعاقب على الفطر كما يعاقب من أكل أو شرب والنبي - صلى الله عليه وسلم - حيث ذكر «رب صائم حظه من الصوم الجوع والعطش» لما حصل من الإثم المقاوم للصوم
الفتاوى الكبرى لابن تيمية (5/ 376)

"In an samu yin karya da cin naman mutane da annamimanci a wajen mai Azumi to Malamai sun tafi a kan cewa; Azuminsa bai karye ba, ma'ana; ba za a yi masa azaba a kan bacin Azumin k**ar yadda za a yi ma wanda ya ki yin Azumin yana ci yana sha ba. Annabi (saw) ya ce: "Da yawa daga cikin masu Azumi ba shi da komai a Azuminsa sai yunwa" saboda zunubin da ya samu wanda ya fi karfin Azumin nasa".

Saboda haka 'yan uwa, mu yi iya kokarinmu wajen kare Azuminmu da Sallolin dare da muke yi, da sauran aiyukan ibada daga dukkan abin da zai zare musu ruhin ibada daga cikinsu, wato a rasa samar da Taqwa da tsoron Allah. Lallai duk ibadar da ta zama ba ta da ruhi to lallai aikin banza ce

Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (9)Shin Gulma da Giba da Annamimanci da Zagin mutane suna karya Azumi?Ya tabb...
06/04/2024

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (9)

Shin Gulma da Giba da Annamimanci da Zagin mutane suna karya Azumi?

Ya tabbata cikin Hadisin da Imamul Bukhari ya riwaito da isnadinsa:
عن أبي هريرة رضي الله عنه، قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «من لم يدع قول الزور والعمل به، فليس لله حاجة في أن يدع طعامه وشرابه»
صحيح البخاري (3/ 26)

Daga Abu Huraira (ra), Annabi (saw) ya ce:
"Duk wanda bai bar yin maganar karya ko aiki da ita ba, to Allah ba ya bukatar ya bar cin abinci da shan abin shansa (Allah ba ya bukatar Azuminsa)".

Wannan ya sa wasu Malamai cikin Salaf suke ganin gulma da cin naman mutane da annamimanci suna karya Azumin mutum. Wasu Malaman kuma suna ganin ba ya karyawa.

Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya fayyace mas'alar inda ya ce:
"وتحقيق الأمر في ذلك أن الله تعالى أمر بالصيام لأجل التقوى وقد قال صلى الله عليه وسلم: "من لم يدع قول الزور والعمل به فليس لله حاجة في أن يدع طعامه وشرابه"، فاذا لم تحصل له التقوى لم يحصل له مقصود الصوم فينقص من أجر الصوم بحسب ذلك".
مختصر الفتاوى المصرية (ص: 289)

"Tantance magana a kan haka shi ne; lallai Allah Madaukaki ya yi umurni da yin Azumi ne don samar da Taqwa da jin tsoronsa, kuma Annabi (saw) ya ce:
"Duk wanda bai bar yin maganar karya ko aiki da ita ba, to Allah ba ya bukatar ya bar cin abinci da shan abin shansa".
To idan Taqwar ba ta samu ga mai Azumi ba, to ba a samu manufar da ake so na yin Azumin nasa ba, don haka zai tauye ladansa gwargwadon munanan abin da ya aikata".

Saboda haka Azuminsa yana nan, amma kuma ba shi da ladan Azumin.
Don haka matukar mutum yana Azumi, amma bai kiyaye harshensa daga maganganun banza da karerayi da gulman mutane da zaginsu da cin namansu ba, to wahalar banza kawai yake sha, ba zai samu ladan komai ba, saboda Allah ba ya bukatar Azumin da ba zai samar da Taqwa ma bawa, ta hanyar kare gabobinsa daga aikata munanan aiyuka ba.

Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (8)Da Nassin Alkur'ani Allah ya saukaka wa Matafiyi da Maras lafiya yin Azumi...
05/04/2024

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (8)

Da Nassin Alkur'ani Allah ya saukaka wa Matafiyi da Maras lafiya yin Azumin Ramadhana a halin tafiya ko rashin lafiya. Don haka ya halasta su sha Azumi sai su rama Azumin da s**a sha bayan Ramadhan, in uzurin nasu ya gushe. A kan wannan Musulmai s**a yi Ijma'i.

Don haka Maras lafiya da ake nufi shi ne wanda ba zai iya yin Azumin ba saboda rashin lafiya ko kuma in ya yi rashin lafiyan nasa zai karu.

Shaikhul Islami ya ce:
المريض الذي لا يطيق الصيام أو الذي يزيد الصوم في مرضه؛ له أن يفطر، وإن تحمل وصام وأجزأه
شرح العمدة لابن تيمية (1/ 208)

"Maras lafiya shi ne wanda ba zai iya yin Azumi ba, ko wanda Azumin zai kara masa rashin lafiyan nasa. Amma idan ya jure ya yi Azumin to ya isar masa ba sai ya rama ba".

To a kan samu wasu masu lafiya amma kuma in sun yi Azumin za su kamu da rashin lafiya, to su ma ana kiyasinsu a kan marasa lafiya, saboda haduwarsu cikin illarn hukuncin, wato samun shan wahala.

Shaikhul Islam ya ce:
وفي معنى المريض الصحيح الذي يخاف من الصوم مرضا أو جهدا شديدا، مثل من به عطاش لا يقدر في الحر على الصوم، وهو يقدر عليه في الشتاء، أو امرأة قد حاضت والصوم يجهدها.
شرح العمدة لابن تيمية (1/ 209)

"Mai lafiyan da yake tsoron kamuwa da rashin lafiya, ko yake tsoron wahala mai tsanani shi ma zai shiga cikin ma'anar maras lafiya, misalin wanda yake da jin kishin ruwan da ya kai ba zai iya yin Azumi a zafi ba, sai a lokacin sanyi ne kawai zai iya yi, ko matar da bayan ta yi al'ada Azumin yana wahalar da ita".

Saboda haka hukuncin Maras lafiya ko wanda yake tsoron kamuwa da rashin lafiya in ya yi Azumi shi ne ana so kar ya yi Azumin, kuma ba a so ya yi, wato yin nasa Makruhi ne.

Shaikhul Islam ya ce:
إن المريض يستحب له الفطر، ويكره له الصوم، فإن صام أجزأه.
شرح العمدة لابن تيمية (1/ 209)

"Maras lafiya ana so ya sha Azumi, ba a son ya yi Azumin, amma in ya yi Azumin ya isar masa ba zai yi ramuko ba".

Wannan sauki ne na Shari'a, saboda Allah yana son bayinsa da sauki ne, ba ya so su shiga tsanani da wahala. Allah ya ce:
{يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ } [البقرة: 185]

Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)

03/04/2024

Zamu dawo da Tafseeran Sheikh Alkasim Hotoro na 2023' Daga Yau insha Allah
Ashafukan Mu Kamar Haka

abdirrahman Assalafy Kano
# DAN FODIO TV
# Dr Idris Abdul-aziz dutsen Tanshi Fans

Insha Allah Daga Yau. Misalin 04:20 Na Yamma

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (6)Mutane sun kasu kashi biyu wajen karya Azuminsu:1- Akwai mai ganganci. Wan...
02/04/2024

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (6)

Mutane sun kasu kashi biyu wajen karya Azuminsu:
1- Akwai mai ganganci. Wannan dole ya rama Azumin da ya karya, in kuma saduwa ne (jima'i) dole ya yi kaffara bayan ya yi ramuko.
2- Akwai mai kuskure, ko mantuwa, ko rashin sani (jahilin da bai san hukunci ba ko bai san yadda ake yi ba). Wannan babu ramuko in ya karya Azuminsa bisa kuskure, ko mantuwa ko rashin sani b***e kuma kaffara.

Wasu Malaman sun banbanta tsakanin mai manyuwa da jahili maras sani wajen karya Azumi. Al-Imam Ibnul Qayyim ya ce:
قستم الجاهل على الناسي في عدة مسائل وفرقتم بينهما في مسائل أخر، ففرقتم بينهما فيمن نسي أنه صائم فأكل أو شرب لم يبطل صومه، ولو جهل فظن وجود الليل فأكل أو شرب فسد صومه، مع أن الشريعة تعذر الجاهل كما تعذر الناسي أو أعظم؟ كما عذر النبي -صلى الله عليه وسلم- المسيء في صلاته بجهله بوجوب الطمأنينة فلم يأمره بإعادة ما مضى...
وعذر عدي بن حاتم بأكله في رمضان حين تبين له الخيطان اللذان جعلهما تحت وسادته ولم يأمره بالإعادة
إعلام الموقعين (3/ 10)

"Kun yi kiyasin jahili maras sani a kan mai mantuwa a mas'aloli da yawa, amma sai kuma kuka raba tsakaninsu a wasu mas'alolin, sai kuka raba tsakaninsu a mas'alar mai Azumi idan ya manta ya ci abinci ko ya sha abin sha, kuka ce: Azuminsa bai baci ba, amma sai kuka ce: idan bai sani ba, sai ya yi zaton akwai sauran dare, sai ya ci ko ya sha Azuminsa ya baci, alhali Shari'a tana yin uzuri ga jahili k**ar yadda take yi wa mai mantuwa ko ma fiye da haka, k**ar yadda Annabi (saw) ya yi uzuri ga wanda ya munana Sallarsa saboda ya jahilci wajabcin nitsuwa a cikin Sallah, sai bai umurce shi da ramukon Sallolinsa na baya ba...
Haka kuma Annabi (saw) ya yi uzuri ga Adiyyi bn Hatim (ra) a kan cin abinci da ya yi a Ramadhan har sai da gari ya waye wartal, har sai da ya iya banbance tsakanin farin zare daga bakin zare, wadanda ya sanya su a karkashin filonsa, amma Annabi (saw) bai umurce shi da ramuko ba".

Saboda haka jahili mai halin rashin sani dadai yake da mai kuskure ko mantuwa a wajen karya Azumi, duka babu ramuko a kansu. Wannan shi ne zabin Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya k**ar yadda Almajirinsa Al-Imam Ibnul Qayyim ya hakaito inda ya ce:
تناقضوا كلهم في جعل الناسي في الصوم أولى بالعذر من الجاهل، ففطروا الجاهل دون الناسي، وسوى شيخنا بينهما، وقال: الجاهل أولى بعدم الفطر من الناسي
إعلام الموقعين (5/ 506)

"Masu Qiyasi gaba dayansu sun yi tufka da warwara ta yadda s**a sanya mai mantuwa a Azumi shi ya fi cancantar uzuri feye da jahili mai rashin sani, sai s**a ce: Azumin jahili ya baci, amma in mai mantuwa ne Azuminsa bai baci ba. Amma Shehinmu (Ibnu Taimiyya) ya daidaita tsakaninsu, ya ce: Jahili shi ya fi cancantar a ce: Azuminsa bai baci ba fiye da mai mantuwa".

Saboda haka duk wanda ya karya Azuminsa saboda mantuwa ko kuskure ko rashin sani to babu ramuko ko kaffara a kansa, kawai zai ci gaba da Azuminsa ne, Azuminsa yana nan bai baci ba. A kan haka Shaikhul Islami ya ce:
قد ثبت بدلالة الكتاب والسنة أن من فعل محظورا مخطئا أو ناسيا لم يؤاخذه الله بذلك وحينئذ يكون بمنزلة من لم يفعله فلا يكون عليه إثم ومن لا إثم عليه لم يكن عاصيا ولا مرتكبا لما نهي عنه وحينئذ فيكون قد فعل ما أمر به ولم يفعل ما نهي عنه. ومثل هذا لا يبطل عبادته إنما يبطل العبادات إذا لم يفعل ما أمر به أو فعل ما حظر عليه.
مجموع الفتاوى (25/ 226)

"Ya tabbata da dalilan Alkur'ani da Sunna cewa; duk wanda ya aikata wani abu da aka hana a halin kuskure ko mantuwa to Allah ba zai k**a shi a kan haka ba, a wannan halin zai zama k**ar bai aikata laifin ba, don haka babu zunubi a kansa, duk wanda babu zunubi a kansa kuwa to shi ba mai sabo ba ne, ko bai zama wanda ya aikata abin da aka hana ba. To a wannan lokaci sai ya kasance ya aikata abin da aka umurce shi, bai aikata abin da aka hana shi ba. Irin wannan kuwa ibadarsa ba ta baci, kawai ibada tana baci ne ne idan mutum bai aikata abin da aka umurce shi ya aikata ba, ko kuma in ya aikata abin da aka hana shi aikatawa".

Lallai wannar ka'ida ce ta Shari'a mai girma wajen hukunci wa mutane da aiyukansu, rashin sanin irin wannar ka'ida ne yake jefa jahilai da masu guluwwi cikin kuskure wajen hukuncinsu ga mutane ko a kan aiyukansu.

Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)

02/04/2024

Miliyan 84 aka taya Littafan Cikin Library na Mal Alqasim Umar Jibrin Hotoro (Hafizahullah)
Inji Brr Ishaq Ishaq Adam Hafizahullah

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (5)Malamai sun yi sabani a kan Mai Azumi idan ya ci abinci ko ya sha abin sha...
01/04/2024

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (5)

Malamai sun yi sabani a kan Mai Azumi idan ya ci abinci ko ya sha abin sha da rana a watan Ramadhana a halin mantuwa ko kuskure. Sawa'un wanda ya manta ya ci ko ya sha, ko wanda yana ta ci da sha bisa zaton Alfijir bai keto ba, alhali tun tuni Alfijir ya keto.
Wasu Malaman sun ce: Azuminsa ya baci, sai ya yi ramuko.
Wasu kuma sun ce: Azuminsa yana nan bai baci ba, don haka babu ramuko a kansa.
Wannan shi ne fahimtar da Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya zaba, saboda karfin dalilansu da dacewarsa ga kiyasi, Al-Imam Ibnul Qayyim da Allama Ibnu Muflih sun hakaito haka daga gare shi. Duba:
إعلام الموقعين (3/ 244)، الفروع (5/ 39)

Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya ce:
والذين قالوا: لا يفطر في الجميع قالوا: حجتنا أقوى ودلالة الكتاب والسنة على قولنا أظهر؛ فإن الله قال: {ربنا لا تؤاخذنا إن نسينا أو أخطأنا} فجمع بين النسيان والخطأ؛ ولأن من فعل المحظورات الحج والصلاة مخطئا كمن فعلها ناسيا وقد ثبت في الصحيح أنهم أفطروا على عهد النبي صلى الله عليه وسلم ثم طلعت الشمس ولم يذكروا في الحديث أنهم أمروا بالقضاء ولكن هشام بن عروة قال: لا بد من القضاء وأبوه أعلم منه وكان يقول: لا قضاء عليهم. وثبت في الصحيحين أن طائفة من الصحابة {كانوا يأكلون حتى يظهر لأحدهم الخيط الأبيض من الخيط الأسود وقال النبي صلى الله عليه وسلم لأحدهم: إن وسادك لعريض إنما ذلك بياض النهار وسواد الليل} ولم ينقل أنه أمرهم بقضاء وهؤلاء جهلوا الحكم فكانوا مخطئين. وثبت عن عمر بن الخطاب أنه أفطر ثم تبين النهار فقال: لا نقضي فإنا لم نتجانف لإثم. وروي عنه أنه قال: نقضي؛ ولكن إسناد الأول أثبت وصح عنه أنه قال: الخطب يسير. فتأول ذلك من تأوله على أنه أراد خفة أمر القضاء لكن اللفظ لا يدل على ذلك. وفي الجملة فهذا القول أقوى أثرا ونظرا وأشبه بدلالة الكتاب والسنة والقياس وبه يظهر أن القياس في الناسي أنه لا يفطر والأصل الذي دل عليه الكتاب والسنة أن من فعل محظورا ناسيا لم يكن قد فعل منهيا عنه؛ فلا يبطل بذلك شيء من العبادات ولا فرق بين الوطء وغيره سواء كان في إحرام أو صيام.
مجموع الفتاوى (20/ 572 - 573)

"Wadanda s**a ce: Azumin mutum ba zai baci ba, a dukkan halayen mantuwa da kuskure, sawa'un a lokacin fitowan Alfijir ko lokacin faduwar rana, s**a ce: Hujjarmu ta fi karfi, kuma dalilan Alkur'ani da Sunna suna nuni a kan haka. Saboda Allah ya tabbatar a cikin Ayar Baqara cewa; ba zai k**a masu mantuwa da kuskure da laifi ba, a cikin Ayar sai ya hada mantuwa da kuskure. Saboda aikata laifi a aikin Hajji da Sallah a halin kuskure dadai yake da wanda ya aikata cikin mantuwa. Kuma ya tabbata a Hadisi ingantacce; Sahabbai sun sha ruwa a zamanin Annabi (saw) sai rana ta bayyana, kuma babu wanda ya umurce su da ramuko. Haka ya tabbata a Hadisi ingantacce; wasu daga cikin Sahabbai sun kasance suna ci da sha har sai farin zare ya banbanta daga bakin zare, bayan Alfijir ya fito har gari ya yi haske sosai, amma Annabi (saw) bai umurce su da ramuko ba, saboda wadannan jahilai ne masu kuskure. Haka ya tabbata daga Umar bn Khaddab (ra) ya sha ruwa sai rana ta bayyana, sai ya ce: babu ramuko a kanmu, saboda ba mu da zunubi.

A dunkule; wannan fahimta ita ta fi karfi ta hanyar Hadisi da kafa hujja da nazari kuma ta fi dacewa da dalilan Alkur'ani da Sunna da Kiyasi. Da shi zai bayyana cewa; abin da yake kiyasi game da mai mantuwa shi ne; Azuminsa bai baci ba, saboda ka'idar da Alkur'ani da Sunna s**a yi nuni a kanta ita ce: duk wanda ya aikata abin da aka yi hani a kansa cikin mantuwa to bai aikata laifi, don haka ibadarsa ba za ta baci ba, kuma babu banbanci tsakanin saduwa da iyali da waninsa na ci da sha, sawa'un a cikin Haramin Hajji ne ko Azumi".

Saboda haka, duk abin da aka yi bisa kuskure ko mantuwa a cikin Azumi, na ci ko sha ba ya bata Azumi, ko da kuwa saduwa da iyali ne, k**ar yadda ya gaba a jiya.

Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (4)Kowa ya sani, saduwa (jima'i) da rana da gangan a watan Ramadhan yana bata...
31/03/2024

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (4)

Kowa ya sani, saduwa (jima'i) da rana da gangan a watan Ramadhan yana bata Azumin mutum, kuma yana wajabta ramuko da kaffara. To amma idan mutum ya sadu da iyali kusan Asubahi fa, yana zaton da sauran lokaci ashe bai sani ba tun tuni Alfijir ya keto, ko kuma ya manta ya sadu da iyalinsa da rana tsaka, BISA MANTUWA, me ya wajaba a kansa?

To Malamai sun yi sabani a kan haka, daga cikin Malaman Salaf akwai wadanda s**a ce: BABU RAMUKO A KANSA, B***E KAFFARA.

Wannan shi ne abin da Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya rinjayar, kuma shi ne zabinsa k**ar yadda Almajirinsa Ibnu Muflih ya fada a cikin "Al-Furu'u" (5/ 41).

Shaikhul Islami ya ce:
وهذا القول أصح الأقوال وأشبهها بأصول الشريعة ودلالة الكتاب والسنة وهو قياس أصول أحمد وغيره فإن الله رفع المؤاخذة عن الناسي والمخطئ. وهذا مخطئ وقد أباح الله الأكل والوطء حتى يتبين الخيط الأبيض من الخيط الأسود من الفجر واستحب تأخير السحور ومن فعل ما ندب إليه وأبيح له لم يفرط فهذا أولى بالعذر من الناسي.
مجموع الفتاوى (25/ 264)

"Wannar fahimta ta fi sauran inganci, kuma ta fi dacewa da ka'idojin Shari'a da dalilan Alkur'ani da Sunna, kuma kiyasi ne bisa ka'idojin Imam Ahmad da waninsa cikin Malamai. Saboda Allah ba zai k**a mai mantuwa da mai kuskure ba. Wannan kuwa mai kuskure ne, Allah ya halasta masa ci da saduwa da iyali har sai farin zare ya bayyana daga bakin zare na Alfijir (sai hasken Alfijir ya bayyana daga duhun dare), kuma an sunnanta jinkirta Suhur, don haka duk wanda ya aikata abin da aka sunnanta masa ko aka halasta masa ba tare da sakaci ba, to wannan shi ya fi cancantar uzuri fiye da mai mantuwa".

Saboda haka, duk wanda ya yi saduwa (jima'i) da rana, wato tsakanin fitowan Alfijir har zuwa faduwar rana, da gangan, da saninsa, Azuminsa ya baci. Kuma ramuko da kaffara sun wajaba a kansa.

Amma wanda hakan ya faru da shi, cikin mantuwa, ko cikin rashin sanin ketowan Alfijir, to babu komai a kansa, kawai zai cigaba da Azuminsa ne, babu ramuko a kansa b***e kaffara.

Alal hakika duk wanda ya fahimci Shari'a a dunkulenta, bisa ka'idojinta da gamayyar dalilan Shari'a zai ga cewa; lallai wannar fahimta ita ce mafi inganci kuma mafi karfin dalilai.

Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (3)Wanda ya yi "Istimna'i" ya fitar da maniyyi da hanunsa ko da wani abun, Az...
30/03/2024

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (3)

Wanda ya yi "Istimna'i" ya fitar da maniyyi da hanunsa ko da wani abun, Azuminsa ya baci. A baya an yi ishara a kan wannan.

Wanda Maziyyi ya fito masa saboda kallon mace ko abin da ya yi k**a da haka Azuminsa bai baci ba. Al-Ba'aliy a cikin "Ikhtiyaraatu Shaikhil Islam Ibnu Taimiyya" ya ce:
ولا يفطر بمذي سببه قبلة، أو لمس، أو تكرار نظر، وهو قول أبي حنيفة والشافعي، وبعض أصحابنا.
الاختيارات للبعلي (160)

"Azuminsa ba zai karye ba saboda fitan Maziyyi, imma saboda sunbanta ko shafan mace ko maimaita kallonta. Wannan shi ne fadin Abu Hanifa da Shafi'iy da wasu a cikin Hanabila".

Ibnu Muflih ya ce:
وإن مذى بذلك أفطر أيضا، نص عليه "وم" واختار الآجري وأبو محمد الجوزي وأظن وشيخنا: لا يفطر، وهو أظهر "وهـ ش" عملا بالأصل، وقياسه على المني لا يصح، لظهور الفرق.
الفروع وتصحيح الفروع (5/ 10)

"In Maziyyi ya fito masa saboda runguma to Azuminsa ya baci...
Amma Shaihinmu (Ibnu Taimiyya) ya ce: Azuminsa bai baci ba, kuma wannan shi ne mafi inganci (shi ne fadin Abu Hanifa da Shafi'iy), saboda aiki da asali. Amma yin kiyasin Maziyyi a kan Maniyyi abu ne da bai inganta ba, saboda akwai banbanci tsakaninsu".

Saboda haka fitar da Maniyyi da gangan yana karya Azumi, amma fitan Maziyyi saboda kallon mace ko magana da ita, ko wani abun daban ba ya karya Azumi.

Amma fa kar mu manta, akwai abubuwa da ba sa karya Azumi amma kuma suna rage ladan Azumin. Don haka kar mu manta da babbar manufar Azumi, wato samar da Taqwa.

Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DAN FODIO TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share