23/05/2024
ASSALAM ALAIKUM
YAU ALHAMIS
15 GA ZUL QIDAH 1445
23 GA MAYU 2024
🇳🇬Shugaba Bola Tinubu zai tafi Chadi a yau Alhamis domin halartar bikin rantsar da Mahamat Déby a matsayin shugaban ƙasar.
Mai bai wa shugaban ƙasar shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba.
🇳🇬Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce ba za a yi wani gagarumin biki a ranar cikar gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shekera ɗaya ba.
Idris ya bayyana haka ne a taron manema labarai na ministoci a ranar Laraba a Abuja.
A cewar sa, matakin ya yi daidai da muradin Tinubu na yi wa ƙasa hidima, da kuma amfani da albarkatun ƙasa yadda ya k**ata domin amfanin ɗaukacin ‘yan Nijeriya.
Ya ce, “Ba za a yi gagarumin biki a ranar cikar gwamnatin shekara ɗaya ba, ba za a yi biki ba, ma’aikata daban-daban ne za su gabatar da jawabai.
🇳🇬Yayin da aka yi ta cece-kuce kan nadin na hannun daman Nyesom Wike, Shugaba Bola Tinubu ya janye nadin da ya yi Tinubu ya maye gurbin Chukwuemeka Woke da Dakta Adedeji Ashiru a matsayin daraktan hukumar Ogun-Osun River Basin Yayin da Tinubu ya ji korafe-korafen jama'a, ya mayar da Woke zuwa hukumar da ke kula da mai ta NOSDRA
🇳🇬Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon kwamandan rundunar leken asiri ta ’yan sandan Nijeriya, DCP Abba Kyari bayan shafe watanni 27 yana tsare.
Da wannan dama ta belin makonni biyu da kotun ta bai wa tsohon jajirtaccen ɗan sandan, zai halarci zaman makokin mahaifiyarsa, Yachilla Kyari da ta riga mu gidan gaskiya a bayan nan.
🇳🇬Majalisar Dokokin Katsina ta gargaɗi kamfanin sadarwa na MTN dangane da yawan ɗaukewar sabis ba tare da yi wa al’umma wani gamsasshen bayani ba.
Majalisar na bayyana takaicinda cewa yawan ɗaukewar sadarwar na cutar da kasuwanci da zamantakewar al’ummar jihar.
🇳🇬Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba ta tsige kakakinta, Honarabul Elvert Ekom Ayambem a jiya Laraba.
Honarabul Effiong Ekarika mai wakiltar Calabar ta Kudu 1 ne ya gabatar da ƙudirin tsige kakakin yayin da Omang Omang mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Bekwara ya goyi bayansa.
Bayanai sun ce mambobin majalisar 17 daga cikin 25 ne s**a amince da tsige kakakin nata sak**akon zarginsa da ɓarnatar da kuɗi, rashin kiyaye dokokin majalisar da sauransu.
🇳🇬Gwamnatin Kano ta kafa wani kwamitin da zai bincike mummunar faduwa da daliban jihar kimanin 103,777 s**a yi a jarrabawar 'qualifying' da ya kammala a baya-bayan nan Daliban aji biyar, wato SS2 a makarantun gwamnati na rubuta jarrabawar domin neman hukuma ta dauki nauyin su rubuta jarrabawar WAEC ko NECO idan sun yi nasara Ana bukatar akalla dalibi ya yi nasara a darussa biyar ciki har da lissafi da turanci, sai dai a wannan karon an samu bullar labarin mummunar faduwa domin dalibai 28, 333 ne kawai su ka yi nasara.
🇳🇬 An kori wasu ɗalibai ƴan Najeriya daga makaranta tare da ba su umarnin barin Birtaniya saboda gazawa wajen biyan kuɗin makaranta sak**akon faɗuwar darajar kuɗin ƙasar tasu naira.
Hakan dai ya faru ne a Jami'ar Teesside, wadda ta dakatar da ɗaliban daga shiga aji saboda rashin biyan kuɗin makaranta a kan lokaci.
Wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa sun shaida cewa, matakin Jami'ar ya sanya sun ji k**ar su kashe kansu, inda s**a zargi jami'ar da ɗaukar mataki na rashin tausayi
🇳🇬Rundunar hadin guiwar jami’an tsaro ta ceto wani yaro dan shekara biyu da kuma wasu mata ’yan kasuwa 11 da ’yan bindiga s**a sace a Jihar Kwara.
An yi garkuwa da mutanen ne a hanyar Ajase zuwa Ipo bayan an yi musu kwanton bauna da dare a lokacin da suke dawowa daga kasuwar Oke-Ode da ke Ifelodun, inda s**a je kasuwanci a Larabar da ta gabata.
An ce ’yan kasuwar sun fito ne daga yankunan Offa, da Yaaru da kuma Ikirun da ke jihohin Kwara da Osun
🇳🇬Ana zargin ɗan China ya kashe wata 'yar Najeriya saboda ta ki amincewa su yi soyayya.
An ce dan kasar Sin din ya tunkudo Miss Ocheze Ogbonna daga kan wata babbar mota.
Wannan dai na zuwa ne bayan da a baya wani dan China ya sheke masoyiyarsa a Kano.
DAGA ƘASASHEN WAJE
🌍Aƙalla Falasɗinawa 35,647 ne aka kashe tare da jikkata 79,852 a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma’aikatar lafiya ta ƙasar.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa an kashe mutane 85 tare da jikkata wasu 200 a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan zuwa ranar Talata
🌍Kungiyar fafutikar ’yancin Palasdinawa (PLO) ta sanar cewa, kasashe 130 daga cikin mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193 sun amince da ba wa kasar Palasdinu cikakken ’yanci, k**ar yadda kafar yada labarai ta CNN ta ruwaito.
Kazalika, manyan kasashen Turai uku, Spain, Norway da Ireland sun janye jakadunsu daga kasar Isra’ila kan yakin da take da kuma kashe Palasdinawa a Zirin Gaza.
Firaministan Ireland, Harris Simon, shaida wa taron manema labarai a birnin Dublin a ranar Laraba, cewa kasashe ukun sun yi itifakin mu’amala da Palasdinu a matsayin kasa mai cikakken ’yanci
🌍Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak ya sanar da cewa zai rushe majalisar zatarwar ƙasar a mako mai zuwa gabanin zaɓen ƙasar da za a gudanar a ranar huɗu ga watan Yuli.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan cece-ku-ce da raɗe-raɗin da aka riƙa yi, bayan hauhawar farashi a ƙasar ta kai wani mataki da ba ta taɓa kaiwa ba cikin shekara uku.
Jam'iyyar da ke mulkin ƙasar ta ƴan mazan jiya za ta shiga zaɓen yayin da take baya a ƙuri'ar jin ra'ayin al'umma, yayin da jam'iyyar Labour take gaba.
Jam'iyyar Conservatives ta kwashe shekara 14 a jere tana jagorancin ƙasar ta Birtaniya
🌍Ɗaruruwan Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a ƙofar ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu lokacin taron majalisar ministoci ta yaƙi, suna neman a sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.
FAGEN WASANNI
🏐Ipswich ta gabatar da sabon kwantiragi mai kwaɓi ga kocinta Kieran McKenna, a kokarin hana shi tafiya adaidai lokacin da Manchester United da Chelsea da kuma Brighton ke zawarcin.
⚽Ƙwallaye ukun da Ademola Lookman ya zura a ragar Leverkusen ne s**a bai wa Atalanta nasara akan zakarun na Jamus, kuma wannan ce rashin nasarar da s**a yi a karon farko cikin wasanni 51.
Wannan ne kuma kofin Atalanta na farko a nahiyar Turai.
⚽Kwamitin zartarwa na hukumar UEFA ya yanke cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na gasar Europa ta 2026 da na Conference na 2027 a filin wasa na Besiktas da ke birnin Istanbul.
..........................
Allah ya yaye mana dukkanin matsalolin day S**a addabe mu,ya gafarta mana,ya albarkaci Zuri ar mu,ya sanya alherin sa a gidajen mu...............----------
MARUBUCI
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE