29/08/2023
ALBISHIR. .....!!! Gwamnatin Tinubu Zata Dauki Mutane 300,000 Aiki a sabuwar Hukumar
(NATCOM)
_________
Sabuwar Hukumar nan da gwamnatin tarayya ta kafa wacce zata maida hankali wajen daƙile yaɗuwar mak**ai (NATCOM)
Gwamnatin Tarayyar Najeriya tace zata ɗauki sabbin ma'aikata 300,000 a sabuwar hukumar dakile yaɗuwar mak**ai (NATCOM) Muƙaddashin shugaban hukumar, Otunba Adejare Rewane, ya ce za a ɗauki mutane 7,000 a kowace jiha da kuma Abuja Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa musamman a Arewa maso Yamma
Sabuwar Hukumar nan da gwamnatin tarayya ta kafa wacce zata maida hankali wajen daƙile yaɗuwar mak**ai (NATCOM) ta ce ta gama shirye-shiryen ɗaukar ma'aikata 300,000. Rahoton jaridar Aminiya ya tattaro cewa hukumar zata ɗauki ma'aikata a kowane ɓangaren kasar nan kuma zata ba su horo na musamman domin dakile yawaitar yawon mak**ai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke fama da matsalar tsaro a sassa daban-daban k**a daga barazanar hare-haren yan bindiga, yan ta'adda da sauransu. Muƙaddashin shugaban NATCOM na ƙasa, Otunba Adejare Rewane, shi ne ya bayyana shirin ɗaukar ma'aikatan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, 2023.
Mista Rewane ya bayyana cewa hukumar NATCOM zata ɗauki adadin mutane 7,000 a kowace jiha daga cikin jihohi 36 na Najeriya da babban birnin tarayya Abuja. A kalamansa, muƙaddashin shugaban NATCOM ya ce: "Zamu ɗauki ma'aikata 300,000 a sassan Najeriya a kokarin ganin an samu tabbataccen zaman lafiya. Bayan ɗaukar aikin zamu ba su horo na musamman."
Wannan mataki ka ɗaukar ma'aikatan zai rage yawan zaman kashe wando a ƙasa kuma zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin cimma nasara." "Duk mai son shiga wannan aiki ya riƙa bibiyar jaridu domin ganin matakan da za a bi amma zamu fi maida hankali kan matasa."
Ko yaya kuke kallon wannan shirin kuma wani fata kuke da shi kan shirin?